Wakar Tsuntsaye; Daga
Ahmadu Dan Matawalle
Amshi: Sake shiri fasihi, Bamu jawabi
na Garba mai Yammata.
Taro na baku labari kuji wal khamisatu Ashara wannan babi na sha biyar ne Tsuntsaye zasu jesu neman sarki.
1] Tsuntsayen gida da daji, sun hadu
sun girka shawara, Jimina itace
gwamna tace zata yi musu Sarki.
2] Agwagwa aka bai sarauta, sunce
wofi marar karama, yar banza mai
kama da gammo, bata da siffar da
zasu bita kazama.
3] Hankaka ka bai sarauta, sun ce su
dai ba zasu lamunta ba, sun sake
shawara suna cewa 'Danfashi' bazai
sarki ba.
4] Aka bai Mikiya sarauta, sunce
wannan in ta samu mulki, ita wa zaya
ganta, sai ko mushe ya fadi zaka
ganta da sauri.
5]Borin-Tunke ka bai sarauta,
tsuntsaye duk suna ta mamaki, sai
wannan ya dubi wannan, wai dan sun
sami Shugaba maigirma.
6] Da Shaho yazo da kansa, tsuntsaye
sai suke ta mamaki, sai wannan ya
Wakar Tsuntsaye; Daga
Ahmadu Dan Matawalle
Amshi: Sake shiri fasihi Bamu jawabin
na Garba mai Yammata
1] Tsuntsayen gida da daji, sun hadu
sun girka shawara, Jimina itace
gwamna tace zata yi musu Sarki.
2] Agwagwa aka bai sarauta, sunce
wofi marar karama, yar banza mai
kama da gammo, bata da siffar da
zasu bita kazama.
3] Hankaka ka bai sarauta, sun ce su
dai ba zasu lamunta ba, sun sake
shawara suna cewa 'Danfashi' bazai
sarki ba.
4] Aka bai Mikiya sarauta, sunce
wannan in ta samu mulki, ita wa zaya
ganta, sai ko mushe ya fadi zaka
ganta da sauri.
5]Borin-Tunke ka bai sarauta,
tsuntsaye duk suna ta mamaki, sai
wannan ya dubi wannan, wai dan sun
sami Shugaba maigirma.
6] Da Shaho yazo da kansa, tsuntsaye
sai suke ta mamaki, sai wannan ya
dubi wannan, Shaho yazo shi babu
sauran wargi.
7] shaho ta bai sarauta, tsuntsaye sai
kuzo ku kai caffa, Borin-Tunke ka dau
jakarka a hannu.
8] Fadawa kuzo nadin Shaho, Zabin
dake cikin dawa, sune yan figini
mabusa Sarki.
9] Zalbe ka baiwa mai Kakaki, yan
doka tambura ne Burtu.
10] Zagage ka baiwa Balbela, Zakaran
Kekuwa kasa yan kurya
11] Ga Tsintara tana algaita, ga
Hasbiya tana buga Jauje
12] shaho yana jawabi, Borin tunke ka
bai Waziri, Gauraka ne Ciroma mai
alfarma.
13] Kuma Tuje ka bai Galadima,
Madakin gari ka baiwa Dinya.
14] Sarkin Bayi Shamuwa ce, sannan
Sarkin dawa Kitsawa ce, Alkalin gari ka
bai Kahuhu.
15] Marke ka baiwa Yari, Sa'annan
angulaye kurhu na banzar gari
madeba kashi.
16] Sarautar da zata dace!! Farin
Barugu shi ka baiwa limami, sannan
na baku labari, kuma sannan
Kadafkara shine Ladaninsa ko dare ko
rana.
dubi wannan, Shaho yazo shi babu
sauran wargi.
7] shaho ta bai sarauta, tsuntsaye sai
kuzo ku kai caffa, Borin-Tunke ka dau
jakarka a hannu.
8] Fadawa kuzo nadin Shaho, Zabin
dake cikin dawa, sune yan figini
mabusa Sarki.
9] Zalbe ka baiwa mai Kakaki, yan
doka tambura ne Burtu.
10] Zagage ka baiwa Balbela, Zakaran
Kekuwa kasa yan kurya
11] Ga Tsintara tana algaita, ga
Hasbiya tana buga Jauje
12] shaho yana jawabi, Borin tunke ka
bai Waziri, Gauraka ne Ciroma mai
alfarma.
13] Kuma Tuje ka bai Galadima,
Madakin gari ka baiwa Dinya.
14] Sarkin Bayi Shamuwa ce, sannan
Sarkin dawa Kitsawa ce, Alkalin gari ka
bai Kahuhu.
15] Marke ka baiwa Yari, Sa'annan
angulaye kurhu na banzar gari
madeba kashi.
16] Sarautar da zata dace!! Farin
Barugu shi ka baiwa limami, sannan
na baku labari, kuma sannan
Kadafkara shine Ladaninsa ko dare ko
rana.