"" /> HADEJIA A YAU!: Jul 17, 2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, July 17, 2012

KASAR HADEJIA DA KABILUN CIKINTA


HADEJIA A YAU! Kasar Hadejia tana da kabilu da dama wadanda kuma suke da yarensu daban-daban: kamar...
1, HAUSAWA
2, ABORAWA (FULANI)
3, MANGAWA
4, GIZMAWA
5, BADAWA
6, KOYAMAWA.

1, HAUSAWA:- Kabilar Hausawa sune kabila mafiya yawa a kasar Hadejia Domin su babu wadda zaice ga wani lokaci da suka shigo Kasar Hadejia, kuma tafi karfi a kasar sakamakon dadewar Garuruwansu. kamar Garun Gabas (Biram), Auyo, da Matsa. kuma ko zuwan Bayajidda Garun Gabas yazo ne ya samu Mutanen Garin suna yin yaren Hausa.

2, ABORAWA (Fulani):- Kabilar fulani sun shigo kasar Hadejia tun a Farkon karni na goma sha biyar (15) kuma sun shigo ne daga yankin Massina wasu kuma daga Katsina, kuma sun Taho ne daga Gabar Kogin SENEGAMBIA wato SENEGAL. Sun fara zama ne a Rinde wasu kuma sun Zauna a Jarmari wasu a Marke wasu a Adiyani da Margadu. Kuma ayarinsu ya kasu biyu Inda wasu suka wuce kasar Kano Karkashin Jagorancin Lamido Usman Kalinwama. A Karni na goma sha Tara (19) Wasu fulanin sun sake shigo Kasar Hadejia daga yankin Machina Karkashin Jagorancin Ardo Abdure Dan Jamdoyi. Kuma ance Kafin suzo Hadejia saida suka zauna a Kankiya ta Jihar Katsina. kuma wadannan fulani suke Sarautar Hadejia har zuwa Yau.

3, MANGAWA:- Kabilar Mangawa ko Barebari wadanda mafi yawancinsu suna zaune a Gabas da Hadejia da kuma Arewacin kasar Sun zo ne A karni na goma sha bakwai (17) sun taho ne daga yankin Borno kuma mafiya yawansu sun zo kasar Hadejia ne Tonon Azurfa da Tagullah. Inda kuma daga baya wasu sun shigo kasar Hadejia A lokacinda RaBe yaci Kukawa da Yaki sai suka kaura suka dawo kasar Hadejia, Kamar garuruwan Birniwa, Baramusa, Kacallari, da Sauransu.

4, GIZMAWA:- Gizmawa suma kamar Mangawa sun shigo ne a Karni na goma sha bakwai (17) kuma suma suna zaune ne a yankin Guri, Marma, Lafiya da sauransu kuma suma yarensu kusan kamar barbarci ne saidai wasu kalmomin da yake canzawa.

5, BADAWA:- Kabilar Badawa basu da yawa a kasar Hadejia, kuma suna zaune ne a Garuruwan Iyakar Hadejia da Bedde, Kamar Gayin, Adiyani, Margadu,da Kadira. wasu sun zauna anan ne tun kafin yakin Gogaram. wasu kuma sunce dama anan suke tuntuni. ganin cewa suna iyaka ne da Kasar Bedde.

6; KOYAMAWA:- Kabilar koyamawa suma basu da yawa kuma Dangin Barebari ne, sai dai zanensu ya bambanta. kuma yarensu ma ba iri daya bane. Kuma suna cewa sun taho ne daga Gabas da Sudan. sannan suna zaune ne a Kasar Kafin Hausa, Bulangu, Yayari, koyamari da sauran garuruwan kasar Kafin hausa.

7; TIJJANAI:- Kabilar Tijjanai fulani ne dake zaune a Yelleman kuma Malamai ne masu bin Darikar Tijjaniyya. shi yasa ake ce musu Tijjanai. Sun shigo kasar Hadejia a shekarar 1903, Daga Malo a yankin Tukolar Senegal. sun taho ne bayan Turawan France sun yiwa Yankinsu Mulkin Mallaka. Sun taho karkashin jagorancin Shugabansu Muhammadu El-Bashir, kuma sun fara zama ne a Lokoja. Magajinsa kuma Ahmadu Madaniyyo sai ya sake tasowa daga Lokoja yazo Kasar Hadejia aka basu Wuri suka zauna. wato Yelleman Tijjanai. Alhamdu lillahi. Hadejia A Yau.