"" /> HADEJIA A YAU!: 10/01/2026 - 11/01/2026

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, October 17, 2026

MAI MARTABA SARKIN HADEJIA YA HALARCI TARON YAYE DALIBAI A JAMI'AR AZARE

HADEJIA A YAU!

Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh.DR. Adamu Abubakar Maje C.O.N, ya halarcin  taron yaye Dalibai  karo na farko a jami'ar Kiwon lafiya dake Azare ta jihar Bauchi (Federal University Of Health Science) 

An gudanar da wannan bikin wadda aka yiwa lakabi da "Maiden Convocation Ceremony for the Award of Degrees" a harabar makarantar da ke Azare a yau Asabat 17/10/2026, Oktoba, 2026. An karrama ɗaliban da suka kammala karatun su a wannan jami’a ta kimiyyar lafiya.


Wannan biki ya kasance wani muhimmin tarihi ga jami’ar, tare da nuna irin rawar da manyan cibiyoyin ilimi ke takawa wajen samar da ƙwararrun ma’aikata da za su taimaka wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya da ci gaban Najeriya.

Bayan wannan taro Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh DR. Adamu Abubakar Maje CON, ya sada zumunci da Sarakuna, ciki har da mai masaukin Baki Mai Martaba Sarkin Katagum Alh. Umar Farouk. Masarautar Katagum tana daya daga cikin masarautun da suke da zumunci tsakanin su da Masarautar Hadejia, wadda abokan wasa ne tun a zamanin da fulani suka rusa Daular Barno da ke da matsugunnin mulki a garin Ngazargamu. 
Hadejia A yau.!Hadejia A yau


SARKIN YAKIN HADEJIA (ALHAJI SAIDU KANTI)

Hadejia A yau. 

Sarkin Yakin Hadejia Alhaji Sa'idu Kanti ya kasance fitaccen masanin harkar kuɗi kuma mai riƙe da sarautar gargajiya ta Sarkin Yaƙin Hadejia a Masarautar Hadejia. Ya halarci makarantar firamare ta elementary a Hadejia tsakanin shekarun 1948 zuwa 1952, sannan ya tafi Senior Primary School ta Hadejia (1952–1955). Bayan nan ya yi karatunsa na sakandare a makarantar Provincial Secondary School da ke Kano (1955–1957).

Ya yi aiki da babban kamfanin U.A.C. of Nigeria a matsayin mai kula da rumbun kaya (storekeeper) da sauran matsayi. Daga baya ya koma (Hadejia Native Authority), inda ya riƙe muƙamin babban mai karɓar kuɗi (cashier) a 1961, kuma ya zama babban Akanta/Ma'aji (Treasurer Accountant) a shekarar 1965.
Ya riƙe wannan matsayi na tsawon shekaru 10 har zuwa lokacin da aka naɗa shi Ma'ajin Ƙaramar Hukumar Hadejia a shekarar 1976. Ya rasu ranar 5/1/2013.

A cikin wannan hoton akwai Marigayi Abba Santare, Marigayi Dan Amar Mallam Ginsau, Marigayi Dan Iya Abdu, Marigayi Dan Buran Muhammadu, Alh. Idi Sakatare, Alhaji Sai'du Kanti Sarkin Yaki, Ma'aji Imamu da Jarma Sabo. Allah ya musu rahma.