HADEJIA A YAU!
Kamar yadda aka sani ƙasar Hadejia tana gabatar da Hawa guda uku a kowace shekara, wato Sallar Azumi, Sallar Layya da kuma Maulidi. Sannan kuma a kowace Sallah ana gabgaba da hawa guda biyu... Hawan sallah da Hawan Bariki, Sannan rana ta uuku yara suyi Hawan daushe da La'asar.
Kamar yadda Tarihi dai ya nuna Sarkin Hadejia Mallam Abdulkadir shine ya kirkiro Hawan Bariki, a wata fira da mukayi da Galadiman Jauje ya tabbatar mana cewa Sarki Abdulkadir mutum ne Mai son nishadi, hakan yasa a zamanin sa aka kirkiri Hawan Bariki. Sarki yaka je washegarin sallah da hakimansa da Dagatai su kaiwa D.O. Ziyara.
Ranar Laraba 20/April/2005 Mai martaba sarkin Hadejia Alh. Adamu AbuAbuba Maje ya kirkiro Hawan Ziyara kokuma Hawan Mai Bubban Daki, wannan hawa an fara yinsa ne a sallar Mauludi, wadda kuma za'a rinka yinsa ko wace sallah da yamma. Wato za'a hau washe garin Hawan Bariki.
Ranar Juma'a 22/April/2005, Mai martaba ya hau da yamma. Inda yabi ta tudun mabudi Har zuwa Tudun Barde ya shiga yayi ziyara ga Mai bubban Daki, Bayan ya fito sai yabi ta makera ta Dubantu ta Ganuwar kofar yamma, sannan sai yabi ta bakin kasuwa ta Makwallah ta kofar Jarma sannan In yazo kofar Fada sai ya Tsaya Hakimai kuma su Fara zuwa daya bayan daya suna Jafi. Bayan sun Gama sai ya shiga Gida ya sauka. Hadejia A yau.