"" /> HADEJIA A YAU!: Feb 2, 2020

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, February 2, 2020

TARIHIN GARIN GUMEL (TUMBI)... Kashi na daya.

HADEJIA A YAU!

         TARIHIN GARIN GUMEL

.
Asalin mutanen Gumel Barebari ne kuma sun fito daga garin Ngazargamu, Muhammadu shine ya fito da ‘ya’yan sa guda biyu, Danjuma da Adamu Karo. Dalilin fitar sa shi Dan uwan Shehu ne, to shehu yana da wani Doki wadda yake so kwarai har yasa aka ware shi daga cikin Dawakai aka masa gida daban. Shi kuma Muhammadu yana da  Godiya sai ya tsanantawa mai kiwonsa yayi mata baye, ana nan sai  godiya ta haihu ta haifi Dan Doki har ya girma ya fara hamimiya sannan sai Shehu yaji hamimiyar dan Dokin wannan , sai shehu yace “Duk inda Dokin nan ya fito dan Doki na ne” sai yayi kiran mai kiwon sa yace masa “In baka fada min wadda yayi baye da doki na b azan halaka ka” sai yace masa “Muhammadu ne ya tsananta min”,  sai Shehu yace to shikenan.

 To da Muhammadu yaji wannan zance sai ya tsorata ya gudu shi da ‘ya’yan sa biyu yazo wani gari da ake kira Nagalu kasar Shadiko, yanzu tana cikin Jamhuriyar Nijer. Yana nan sai Shehu ya aika masa cewa ya koma gida ba komai, sai Muhammadu yace “NA ATIMA DIGAIYE” Wai Anan na fita. To saboda waccan kalma da ya fada shine har yanzu ake kiransa da Diga Diga kakan Mangawa. To daga Nagalu da Shehu ya aiko ya koma har yau sai ya bar nan ya tashi ya koma Babaye don yayi Noma, daga nan sai suka taru suka yi shawara a Dogoma ya kamata ayi Shugaba, sai Muhammadu yace a yiwa Adamu Karo bubban dan sa, shine ya fara sarauta a Dagoma suka zauna gari ya zama nasu suka shekara uku, daga nan Adamu Karo ya tashi zuwa yaki kasar Kano sai Fulani suka harbe shi da kibiya a wani gari da ake kira Kanebu sai ya rasu.
Sai aka dawo gida aka nada kaninsa Danjuma yayi shekara goma sha bakwai yana sarauta sai ya rasu, sai aka nada dan Adamu Karo Muhammadu Mai Kota, sai suka tafi wajen Shehun Barno don ya basu Tuta, sun karbi Tuta a hijira ta 1781. 

Shi Muhammadu Mai Kota shine ya fara karbar Tuta, dalilin da yasa ake ce masa Mai Kota shine bayan ya karbi Tuta a Barno sai ya koma Sokoto wajen Sarkin Musulmi don ya bashi Tuta, to Sarkin Musulmi yasan akwai Tutar Shehun Barno a hannun sa sai yace dashi;- “Sai ka koma wadda aka min izni in bayar ta kare” Sai yayi Addu’ah a jikin Kota ta Noma ya bashi yace kaje da wannan ba kai ba duk Sarkin da za’ayi in Damina tayi ya karta wannan Kota ko da sau biyu ne, in da duk Duniya za’a yi yunwa to kasar sa baza su yi ba. To saboda wannan Kotar sai ake kiransa Muhammadu na Kota, kuma wannan Kotar tana nan har yanzu a gidan Sarautar Gumel.

Muhammadu na Kota ya shekara Ashirin da bakwai (27) yana Sarauta ya rasu, sai aka nada Dan sa Muhammadu Kalgo yayi shekara Hudu (4) yana sarauta sai wani Barawo da ake kira  Barjo ya biyo dare ya kashe shi. Sai aka tafi Barno aka nadaMuhammadu Dan Auwa, ya shekara Goma sha bakwai yana Sarauta kuma Jarimi ne domin ya shahara wajen yaki. Ya sha kaiwa hari kasar kano yana cinye musu kauyuka, har ma mai wakar Bagauda yana cewa “Da Tumbi da Washa sun ga banza sun hada kai suna dibar kanawa, sannan sun tashi daga Dagoma sun dawo Tumbi”  A lokacin mulkin sa kasar Kano suka yi ta kawo chaffa wajen sa, tun daga Dutse Gadawur suke kaiwa haraji har Tumbi.

