Hadejia A yau.
Sarkin Yakin Hadejia Alhaji Sa'idu Kanti ya kasance fitaccen masanin harkar kuɗi kuma mai riƙe da sarautar gargajiya ta Sarkin Yaƙin Hadejia a Masarautar Hadejia. Ya halarci makarantar firamare ta elementary a Hadejia tsakanin shekarun 1948 zuwa 1952, sannan ya tafi Senior Primary School ta Hadejia (1952–1955). Bayan nan ya yi karatunsa na sakandare a makarantar Provincial Secondary School da ke Kano (1955–1957).
Ya yi aiki da babban kamfanin U.A.C. of Nigeria a matsayin mai kula da rumbun kaya (storekeeper) da sauran matsayi. Daga baya ya koma (Hadejia Native Authority), inda ya riƙe muƙamin babban mai karɓar kuɗi (cashier) a 1961, kuma ya zama babban Akanta/Ma'aji (Treasurer Accountant) a shekarar 1965.
Ya riƙe wannan matsayi na tsawon shekaru 10 har zuwa lokacin da aka naɗa shi Ma'ajin Ƙaramar Hukumar Hadejia a shekarar 1976. Ya rasu ranar 5/1/2013.
A cikin wannan hoton akwai Marigayi Abba Santare, Marigayi Dan Amar Mallam Ginsau, Marigayi Dan Iya Abdu, Marigayi Dan Buran Muhammadu, Alh. Idi Sakatare, Alhaji Sai'du Kanti Sarkin Yaki, Ma'aji Imamu da Jarma Sabo. Allah ya musu rahma.




No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!