HADEJIA A YAU!
Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh.DR. Adamu Abubakar Maje C.O.N, ya halarcin taron yaye Dalibai karo na farko a jami'ar Kiwon lafiya dake Azare ta jihar Bauchi (Federal University Of Health Science)
An gudanar da wannan bikin wadda aka yiwa lakabi da "Maiden Convocation Ceremony for the Award of Degrees" a harabar makarantar da ke Azare a yau Asabat 17/10/2026, Oktoba, 2026. An karrama ɗaliban da suka kammala karatun su a wannan jami’a ta kimiyyar lafiya.
Wannan biki ya kasance wani muhimmin tarihi ga jami’ar, tare da nuna irin rawar da manyan cibiyoyin ilimi ke takawa wajen samar da ƙwararrun ma’aikata da za su taimaka wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya da ci gaban Najeriya.
Bayan wannan taro Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh DR. Adamu Abubakar Maje CON, ya sada zumunci da Sarakuna, ciki har da mai masaukin Baki Mai Martaba Sarkin Katagum Alh. Umar Farouk. Masarautar Katagum tana daya daga cikin masarautun da suke da zumunci tsakanin su da Masarautar Hadejia, wadda abokan wasa ne tun a zamanin da fulani suka rusa Daular Barno da ke da matsugunnin mulki a garin Ngazargamu.
Hadejia A yau.!Hadejia A yau