Lokacin da Shehu Laminu ya samu labarin cewa Muhammadu Dan Auwa yayi karfi duk sararin nan babu kamar sa, ko shi zuwa gaba zai fi karfin sa. Sai Shehu Laminu ya aiko Dan Auwa yaje yana neman sa, sai Dan Auwa yaki zuwa har saida Shehu Laminu yah au da kansa yazo wani gari da ake kira BARMARI, kasar Yalawa tsakanin su da Tumbi bai fi Mil Bakwai ba (7) inda Dan Auwa yake. Da Shehu yazo wannan gari sai ya aika Dan Auwa yazo, duk da haka sai yaki zuwa yace a fadawa Shehu yazo nan Tumbi ya same shi domin in yazo nan babu yadda zai yi dashi, amma in shine yaje to Uban dakin sa ne sai yadda Shehu yayi dashi. 

Sai Shehu ya hada Dabara da Malamai na cikin garin Tumbi yace “Ku sani zan je Tumbi amma duk abinda ya faru ku sani yaki tsakanin Musulmi da Musulmi babu kyau, ku fadawa Dan Auwa gaskiya yazo” sai wani Malami daga cikin Malaman Tumbi yaje gaban Dan Auwa ya rantse da Alqur’ani cewa  in ya kais hi gaban Shehu zai tashe shi ya dawo gida, sai Dan Auwa ya yarda suka tafi gaban Shehu Laminu. Da suka je gaban Shehu sai Malamin ya tashi Dan Auwa a tsaye yace masa “ Kamar yadda na maka rantsuwa zan tashe ka to na cika Alkawari, sai Malami ya tafi ya bar Dan Auwa da Shehu Laminu. Bayan sun kama Dan Auwa sun rasa yadda zasu yi su kashe shi, sai Dan Auwa da kan say ace a samo mazagin wando a shake shi dashi. Haka kuwa aka yi suka samo mazagi suka shake shi ya mutu, sai kuma Shehu yasa aka yanka Sa aka fede shi aka dauki fatar aka saka gawar Dan Auwa a ciki aka nade aka jefa a Kogi, tun daga wannan lokacin kogin ya daina kawowa Ruwa.

Dalilin tsagen fuskar Gumelawa kuwa Muhammadu Dan Auwa ne ya Auri wata ‘yar Sarkin Washa da ta haihu sai ‘Yanuwan matar suka ce sai ayiwa yaron tsage irin nasu, to wannan tsagen an same shi ne daga Washa. Bayan Shehu Laminu ya kama Dan Auwa ya kashe shi sai ya nada kanin sa  Muhammadu Dan Tanoma a sarautar Tumbi.

Bayan Muhammadu Dan Ta Noma ya shekara Tara (9) yana sarautar Tumbi sai yaso yayi gidan gona, sai ya fadawa Malaminsa sai Malamin yayi rubutu yace a baiwa Godiya tasha duk inda tayi fitsari to anan za’ayi. To anan Gumel kusa da fada Duhuwa ce da wata Saniya ta gawurta ta zama kamar Bauna take tsare mutane, ana kiran Saniyar da suna Gumale. Sai Dan Tanoma yasa aka je aka kashe Saniyar sannan aka tafi da wannan Godiyar, da tazo kusa da wurin wani zuwo sai tayi fitsari. Sai mutanen da suke biye da ita suka ce “LAU TAYI” ma’ana sunan Godiyar Lau, wannan shine dalilin da ake cewa Gumel Lautai. Da aka zo aka fadawa Sarki sai ya tambaya a ina da inda aka kashe Gumale tayi? Sai suka ce masa a gabas da wurin ne kadan, wannan shine dalilin da yasa ake kiran garin da suna Gumel. Zamu kawo muku kashi na biyu.

Madogara...  
Assessment report on Gumel Emirate 1916.
Eap.bl.uk/Archive-file EAP087-3-24.
Gado da Masun Gumel.