Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, November 23, 2026

CHIGARIN HADEJIA ALHAJI LAWAN ZAKARI.

HADEJIA A YAU!

Alhaji Lawal Zakar (wadda a wani lokaci ake kira Zakari Lawal) shine Chigarin Hadejia na biyu a Masarautar Hadejia da ke Jihar Jigawa a tarayyar Nigeria.

Ga taƙaitaccen tarihin da ya shafi sarautarsa da asalinta a Masarautar Hadejia:

1. Asalin Sarautar Chigari a Hadejia

Sarautar Chigarin Hadejia sabuwar sarauta ce ta musamman a Masarautar Hadejia wadda Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji (Dr.) Adamu Abubakar Maje (CON), ya ƙirƙira tare da naɗa waɗanda suka cancanta domin taimakawa wajen gudanar da mulkin masarautar.

Chigarin Hadejia na Farko: Marigayi Alhaji Salisu Zakar (tsohon Kwamishinan Kasuwanci da Masana'antu na Jihar Jigawa kuma tsohon Shugaban Hukumar SUBEB) shine ya fara riƙe wannan sarauta har zuwa rasuwarsa a ranar 6 ga watan Agusta, 2022.

2. Naɗin Alhaji Lawal Zakar (Chigarin Hadejia na II)

Bayan rasuwar marigayi Alhaji Salisu Zakar, majalisar Sarkin Hadejia ta zaɓi Alhaji Lawal Zakar domin ya gaji wannan sarauta ta Dan Uwan sa. An nada shi ranar 30/September/2023, a fadar Mai martaba Sarkin Hadejia. 

• Ranar Tabbaatarwa: A ranar 26 ga watan Nuwamba, 2022, Majalisar Sarkin Hadejia ta umarci mutanen fada ƙarƙashin jagorancin Gidan Sallaman Hadejia da su tabbatar da Alhaji Lawal Zakar a matsayin sabon Chigarin Hadejia. Wannan yana daya daga cikin Al'adun Sarauta a Masarautar ta Hadejia. 

Gudunmawa da Zamantakewa

A cikin al'ummar Hadejia da Jihar Jigawa baki ɗaya, ana kallon Alhaji Lawal Zakar (Zakari Lawal) a matsayin dattijo mai dattako da kishin al'umma:

• Taimakon Al'umma: Ya shahara wajen tallafa wa matasa da 'ya'yan talakawa, musamman wajen samar musu da guraben ayyukan yi da hanyoyin dogaro da kai.

• Raya Al'ada: Yana taka muhimmiyar rawa a cikin majalisar fadar Sarkin Hadejia, musamman a lokutan bukukuwan gargajiya kamar Hawan Sallah da Hawan Sallar Gani.


Saturday, November 21, 2026

ISMAILA A SABO HADEJIA

HADEJIA A YAU!

HADEJIA A YAU!

ISMAILA A. SABO HADEJIA

Marubuci | Mai Tattara Tarihi | Ma'aikacin Gwamnati

Ismaila A. Sabo Hadejia Ismaila A. Sabo

Tarihin Rayuwarsa

Ismaila A. Sabo Hadejia an haife shi a ranar 22 ga Maris, 1977, a Unguwar Rumfa, cikin garin Hadejia, Jihar Jigawa.

Ya yi karatunsa a Abdulkadir Primary School, Government Day Secondary School Wunti, College of Islamic and Legal Studies Ringim, da Federal College of Education Kano.

Aikin Gwamnati

Ya fara aikin gwamnati a shekarar 2002. Yana aiki a bangaren Nature Conservation, ƙarƙashin Ministry of Environment, Jihar Jigawa.

Jagoranci

Shi ne Coordinator na ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative.

Littattafan da Ya Rubuta

1. Fulani da Mulkin su

Tarihin Fulanin Hadejia.

2. Ganuwar Hadejia da Kofofin ta

Tarihin ganuwar Hadejia da ƙofofinta.

3. Hadejia da Mutanen ta

Tarihi da Al'adun Hadejia.

4. Taurarin mu

Gudunmawar wasu mutanen Hadejia.

5. Fasaha Kyautar Allah

Tarihin Rayuwar Ahmadu Dan Matawalle da Wakokin sa.

Gudunmawa ga Tarihin Hadejia

Ta hanyar rubuce-rubuce da wallafa littattafai, Ismaila A. Sabo yana taimakawa wajen tattarawa da adana tarihin Masarautar Hadejia, al'adunta da tarihin fitattun mutanenta domin amfanin al'ummomin yanzu da masu zuwa.

HADEJIA A YAU!

Tarihinmu shi ne gadonmu.

