Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje C. O. N.!
Ranar Asabat 3-january-1999, Mai martaba sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje Haruna ya Nada Alh. Adamu Abubakar A matsayin IYAN HADEJIA, NA FARKO. Kuma Ranar Laraba 11-september-2002, Allah ya yiwa Mai martaba Sarkin Hadejia Rasuwa. Alh. Abubakar maje Haruna.
TO A SAKAMAKON AMINCEWA DA GWAMNATI TAYI DA ZABEN 'YAN MAJALISSAR SARKI WATO (KING MAKER'S) Suka zabi Iyan Hadejia Alh. Adamu Abubakar maje a matsayin sarkin Hadejia, Na Goma sha shida (16). kuma an nada shi Ranar Asabat 14-september-2002. Bisa Al'ada ba'a kwana uku ba tare da an nada Sarki ba.
HAWANSA NA FARKO A MATSAYINSA NA SARKIN HADEJIA SHINE Hawan sallar Azumi wato A watan Disamba 2002. Sannan sallar Layya February 2002 Bai Hau ba saboda yaje Saudiyya.
29-March-2003.
A YAU ASABAT 29-March-2003 ANYI BIKIN BADA SANDA! An baiwa sarkin Hadejia Sanda a Karkashin shugabancin Gwamnan Jigawa ALH. IBRAHIM SAMINU TURAKI! A FILIN WASAN KWALLON KAFA NA HADEJIA WATO (STADIUM).
Kuma bayan an Bashi Sandar jagorancin Kasar Hadejia A karkashin Tutar Shehu Usman Dan fodio, Mai martaba sarki yayi Hawa Guda Uku Wadanda suka Kayatar da jama'ar Hadejia.
1, BIKIN GASAR ALQUR'ANI A SECONDARY FANTAI
2,TARON DA AKAYI A MAKARANTAR KOFAR AREWA
3,SAI HAWAN GANDU WANDA SHIMA YANA DA TARIHI A MASARAUTAR HADEJIA.
Hakiman da ya fara Nadawa sune:-
1, DAN GALADIMA Alh.babbaji Adamu Hakimin waje.
2, SARKIN DAWAKI Alh. Umar Ibrahim Hakimin kiri kasamma.
3, KATUKAN HADEJIA NA (2) BIYU Hakimin Turabu. A gaba zan kawo muku Labarin Fitar sarkin Hadejia Rangadi da yayi da kuma Hakiman da ya Nada.