"" /> HADEJIA A YAU!: Sep 17, 2019

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, September 17, 2019

DAMA CE KAWAI.... Dr. Nuruddeen Muhammad

HADEJIA A YAU!

Labarin Rayuwata

Dama ce kawai...! Dr. Nuruddeen Muhammad. 

Ma'anar Dama itace "wani lokaci ko wasu jerin al’amura da kan yi dalilin faruwar wani abu."

Rayuwata gaba d'ayanta labari ne na damarmaki wanda ke sanya fata da karfafa zuciya. Wadannan damarmaki sun kasance da iznin Allah mad'aukaki tamkar wata fitila ce da ta haskaka mini tafarkin rayuwa na zama duk abunda na zama.

Dacewa da samun wad'annan damarmaki, da kuma amfani da su a lokutan da su ka bijiro, shine dalili da kuma matakin dagowata daga tsukun yankin mahaifata a Hadeja, Jihar Jigawa, arewa maso yammacin Najeriya, inda ya kaini zuwa madaukakan wurare kamar ofisoshi da d'akunan taron Majalisar ‘Dinkin Duniya da ke birnin New York na k'asar Amurka da kuma dukkan nahiyoyin da ke fadin wannan duniya.

Babbar dama ta farko a gareni ita ce ta samun mahaifi irin wanda Allah ya azurta ni da shi (Mallam Muhammad Adamu UNIK), jajirtaccen malamin makaranta kuma Hedimasta da ya shahara kan gaskiya da rikon amana da kuma aiki tukuru. Malam ne ya fara cusa min ak'idar sanin darajar ilmi da maida hankali a kan aiki, tare da nusar da ni kyawawan dabi’u na rayuwa irin su: gaskiya da rik'on amana, hak'uri da juriya, karfin hali, sanin darajar d'an adam, fin k'arfin zuciya, tausayi, da kuma uwa uba, ya dasa min ginshik'in tsoron Allah a zuciyata. 

Wannan Damar dai ita ce ta ingantaccen ilimin da na samu  k'yauta a makarantun gwamnati (tun daga makarantar firamare ta unguwa zuwa sakandaren yanki, jami'a da kuma k'ololuwar mataki na karatun aikin likita. Karatu, tarbiyya da kuma jajircewa su ne dai ta hanyar da Ubangiji ya d'aukaka Nura ya koma Dakta Nura a yau.

Dama ce bud'e ido da na yi da wuri akan harkokin siyasa na gane yadda ake gudanar da ita, a inda na fahimci tasiri ko k'arfi na tarayyar jama'a a karkashin wata manufa guda idan aka yi amfani da shi wajen yad'a ak'idar da za ta amafanar da daukacin al'umma, musamman bangaren talakawa.

Babbar Dama ita ce da Allah (SWT) ya had'ani da Dr Sule Lamido, wanda ya gano wad'ancan halaye nawa, da tarbiyya, da karatu, da kuma bibiyar siyasa, ya gamsu da su, sannan kuma ya ci alwashin sarrafa su. Shine dai sanadiyyar da ta kai ni can k'ololuwar  gwamnati ina matashi d'an shekara 34 kacal, inda a gefe daya na san maza kuma maza su ka san ni, amma kuma a wani gefen na gane cewa duniyar nan fa ba komai ba ce face wani yanayi na k'ank'anin lokaci.

Ba komai ba ne face Dama ta jawo min yabo da girmamawa daga shugabannin k'asashe, manyan jami'an difilomasiyya da siyasa, fitattun shugabannin al'umma,  hamshak'an ‘yan kasuwa da kuma y'an uwana likitocin da na samu dacewar yin gogayya da su, kuma Allah ya ba ni damar nuna musu kokari da jajircewata ta ganin na kai gaci a duk wani al’amari da na sa a gaba ko kuma duk wani aiki da aka sanya ni.

Babbar tambaya a nan ita ce, ta ya ya wani matashi marar gata a sama, wanda ya fito daga arewacin Nijeriya, yankin da miliyoyin ‘ya’yan talakawa irinsa su ke rasa makomar rayuwa tun suna ‘yan kasa da shekaru 10, ya zama Ministan Najeriya ma fi k'arancin shekaru tun bayan dawowar mulkin damokirad'iyya a kasar a 1999, k'wararre a aikin likitanci, gogagge a harkar diflomasiyya, kuma har ya taka rawa a harkokin siyasar al'ummarsa, a k'asar da samun irin wannan tagomashi sai ‘yan tsiraru, masu uwa a gindin murhu??!
..... Amsar dai mai SAUK'I ce!!...

Alhamdulillah... DAMA CE KAWAI!!!

Sanin da na yi cewa, ba dan wad'annan damarmaki da na samu a rayuwata ba, da kuwa ni ma zan iya shiga kowane irin hali, shine babban k'aimin da ya sanya na yi tunanin kafa wannan Gidauniya ta Unik Impact (www.unikimpact.foundation). Ita dai wannan Gidauniya tamkar wani dandamali ne na yi wa al'umma, musamman 'yan uwa matasa, kokarin samun dama a rayuwa ta hanyar bayar da tallafi ga harkokin ilminsu, tattalin arziki da kiwon lafiya, har ma da inganta muhallinsu. Sannan da yi musu jagoranci bisa sanin muhimmancin ilimi da kuma rungumar dabi’un kirki irin su: jajircewa a kan aiki, gaskiya da rik'on amana, fin k'arfin zuciya da kuma nuna tausayi ta hanyar yi wa al’umma hidima da taimakon na kasa.

Babban burin wanna Gidauniya shine tarairayar zukatan matasanmu da d'ora su a kan tafarkin samun d'aukaka da cin nasara a rayuwarsu. Idan har ni zan sami irin wannan d'aukaka, to a cikin ikon Allah kowa ma zai iya samun irin ta, ko sama da hakan  ma idan ya sami dama.

Hakika tarbiyya ce, da kuma karatun da duniya ta koya min, su ka ganar da ni cewa, d'aya daga cikin hanyoyin da mutum zai nuna godiya a bisa ni'imomin da Allah ya yi ma sa, shine, shi ma ya yi sanadiyyar samun dama ga wasu. Ta haka ne kawai zamu yi tunanin gyara al'ummar nan; ko da kuwa a sannu sannu ne.

Wani k'wararre da na yi aiki tare da shi, ya ta6a yi min tambaya cewa ya ya na ke hangen wannan Gidauniya ta Unik Impact a cikin zuciyata?... sai na amsa masa da cewa:

"Kamar gungu ne na wasu mutane da  Allah ya bai wa Dama a rayuwa  inda su ma su ke k'ok'arin ganin wasu da yawa sun sami irin wannan damar."

Hausawa dai su kan ce: ‘Yi wa wani, yi wa kai....’