"" /> HADEJIA A YAU!: 03/01/2014 - 04/01/2014

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, March 17, 2014

TARIHIN JARMAN HADEJIA ALH. ABBA SAMBO (DAGA NA GABA PART FIVE 5)

TAKAITACCE TARIHIN MAIGIRMA JARMAN HADEJIA ALH. ABBA SAMBO!!
Daga Muhammad Yawale.




An haifi Alh. Abba sambo a shekara ta 1943 a cikin garin hadejia, ya fara karatun allo a matakin karatunsa na farko sannan lokacin ya isa shiga makarantar boko. Ya fara da hadejia junior elementary school dake dalla wanda a yanzu ake kira Abdulkadir primary school a shekarar 1953-1957 a garin hadejia. Bayan ya kammala wannan makarantane ya samu shiga middle school a cikin shekarar 1957-1959, daga nan bayan kammala middle school ya koma makarantar horan malamai ta wudil/bichi teachers collage a shekarar 1960-1965.


Bayan kammala wannan karatune ya samu zama headmaster a garin gabas primary school a shekara ta 1966-1971, ya koma karin karatu a advance teachers collage zaria a cikin shekara ta 1971-1974 wanda ya samu certificate in education (NCE). Bayan kamamala (NCE) bai tsaya ba domin samun degree na farko a fannin physical Health Education (PHE) wanda ya kammala a 1975-1978 ABU Zaria. Yayi hidimar kasa (NYSC) a federal advance teachers collage dutsinma katsina state daga 1978-1979.

Wasu ayyuka da yayi:
(1) mataimakin shugaban wasannin motsa jiki gwamnatin tarayya (NSSF) 1985-1989
(2) wakili a hukumar ilimi mai zurfi ta jami'ar Ahmadu
bello dake zaria 1988-1991 
(3) wakilin tantance jarabawar dalibai na kasashen africa 1995. 

(4) shugaban wasannin motsa jiki na makarantun jihar jigawa.


Mukaman da ya rike: (1) shugaban makarantar primary ta garun gabas.(2) jami'i mai kula da shiyar kudu maso yamma wadda take birnin kudu a jihar kano (3) mataimakin shugaban kwalejin makarantar horarda malamai dake garin hadejia (4) mataimakin jami'in ilimi na shiyoyin kananan hukumomin gezawa, da minjibir a jihar kano (5) shugaban makarantar sakandiren jeka ka dawo dake kazaure (6) shugaban kwalejin horar da malamai ta garki. Da sauransu.

Jarman hadejia ya bar aiki ranar 30th ga watan oktoba, 2001 a matakin aiki na 16/17. Bayan rasuwar marigayi jarman Hadejia Alh. Usman sambo na (2) a ranar Asabat 4 ga watan december 2010, maimartaba sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar maje Con, ya nada ALH. ABBA SAMBO a matsayin JARMAN HADEJIA na (3) a gidan Tafarki Guruza, Jarman Hadejia na biyar (5) a jerin Sarautar Jarma a kasar Hadejia kuma Dan majalisar maimartaba sarki.
HADEJIA A YAU....

Thursday, March 6, 2014

TAURARINMU HADEJIAWA (Part four 4)

DAGA MUHAMMAD IDRIS



Hadejia A yau! 

FARFESA HARUNA WAKILI...............Farfesa Wakili haifaffen kofar fadar Hadejia ne, kuma kamar yadda sunansa ya nuna mahaifinsa shi ne Wakilin kudun Hadejia [Dandalma] wato mai kula da yankin kudancin garin Hadejia.

Farfesa Wakili shi ne Farfesa na biyu a masarautar Hadejia kuma yana daya daga cikin `yan majalissar dattijai na Jami`ar Bayero ta kano kuma babban Alaramma a tsangayar tarihi ta makarantar, harwayau shi ne Mufti akan harkar tarihi a Arewacin kasar nan dominkafafen watsa labarai da dama na ciki da wajen Nijeriya suna dogara da fatawowinsa wajen warware matsalolin tarihi da suka bujuro musu.Baya da harkokinsa na cikin Jami`a Farfesa Haruna Wakili ya rike Daraktan Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami`ar wato MUMBAIYA dake Gidan Malam Aminu Kano a Unguwar Gwammajar kano.

" Na zaune bai ga gari ba", wanda bai sanJami`a ba, ba zai san gudunmawar Wakiliba domin a shekaru ashirin da biyar da suka gabata duk dan masarautar Hadejia da ya je Bayero ofishin Wakili ne zangonsa, shi kansa ba zai iya kididdige daliban da ya yi wa hanyar karatu a jami`a ba.

