HADEJIA A YAU! Muna farawa da sunan Allah wanda da Ikonsa ne Komai ya Kasance da kuma Abinda zai kasance! Tsira da Aminci su kara tabbata ga Manzo (s.a.w.) wanda Allah ya aikoshi da zance Mafi dadi wato Alqur'ani.
A ranar Asabat 22/december/2012, Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar Maje (c.o.n.) zaiyi bikin cika shekar Goma yana Mulkin kasar Hadejia, A karkashin Daular Usmaniyya.
A ci gaba da kawo Muku Tarihin wadanda suka baiwa Kasar Hadejia Gudunmawa wajen ci Gabanta, yau zamu kawo muku Takaitaccen Tarihin Sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar Maje. Hadejia A yau!
An haifi Mai Martaba Sarkin Hadejia a shekarar 15/october/1960, a cikin garin Hadejia. Ya fara Makarantar primary a Abdulkadir pri.school Hadejia a shekarar 1967-1972, sannan Ya shiga Makarantar Secondary a Garin Ikot Ekpene Cross-river a shekarar 1973-1976, sannan ya koma Govt.sec.school Danbatta a shekarar 1976-1979.
Mai Martaba Sarki ya samu Nasarar shiga Makarantar Gaba da Secondary ta school of Rural and social science dake Rano ta jihar kano a shekarar 1981-1982, da kuma 1983-1985.
By Ismaila A sabo
Mai Martaba Sarki ya fara Aikin Gwamnati a tsohuwar Jihar Kano a ministry of social wellfare a shekarar 1982-1988, sannan ya koma Kano state pilgrim wellfare board a shekarar 1988-1991.
Bayan da aka kirkiro Jihar Jigawa Mai Martaba Sarkin Hadejia ya koma Jigawa state pilgrim board a shekarar 1991-1998. Sannan ya koma Ma'aikatar Kananan Hukumomi ta jiha a shekarar 1998-1999 Inda ya rike mukamin senior personnel officer.
A wannan shekarar ne Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje Haruna ya nadashi sarautar IYAN HADEJIA dan majalissar Sarki. Hadejia A yau!
A shekarar 2000-2002, ya rike Mukamin Sakataren Alhazai a Jigawa state pilgrim board.
A ranar Laraba 11/september/2002 Allah yayiwa sarkin Hadejia rasuwa Alh. Abubakar Maje Haruna, sakamakon zaben 'yan majalissar Sarki suka zabi Alh. Adamu Abubakar a Matsayin Sarkin Hadejia Na Goma sha shida (16).
Kuma an Nadashi ranar Asabat 14/september/2002. A karkashin jagorancin Galadiman Hadejia Alh. Habibu Adamu.
A ranar Asabat 23/march/2003, An baiwa Mai martaba Sarki Sanda, a karkashin Jagorancin Gwamnan Jihar Jigawa na wancan Lokacin Alh. Ibrahim Saminu Turaki. Hadejia A yau!
Muna Taya Mai martaba Sarki Murnar cika shekara Goma yana Mulkin Masarautar Hadejia.