"" /> HADEJIA A YAU!: Feb 19, 2016

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, February 19, 2016

TARIHIN HADEJIA.



Takaitaccen Tarihin masarautar Hadejia.


Masarautar Hadejia dadaddiyar Masarauta ce wadda ta kafu shekaru aru aru da suka gabata, daga lokacin kafuwarta kawo yanzu masarautar tayi fice da yin suna bisa ga muhimman tarihi da take dashi. Masarautar Hadejia tana daga cikin masarautu da sarakunan HABE suka mulka kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, kuma tana daga cikin masarautun da ake kira Hausa Bakwai. Masarautar tana daga cikin Masarautu da suke karkashin Daular Usmaniyya, daga Gabas tayi iyaka da Tsohuwar Daular Borno daga yamma tayi iyaka da Masarautar Kano, daga Kudu kuma tayi iyaka da Masarautar Katagum sannan daga Arewa tayi iyaka da Masarautar Gumel. Birnin masarautar yana cikin garin Hadejia dake Arewa maso gabashin Jigawa a Arewacin Nigeria, sunan garin ya samo asali ne daga wani Maharbi wadda shine ya kafa garin wato HADE, da kuma Matarsa JIA. Sunayen wadannan mutane shi aka hada ya zama HADEJIA, domin a lokacin mutanen wasu garuruwa in zasu zo sukan ce mun tafi garin Haden jiya, wato ana masa Lakabi da sunan Matarsa. Saboda takaita kalma ta Hausawa shine yasa aka hade sunan ya zama Hadejia. 

Masarautar Hadejia tana da fadin kasa wadda ta kai Murabba’in kilo mita dubu shida da dari tara da sittin da uku(6963), wannan yanki yana da shimfidaddiyar kasa mai kyau wadda ake kwatanta yanayinta da na kasar Chadi, kuma tana da Jigayi masu tarin yashi da kuma kwari mai tabo da laka amma bada da tsaunuka ko Duwatsu. Kasar Hadejia tana da Kogi wadda ya kasance akwai ruwa kowane lokaci, sannan tana da fadamu masu yawa wadanda suke kafewa lokaci zuwa lokaci.

Kogin kasar Hadejia ya taso ne daga Kudancin Katsina ta Arewa da Zaria sannan ya nufi Arewa maso gabas ya shigo ta Kasar Kano ya ratsa kasar Hadejia, sannan ya nufi Tafkin Chadi. Wannan Kogi ya ratsa ne ta Kudancin Hadejia da Gabashinta, wannan bangare ne da yake samarda ruwan sha da kamun kifi da kuma aiwatar da Noman rani. A lokacin damina kogin yakan cika inda yake samarda kananan fadamu a sassa daban daban wadda ake amfani dasu a wajen noman lambu. A bangaren Noma Masarautar Hadejia tana gabatarda noma a lokuta biyu wato Rani da Damina, inda masana yanayin kasa suka tabbatar cewa duk abinda aka shuka a wannan kasar zai fito yayi kyau saboda yanayin kyawun kasar. 

A bangaren kasuwanci kasar Hadejia ta shahara wajen saye da sayarwa tun kafin Jihadi, domin ta zama wata mahadar kasuwanci ce tsakanin Daular sokoto da Daular Borno. Mutanen Masarautar suna da sana’oinsu da dama kama daga sana’ar hannu zuwa Fatauchi da sauransu. Kasar Hadejia tana da kasuwanni da yawa wadanda suke ci a dukkanin sati sannan da masu ci a kowacce rana.

Masarautar Hadejia tana da Kabilu da yawa wadanda suke yarensu da Al’adunsu sun banbanta kuma suna zaune a yankuna daban daban na kasar, Kabilun kuwa sun kunshi Hausawa, Fulani, mangawa, Ngizmawa, koyamawa, Baddawa, da sauransu. Wadannan Kabilu kowanne da irin yarensa da kuma Al’adarsa da irin tsarin zamantakewarsu, sai dai duka suna bin Tafarkin Addinin Musulunci ne tun bayan Jihadin Shehu Usman Danfodiyo.

posted from Bloggeroid