Saturday, November 14, 2026

SHEIKH YUSUF SULEIMAN (MAI TA FADA)

HADEJIA A YAU!

Sheikh (Alaramma) Malam Yusuf Sulaiman Mai Tafada fitaccen malamin addinin Musulunci ne, mahaddacin Alƙur'ani mai girma (Alaramma), kuma babban malami a masarautar Hadejia da ke jihar Jigawa a Najeriya. 

Ga taƙaitaccen bayani game da shi da matsayinsa a cikin al'umma:

Matsayi da Ilimi: Ana yi masa laƙabi da Alaramma saboda zurfin iliminsa na Alƙur'ani mai girma da kuma bayar da gudunmawa wajen koyarwa da yaɗa ilimin addini a yankin Hadejia da ma kewaye. Mallam Yusuf ya fara karatun Allo da na Ilmi a wurin mahaifin sa, wato Sheikh Suleiman da ke Unguwar Mu'azu. 
Taimakon Al'umma: Al'ummar yankin Hadejia sun san shi sosai da kyauta, sadaka, da taimakon marasa ƙarfi, lamarin da ya sa ake kiransa da laƙubba irin su Garkuwan Malamai da Khadimul Ummah (Mai hidima ga al'umma). Mallam yana daukar nauyin marasa lafiya musamman masu karamin karfi wadda basu da hanyar da za su nemawa kan su magani a Asibiti. 
Gudunmawa a Masarautar Hadejia: Yana daga cikin manyan malamai masu daraja da ake girmamawa a fadar masarautar Hadejia, inda yake halartar manyan tarukan addini da na al'ada, ciki har da bikin buɗe sabon gidan tarihin masarautar Hadejia. Mallam yana halartar tarurruka musamman Wadanda suka shafi Addini da kuma gasar Alqur'ani mai tsarki. 


SARKIN ZAZZAU AHMAD NUHU BAMALLI.

HADEJIA A YAU!

Mai Martaba Ambasada Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, CFR, shine Sarkin Zazzau na 19, wanda ya hau karagar mulkin Masarautar Zazzau a ranar 7 ga Oktoba, 2020, bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau na 18, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, wadda ya rasu a ranar 20 ga Satumba, 2020, bayan shafe shekaru 45 yana mulki.

Sarki Ahmad Nuhu Bamalli ya kasance mutum mai ilimi da gogewa a fannoni daban-daban, ciki har da shari'a, harkokin banki, gudanarwa, diflomasiyya da shugabancin al'umma. 

Sarki Ahmad Nuhu Bamalli ya kasance mutum mai ilimi da gogewa a fannoni daban-daban, ciki har da shari'a, harkokin banki, gudanarwa, diflomasiyya da shugabancin al'umma. 

1. Haihuwarsa da asalin iyalinsa

An haifi Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a ranar 8 ga Yuni, 1966, a garin Zariya, Jihar Kaduna, Najeriya.
Ya fito ne daga gidan sarautar Mallawa, daya daga cikin manyan gidajen sarautar tarihi a Masarautar Zazzau. Mahaifinsa shine Alhaji Nuhu Bamalli, wadda ya taba rike mukamin Magajin Garin Zazzau, sannan ya yi aiki a gwamnatin Najeriya a matsayin Ministan Harkokin Waje.

Kakansa shine Sarkin Zazzau Alu Dan Sidi, wadda ya kasance sarki daga gidan Mallawa. Wannan zuriyar ce ta sa Ahmad Nuhu Bamalli ya kasance daya daga cikin 'ya'yan gidan sarautar da ke da alaka ta tarihi da gadon sarautar Zazzau. 

2. Karatunsa da neman ilimi

Sarki Ahmad Nuhu Bamalli ya fara karatunsa na firamare da sakandare a cikin garin Kaduna. Bayan kammala karatun sakandare, ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi karatun shari'a (Law), ya kuma kammala digirinsa na farko a shekarar 1989. Daga baya ya ci gaba da neman ilimi a fannoni daban-daban, inda ya samu:
Digiri na farko a fannin shari'a (LLB), 1989.

Postgraduate Diploma a fannin Management, 1998.

Digiri na biyu a fannin International Affairs and Diplomacy, 2002.

Horon Conflict Resolution a Jami'ar York, Birtaniya, 2009.

General Management Programme a Harvard Business School, 2011.

Diploma a fannin Organisational Leadership daga Jami'ar Oxford, 2015.

Wadannan karatuttuka sun taimaka wajen gina kwarewarsa a shugabanci, diflomasiyya da gudanar da harkokin jama'a. 

3. Tafarkin aikinsa da gogewarsa

Kafin ya zama Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya yi aiki a hukumomi da kamfanoni daban-daban a Najeriya. Ya shafe kusan shekaru 26 yana gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban na tattalin arziki da gudanarwa.

