Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, November 21, 2026

ISMAILA A SABO HADEJIA

HADEJIA A YAU!

HADEJIA A YAU!

ISMAILA A. SABO HADEJIA

Marubuci | Mai Tattara Tarihi | Ma'aikacin Gwamnati

Ismaila A. Sabo Hadejia Ismaila A. Sabo

Tarihin Rayuwarsa

Ismaila A. Sabo Hadejia an haife shi a ranar 22 ga Maris, 1977, a Unguwar Rumfa, cikin garin Hadejia, Jihar Jigawa.

Ya yi karatunsa a Abdulkadir Primary School, Government Day Secondary School Wunti, College of Islamic and Legal Studies Ringim, da Federal College of Education Kano.

Aikin Gwamnati

Ya fara aikin gwamnati a shekarar 2002. Yana aiki a bangaren Nature Conservation, ƙarƙashin Ministry of Environment, Jihar Jigawa.

Jagoranci

Shi ne Coordinator na ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative.

Littattafan da Ya Rubuta

1. Fulani da Mulkin su

Tarihin Fulanin Hadejia.

2. Ganuwar Hadejia da Kofofin ta

Tarihin ganuwar Hadejia da ƙofofinta.

3. Hadejia da Mutanen ta

Tarihi da Al'adun Hadejia.

4. Taurarin mu

Gudunmawar wasu mutanen Hadejia.

5. Fasaha Kyautar Allah

Tarihin Rayuwar Ahmadu Dan Matawalle da Wakokin sa.

Gudunmawa ga Tarihin Hadejia

Ta hanyar rubuce-rubuce da wallafa littattafai, Ismaila A. Sabo yana taimakawa wajen tattarawa da adana tarihin Masarautar Hadejia, al'adunta da tarihin fitattun mutanenta domin amfanin al'ummomin yanzu da masu zuwa.

HADEJIA A YAU!

Tarihinmu shi ne gadonmu.

No comments:

Post a Comment

RUBUTA RA'AYINKA!