"" /> HADEJIA A YAU!: 01/01/2017 - 02/01/2017

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, January 15, 2017

SARKIN MUSULMI SIR. ABUBAKAR III.

HADEJIA A YAU!


SARKIN MUSULMI ABUBAKAR. 
Cikin 1902, ana kamar badi Turawa zasu zo Sokoto anka haifeni a wani gari wai shi Dange. Tun ina dan shekara Bakwai (7) Marigayi Sarkin Musulmi Hassan ya riĆ™e ni, da na dan yi wayo na isa fara karatu, da yake Sarkin Musulmi Malami ne bai kai ni kowace makaranta ba, sai ya tsareni nan gaba nai shina koya min karatu. Shina kuma kula dani da hana ni yawan Shedana irin ta yara. 

Lokacin da Sarkin Musulmi Hassan ke Mallamin Uban Kasar Dange (Hakimin Dange),  da na fara ido wajen Karatu sai nayi ta taimako nai wajen Aikinga. Muna nan haka cikin Shekarar 1923, Sarkin Musulmi Hassan ya sami Sarautar Sarkin Bauran Dange. Da ya sami wannan Sarautar ni kuma sai ya maishe ni matsayi nai na zama ni am Mallami nai. (Malamin Hakimi). 

Muna nan haka har cikin shekarar 1931, Allah ya nufa Sarkin Musulmi Hassan ya zama Sarkin Musulmi. Da anka natsa sai ya dauko ni daga Dange ya maida ni Sokoto ya nada ni Sardauna, na zama daya daga cikin mataimaka nai ga harkokin kasa.  A cikin Birni kuma ya sa in rinka kula da dukkan wurare na Aiki, kamar su Gidan Yari,  Gidan Ayyuka, likitocin Shanu, Gandun Daji, Dagarawa da dai Sauransu. A wannan lokacin har Kaduna nazo koyon Aikin 'yan Doka dan in samu sanin hanyar taimakonsu. In ko na fita Rangadi in ka jini a wajen wanga Uban kasa yau gobe sai ka jini a wajen wancan, musamman lokacin Haraji ko Jangali. Wani lokaci nakanyi wata biyar ko shida ban leko cikin Birni ba. 

Muna nan haka sai anka yi mani  Uban Kasar Talatar Mafara, nayi watanni hudu (4) ina wagga Sarauta, sai Allah ya yiwa Sarkin Musulmi Hassan rasuwa cikin Shekarar 1938, Allah shi gafarta masa Amin. Bayan rasuwa tai ni kuma Allah ya kawo ni wagga Matsayi. Ina fatan Ubangiji Allah shi taya ni rikawa. 

Sarkin Musulmi Abubakar shine dan Usman,  Usman dan Sarkin Musulmi Mu'azu (wato uban Marigayi Sarkin Musulmi Hassan) Sarkin Musulmi Mu'azu dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, Sarkin Musulmi Bello dan Shaihu Usman Dan Hodiyo. Allah shi gafarta musu baki daya Amin. 

Sarkin Musulmi Abubakar bai shiga makarantar Turawa ba amma ya koyi Rubutu da Karatu irin nasu. Sarkin Musulmi Abubakar  shine Sarkin da yafi kowa dadewa a Sarautar Sarkin Musulmi, domin ya shekara Hamsin yana kan Halifar Shehu  Usman Dan Hodiyo. Ya fara Sarauta tun lokacin Turawa,  An nada shi ranar 17/yuni/1938, Razdan na Sokoto  Commander J. Carrow shine ya nada shi. Sarkin Musulmi Abubakar yayi Aiki da Gwamnatoci  Takwas (8), a Nigeria bayan samun 'yancin  Kai.  Bayan zamansa Sarkin Musulmi shine ya Baiwa Ahmadu Bello Sarautarsa ta Sardauna a cikin shekarar 1938. Ya rasu yana da shekaru 85 a Duniya,  ya rasu a cikin shekarar 1988. Allah ya Gafarta masa da rahma tare da Al' ummar Annabi baki daya. 


Madogara....... 
1. Sultan Abubakar lll, Littafin Jean Boyd da Hamzat M. Maishanu.
2. Sultan Muhd. Maccido  in the shadow of his Ancestors,  Littafin Hassana Isma'ila Bichi.
3. Gaskiya ta fi Kobo ta Hudu (4) 1939.