Sarautar Barde, sarautar ce ta Habe wacce Fulani suka gada bayan Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, kuma sarauta ce ta Mayaka ko Jarumai. Ma'anar sarautar Barde ita ce, duk lokacin da sarki zai yi wata tafiya mai nisa, Barde zai kasance a gaba har sai ya tabbatar da masaukin Sarki akwai kyakkyawan tsaro a wurin kafin Sarki ya iso ya sauka. Kuma yana binciken inda abokan gaba suke lokacin yaki sannan yana binciken inda abokan yaki suka buya don kawo harin samame.
UNGUWAR TUDUN BARDE HADEJIA 1808 Ca
Wannan unguwa mai suna a sama, (Unguwar Tudun Barde) ta samo sunan ta ne daga Barde Risku shugabanr rundunar yakin Hadejia, shi ne ya fara sarautar Barde a Haɗejiya.
Barde Risku mutumin Takoko ne ta karamar hukumar Mallam Madori shi ne wanda mahaifin sa ya hada shi da Sarki Sambo lokacin jihadi bisa dalilin gayyatar mahaifin da Sarki Sambo yayi, yana da yar'uwa wanda Sarki Sambo ya aura wato DIBI mahaifiyar Sarki Buhari.
Barde Risku shi ne wanda da Sultan ya mikawa Sarki Sambo tuta shi kuma ya mikawa Risku, wannan tasa a lokacin sa Tuta da shemar da ake kafawa lokacin yaki suke karkashin kulawar sa.
Unguwar Tudun Barde tana Kudu masu yamma da fadar Haɗejia daga cikin ta aka samuTudun Mabudi koda yake babu unguwa Tudun Mabudi a hukumance.
Barde Risku yana da da guda daya da ya tabbata a tarihi wato Barde Fannami.
Kamar yadda tarihi na kunne ya girmi kaka ya nuna, bayan Sarkin Hadejia Sambo ya shiga garin Hadejia duka qasa ta zama tasa sai ya tasamma gyare gyare tare da nada hakimai da zasu taya shi jagoranci kasar Hadejia. Sambo ya nada hakimai daga kowanne bangare na kabilun da suke kasar Hadejia, wannan tasa ya nada Risku daga bangaren Kanuri. Daga wannan lokacin zuwa yau ga jerin mutanen da suka yi Sarautar Barde....
1. Barde Risku
2. Barde Fannami
3. Barde Dandaku
4. Barde Zangoli
5. Barde Ibrahim Hassan
Babangida Mukhtar Hadejia.