TARIHIN KAFUWAR GANDUN BUNDUGOMA.
Daga Umar Yusuf Da'awa
A Zamanin Mulkin Sarkin
Haɗejiya Haru Bubba wadda ya yi mulki a shekarar 1865-1885 ne, kasuwa ta mamaye
Kudancin Haɗejiya, Ma'ana ɓagaren Kudu da garin Haɗejiya. Kasuwa ta kafu jama'a
sun shigo garin Haɗejiya, kama daga Turawa (Turkiyya) Larabawa dama Hausawammu na
gida da na wajen kasar nan.
Saboda shahara da Haɗejiya tayi na noman Gyaɗa da
Auduga da Dawa da Gero dadai sauran su, wannan tasa jama'a suka shigo Haɗejiya
daban daban. Haka aka yi ta kasuwanci a wannan yanki, har akwai lokacin da Jirgi
yakan sauka a Haɗejiya mai sauƙar Ungulu na larabawa da Turawa a basu Auduga da
gyaɗa, su kuma su kawo mana tufafin irin su Abaya da kayan mulki irin na gabas.
Kasuwa tayi ƙarfi jama'a sun cika, sai ɓarayi suka fara ziyartar wannan kasuwa
suna yin wasoso, har labari ya iskewa Sarki, nan take sarki ya tashi ɗaya daga
cikin Fadawansa a bangaren 'Yan Baka wadda ake ƙira da Bundugoma, yace yaje ya
sa ido ga yan kasuwa ya tabbatar sun yi saye da sayarwa lafiya babu tsoro.
Bundugoma ya amsa umarnin sarki, in ya tafi tun Safe har yamma shi da yaran sa
suna kula da 'yan kasuwa. Da yaga haka kawai sai ya tare wannan wuri gaba ɗaya
da zama, ya share fili ya gina bukkar sa tare da yaran sa. Wannan tasa har yau
ake ƙiran wannan wuri da Gandun Bundugoma. Bundugoma kuwa ana nufin mai Bindiga
a yaren Manganci, domin shi Bamange ne. Kuma sune suke Sarautar Galadiman
Bindiga a Hadejia. Kasuwa ta ci gaba da ci, kuma tafi cika ranar Lahadi saboda
Baki suna zuwa ne ranar Asabat su kwana lahdi su ci kasuwa su wuce.
A zamanin
sarkin Hadejia Abdulkadir Turawa suka umarci a dawo da kasuwa yamma da gari don
dacewa da zamani, sai kasuwa ta dawo duriyar yamma da gari wato Unguwar Rinde
inda kasuwa take yanzu.
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!