HADEJIA A YAU!
Daga Dr. Nuraddeen Muhammad
Daga Dr. Nuraddeen Muhammad
Gangamin Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Da Inganta Muhalli a Garin Hadeja
Lahadi 18 ga Agusta, 2019.
A'uzubillahi Minash shaid'anir rajim. Bismillahir rahmanir raheem.
Maimartaba Sarkin Hadeja, kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa; Alhaji (Dr) Adamu Abubakar Maje Haruna (CON), Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa; Alhaji Umar Namadi, ‘Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar yankin Arewa maso gabas na Jihar Jigawa; Sanata Ibrahim Hassan Hadeja (Shattiman Hadeja II), Bubban Sakatare a Ma'aikatar kula da Muhalli ta Jihar Jigawa; Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa, Shugaban Hukumar Talabijin ta Jihar Jigawa; Alhaji Ishaq Hadeja, Shugaban K'ungiyar Gangamin Tsabtace Garin Hadeja da Shuka Bishiyoyi (HGPE); Mallam Ahmad Ilallah, Wakilan Kungiyar Inganta Muhalli da Shuka Bishiyoyi ta garin Gumel (GCIGCE)
Shugabannin Kungiyoyin sa kai na al'ummar Hadeja, Sauran manyan bak'i da aka gayyata' Yan Jarida na rediyo, da talabijin, da jaridu, da kuma kafafen sada zumunta na zamani, Y'anuwana maza da mataA ssalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu....
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Mad'aukakin Sarki, mai kowa mai komai, da ya bamu ikon taruwa a yau domin gudanar da wannan gagarumin aiki na alheri. Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon tsira Annabi Muhammad (SAW), fiyayyen halitta kuma mafificin masu tsabta da inganta muhalli.
Daga farko, zan fara da godiya maras adadi ga shugabannin wannan gamayya ta matasa domin tsabtacewa da kuma inganta garin Hadeja da suka bani wannan muhimmiyar dama har kashi biyu.
Ta farko ita ce kasancewa babban mai gabatar da jawabi a matsayina na d'an uwansu matashi - Dr Nura. Domin a ba mutum damar yin magana gaban irin wannan gangami, musamman idan a ka yi la'akari da irin mutanen da aka tara a wannan wuri, to ba k'aramar dama ba ce da kuma girmamawa.
Maudu'in da a ka ce na yi magana a kansa shine 'Muhimmancin Aikin Sa kai a Tsakanin Al'umma Domin Inganta Muhalli'.
Dama ta biyu kuwa ita ce, ta alfarmar da aka yi wa Gidauniyar da na k'irk'ra, wato Gidauniyar Unik Impact (ko Unik Impact Foundation a turance) ta yin tarayya a wannan aikin alheri da suka assasa ta hanyar ba da gudunmuwar d'aruruwan irin mad'aci da kuma mangwaro na zamani. Babban abin godiya ne a ba ka damar shiga cikin wani aikin alheri na al'umma.
Shuka bishiya abu ne mai matuk'ar muhimmanci a garemu ba wai kawai ta fuskar kariya da inganta muhalli ba, a'a, har ma ta fuskar addininmu, tattalin arzik'inmu, da kuma walwalarmu.
Tun farko, shi dai addinin musulunci, a matsayinsa na tsarin wayewa na gabadayan rayuwa, ya yi tanadin tsare-tsare da ka iya magance matsaloli na muhalli da ke yi wa d'an adam barazana a wannan lokaci. A bisa tarbiyya irin ta addinin musulunci, wasu magabatan na kallon cewa hatta shi kansa muhallin wani nau'ine na amana da Allah (SWT) ya mallaka a hannun bayinSa. Akwai ayoyi da dama na Alkura'ani mai tsarki da su ke tsawatarwa ga mumunai akan almubazzaranci, yad'a 6arna da kuma fasadi a bayan k'asa. Lalatawa da kuma wofintar da muhalli, tamkar wani nau'ine na almabozaranci da kuma 6arna a bayan k'asa.
Saboda matukar muhimmancin da addinin musulunci ya dora kan amfanin itatuwa a muhallin dan Adam shi ya sa ma ya yi hani da sare bishiyoyi da sauran nau'in shuke- shuke ba tare da wani kwakkwaran daliliba.
Manzon Allah Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya kwadaitar a cikin ingattattun hadisansa akan falala da kuma fa'idar inganta muhalli, da daraja shi, da kare shi ta hanyar shuka bishiyoyi. D'aya daga cikin hadisan shine wanda mazon ya ke cewa; "ita duniyar nan koriya ce shar k'yak'yk'yawa, kuma Allah (SWT) ya dank'a muku ita a matsayin amana".
Ko da a yanayi irin na yak'i, Manzon tsira ya kan gargadi kwamandojin rundunonin musulmi da su guji sare bishiyoyi da kuma amfanin gona na abokan gaba. Ma'aikin dai ya kasance a lokacin rayuwarsa yana bada muhimmanci da karfafa guiwa kan amafani da k'asa mai d'orewa.