Daga cikin wuraren da ya yi aiki akwai:
Kamfanonin hada-hadar kuɗi da bankuna.
Abuja Metropolitan Management Agency. Nigerian Mobile Telecommunications Limited (MTel), inda ya rike mukamin kula da ma'aikata.

Nigerian Security Printing and Minting Corporation, inda ya rike mukamin Executive Director, sannan ya zama Acting Managing Director. Kaduna State Independent Electoral Commission, inda ya yi aiki a matsayin kwamishina.

A lokacin da yake gudanar da wadannan ayyuka, ya samu gogewa wajen shugabanci, tafiyar da hukumomi da hulda da al'umma.

4. Ayyukansa a fannin diflomasiyya

A shekarar 2017, tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Jakadan Najeriya a kasar Thailand. Ya kuma rike wakilcin Najeriya a kasar Myanmar a lokaci guda. A matsayinsa na jakada, ya kasance daya daga cikin wakilan Najeriya da ke gudanar da hulda tsakanin kasashen biyu, tare da wakiltar muradun Najeriya a harkokin diflomasiyya. Ya ci gaba da wannan aiki har zuwa shekarar 2020, lokacin da aka nada shi Sarkin Zazzau. 

5. Sarautar Magajin Garin Zazzau

Kafin hawa karagar mulkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya kasance Magajin Garin Zazzau. Wannan sarauta ce mai matukar muhimmanci a tsarin sarautun Masarautar Zazzau.
Ya gaji wannan sarauta ne daga mahaifinsa, Alhaji Nuhu Bamalli, bayan rasuwarsa a shekarar 2001.

Matsayinsa na Magajin Garin Zazzau ya kara tabbatar da kusancinsa da al'adun sarauta da tsarin gudanarwar masarautar.

6. Hawansa karagar mulkin Masarautar Zazzau

A ranar 7 ga Oktoba, 2020, Gwamnan Jihar Kaduna na lokacin, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da nadin Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19. Nadin nasa ya kasance wani muhimmin lamari a tarihin masarautar, domin shine sarki na farko daga gidan Mallawa da ya dawo kan karagar mulkin Zazzau bayan kusan shekaru 100.

Kakansa, Alu Dan Sidi, shine sarki na karshe daga wannan gidan kafin dawowar gidan Mallawa kan karagar mulkin a shekarar 2020. 

Muhimmancin dawowar gidan Mallawa. Dawowar gidan Mallawa kan karagar mulkin Zazzau a shekarar 2020 wani muhimmin babi ne a tarihin masarautar. Wannan lamari ya nuna ci gaba da kasancewar tsarin gidajen sarauta da zuriyarsu a tarihin Zazzau.

Ahmad Nuhu Bamalli ya zama sarki na 19 tun bayan kafuwar jerin sarakunan masarautar a shekarar 1804, kamar yadda fadar Shugaban Najeriya ta bayyana a sanarwar taya shi murnar cika shekaru 60 a 2026. 

7. Matsayinsa a yau

A halin yanzu, Mai Martaba Ambasada Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, CFR, shine Sarkin Zazzau, kuma yana jagorantar Masarautar Zazzau daga fadarsa da ke Zariya, Jihar Kaduna.

Matsayinsa ya hada da jagorancin gargajiya, kula da al'adun masarauta, da wakiltar masarautar a muhimman harkokin al'umma da na kasa. Gwamnatin Jihar Kaduna ma tana bayyana shi a matsayin Sarkin Zazzau a shafinta na hukuma. 

Madogarar bincike
Radio Nigeria Kaduna – Nadin Sarkin Zazzau, 2020⁠.

Channels Television – Tarihin nadinsa⁠.

State House Nigeria – Sakon taya shi murnar cika shekaru 60, 2026⁠.

Gwamnatin Jihar Kaduna – Jerin sarakunan gargajiya⁠.

Hadejia A yau communication and media services. 14/11/2026. 




Thursday, November 5, 2026

SARAUTAR BARDE KERARRIYA

HADEJIA A YAU!

TARIHIN SAR AUTAR BARDE KERARRIYA

Asali, Kirkirarta da Wadanda Suka Rike Ta a Masarautar Kano da Hadejia. 

Gabatarwa

Sarautar Barde Kerarriya (wadda wasu ke kira Barde Kirkirarriya) na daga cikin sarautun gargajiya da ke da tarihi a masarautun Hausawa. Wannan sarauta ta samo asali ne daga Masarautar Kano, kafin daga bisani ta samu gindin zama a wasu masarautu, ciki har da Masarautar Hadejia.

