HADEJIA A YAU! Alhamdulillahi Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake bada Mulki ga wanda yaso, kuma a lokacinda yaso, Tsira da Aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu wanda Allah ya aikoshi da shiriya da rarrabewa tsakanin Karya da Gaskiya!
Bayan haka muna kara Godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Dr. Sule Lamido, wanda Allah ya bashi Mulkin Jigawa domin ya Gudanar dashi bisa Gaskiya da Adalci. Alhamdulillahi Jigawa a yau.
Ranar Litinin 5/11/2012. Mai Girma shugaban kasa ya kawo mana ziyara Hadejia a karkashin mulkin Gwamna Sule Lamido, Inda kuma akayi hawan Daba kasaitacciya. Hakika wannan abin Alfahari ne a garemu Hadejiawa kuma babu abinda zamucewa Mai Girma gwamna sai godiya.
Bayanda shugaban kasa yazo Hadejia ya ziyarci fadar Mai martaba Sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar Maje, bayan yaga Hawan Daba da aka shirya masa ya gana Da Mai martaba Sarki. Kuma ya nemi Alfarma guda Uku wadda zata kara Inganta wannan yanki na Hadejia. Na farko ya nemi Alfarmar Gwamnati da ta ci gaba da aikin B.E.C. Wanda a halin yanzu ya dakata, na Biyu ya nemi Alfarmar da ayi mana Maganin Ambaliyar Ruwa da ta Addabi wasu sassa na Hadejia.
Na uku ya nemi Alfarmar a Sake Inganta Jingar Kogi wadda ake samun Asarar Dukiyoyi da amfanin Gona.
Muna kara Godiya ga Wannan Gwamnati wadda A zamaninta ne Jigawa ta tabbata Jigawa. Hakika duk wanda yasan Jigawa shekara Bakwai baya Idan yazo zai tabbatarda Jigawa ta samu Uba. Jigawa abar Alfaharinmu, Sule Lamido Abin Alfaharin Jihar Jigawa.
Hakika abubuwanda mukeji a baya kunnenmu ne yaji Idonmu bai gani ba. Dan haka ka bada saida akan abinda Idonka ya gani yafi akan abinda kunnenka yaji. Muna kara jinjina ga Mai Girma Gwamna Wanda ya daga Darajar wannan Jiha tamu. Jigawa ada take Jaririya amma a yanzu Uwace a zamanin Sule Lamido.
Ba rabuwa da Gwani ba Maida Gwani. Jigawa ta tattara Manyan Mutane masu hazaka! kama daga Gwamnan zuwa comishinoni da sauransu. Jigawa tarin Allah Lamido Ikon Allah.
Allah ya huci gajiya, Allah ya maida kowa Gidansa Lafiya. Ameen. Hadejia a yau.