"Mai kamar zuwa kan aika" Yana cikin wannan gwagwarmaya Allah [swt] ya yi masa kwamishinan Ilmi na Jihar Jigawa. wannan mukami nasa duk Bahadeje mai hankali ba zai taba mantawa da shi ba domin baya da ci gaba a gyaran makarantu da samar da aiyuka da matasa da ya yi to kuma a lokacinsa babbar bukatarmu da muka dade muna nema ta neman babbar makaranta ta kai ga biya wato muka samu Jami`ar Kafin Hausa kuma aka gina babbar makarantaraiyukan gona ta Hadejia ta bar lungu ta dawo kan hanya.

Farfesa Haruna Wakili cikakken Bahadeje ne ba ya son raini amma yana da kishin al`ummarsa yana son ci gabansu kuma saboda daga darajar wannan masarauta shi rubutunsa ma na digirinsa na biyu akan wannan Masarauta ya yi.a takaice dai rayuwarsa akan bautawa Ilmi take.Hadejawa suna addu`a Allah Ya ba gwanin yafe gwado.



FARFESA HARUNA BIRNIWA............kamar yadda sunansa ya nuna Farfesa Haruna Birniwa haifaffen garin Birniwa ne kuma yana cikin haular masu mulkin garin.Birniwa shi ne farfesa na farko a cikin wannan masarauta kuma farfesa nabiyu a fadin Jihar Jigawa.


Gaba daya rayuwar Birniwa a kan bautawa Ilmi take domin ya kasance daya daga cikin dattawan malamai a Jami`ar Danfodiyo dake Sokoto na shekaru masu yawa kuma ya rike 'provost' a kwalejin Ilmi dake Gumel sannan ya rike kwamishinan Ilmi a wannan Jiha.

Farfesa Birniwa ya bayarda gudunmawa a fagen bayarda ilmi a Jihar nan matuka domin daruruwan mutane sun ci moriyarzamansa a sokoto domin shi 'admission' a wurinsa kamar mutum ya mari budurwa ne don haka za a ya ce wa shi ne ya budewa Hadejawa kofa a sokoto kuma bai bar sokoto ba sai da ya yi dashe.
Lokacin yana 'provost' ma masu rabo sun samu aiki a wurin.Birniwa ba harkar ilmin zamani kadai ya tsaya ba domin fakihi ne a fannin addini kuma fahintarsa da addini ta kara sa kyawawan halayensa sun kara kyautata domin mutum ne mai hakuri da gaskiya da rikon amana da saukin kai.wani abun sha`awa ga halayensa mai unguwarsa a Hadejia ya ce in dai yana gari duk yadda za a je neman ci gaba da shi ake yi. munaaddu`a Allah ya albarkaci bayansa.

Saturday, March 1, 2014

DAGA NA GABA! HADEJIAWA (PART TWO 2)





DAGA HASHIM AMAR...
MUHAMMAD (ABBAS SECRETARY)- Tsohon Sakataren kananan hukumomin Hadejia, Malam Maduri, SuleTankarkar da Guri; tsohon jami'in kula dajin dadin jama'a, a halin yanzu Akawun Majalisar dokoki ta Karamar Hukumar Guri(Clerk).

Wannan bawan Allah ya taka rawar gani wurin samar wa matasa da dama aikin yia lokacin da yake mukamin Sakatare musamman a Hadejia da Guri. Na san mutane da dama da wannan mutum ya samawa aikin yi, cikin su kuwa har da ni kaina.

HAJIYA SABUWA SHEHU- Shohuwar jami'ar ilmi, tsohuwar shugabar makarantar firamare, tsohuwar Sakatariyar ilmi ta Karamar Hukumar Hadejia; daya daga cikin mata 'yan boko na farko a Kasar Hadejia. Wannan baiwarAllah ta taimaka matuka wurin ci gaban ilmin mata a wannan yanki, ita ce ta dauki mafi yawanmata Malaman Makaranta a Hadejia.

Ta wani bangaren 'yar kasuwa ce da ta samar da aikin yi ga matasa ta wannan bangaren, ita ta kafa shagon gudanar da harkokin sarrafa na'ura mai kwakwalwa (Bussiness Centre)na farko a Hadejia. A yanzu haka 'yar kwamitin kwararru ce masu kula da aiyukan Bankin Duniya a Hadejia. Kuma ta na cikin kwamitin kula da Makarantun Firamare da Bankin duniya suka gina a Hadejia.

Wani abin sha'awa ita ta samar da filin ginin daya Makarantar (Shagari Community), ta nemi filin a hannun Karamar Hukumar Hadejia a  madadin LEA, filin yana hannun ta fiye da shekaru goma. Hajiya Sabuwa ta bayar da tsohongidan ta kyauta ga hukumar ilmi (LEA Hadejia) don gina Makaranta, gidan na unguwar Chadi. Allah Ya saka mata da alkhairi, ya yawaita mana irin ta.