Asalin Sarautar Barde Kerarriya

A cewar tarihin baka, Sarkin Kano Kutumbi, wanda ya yi mulki daga shekarar 1628 zuwa 1648, shi ne sarkin da ya fara kirkirar wannan sarauta.

An bayyana cewa dalilin kirkiro sarautar ya samo asali ne lokacin da Sarkin Kano Kutumbi yake shirin tafiya yaƙi. A lokacin ne ya bukaci a nada masa Barde. Sai aka sanar da shi cewa akwai Barde Rube a waje. Daga nan sai ya ce wa wanda za a nada din: "To, kai ka zama Barde Kerarriya." Wato Barde da aka kirkira a wannan lokaci.

Wani Kaulin Game da Asalin Sarautar

Akwai wani kauli na daban da ke bayyana cewa lokacin da Sarkin Kano yake shirin fita yaƙi, ya yi bankwana da iyalansa. Daya daga cikin 'ya'yansa ya nemi ya bi shi zuwa fagen fama, amma mahaifinsa bai amince ba.

Sai yaron ya sulale da kansa, ya fasa kofa ya bi hanyar zuwa wajen abokan gaba, inda ya kai musu farmaki har ya samu nasara kafin isowar Sarkin.

Bayan Sarkin ya isa wurin, ya fahimci abin da yaron ya aikata, sannan ya ba shi lakabin Barde Kerarriya.

Wadannan kauloli biyu na daga cikin bayanan da ake dangantawa da asalin wannan sarauta a tarihin baka.

Wasu Daga Cikin Masu Rike da Sarautar a Masarautar Kano

1. Alhaji Muhammad Kabiru Bayero

Alhaji Muhammad Kabiru Bayero na daga cikin wadanda suka rike sarautar Barde Kerarriya a Masarautar Kano. An nada shi wannan sarauta a shekarar 1955, a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I.

Ya kuma rike mukamin Hakimin Garki, wadda a wancan lokaci take karkashin tsarin mulkin Masarautar Kano, kuma a yau tana cikin Jihar Jigawa.

Ya rasu a shekarar 1999.

2. Alhaji Shehu Kabir Bayero

Alhaji Shehu Kabir Bayero ma na daga cikin wadanda suka rike sarautar Barde Kerarriya. Ya kasance Hakimin Gwarzo/Takai.

Ya rasu a watan Satumba na shekarar 2026 a kasar Masar.

Shigowar Sarautar Barde Kerarriya Masarautar Hadejia. 
A Masarautar Hadejia, an fara kafa sarautar Barde Kerarriya ne a shekarar 2002, a zamanin mulkin marigayi Sarkin Hadejia, Alhaji Abubakar Maje Haruna.

Wanda aka fara bai wa wannan sarauta a Masarautar Hadejia shi ne marigayi Barde Kerarriya Alhaji Haruna Malamiyo, wanda yake dan Tafidan Hadejia Umaru, dan Sarkin Hadejia Haruna Mai Karamba ne.

A lokacin nadinsa, an kuma ba shi Gundumar Sarawa domin ya rike ta a matsayin Hakimi. Daga baya kuma an sauya masa gunduma har sau uku a tsawon lokacin da yake rike da sarautar.

Alhaji Haruna Malamiyo ya rasu a shekarar 2025.

Alhaji Usman Malamiyo: Magajin Sarautar Barde Kerarriya

Bayan rasuwar marigayi Alhaji Haruna Malamiyo, sai aka nada dansa, Alhaji Usman Malamiyo, a matsayin magajin sarautar Barde Kerarriya a Masarautar Hadejia.

Alhaji Usman Malamiyo sanannen mutum ne a cikin Masarautar Hadejia, musamman wajen hulda da jama'a da kuma jibintar al'amuran al'umma.

Shi ma'aikacin Gwamnatin Tarayya ne, kuma ya taba tsayawa takarar Majalisar Tarayya.


An nada shi sarautar Barde Kerarriya a ranar 27 ga watan Disamba, 2025. A halin yanzu kuma shi ne Hakimin Gundumar Dumadumin Toka a Masarautar Hadejia.

Kammalawa

Tarihin Sarautar Barde Kerarriya na nuna yadda sarautun gargajiya ke da muhimmiyar rawa wajen tafiyar da al'amuran al'umma, musamman a bangaren shugabanci, tsaro, al'adu da kula da jama'a.

Daga Masarautar Kano zuwa Masarautar Hadejia, wannan sarauta ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin sarautun gargajiya masu muhimmanci a tsarin sarautar gargajiya.

Hadejia A Yau – Adana Tarihi, Al'adu da Gadon Masarautar Hadejia.