AMSHI - Haka nan ne malam Ahmadu masu fasaha kanda gwamna kai aka yiwa firimiya.
1, Bismillah waka nai nufi tarihin malam amadu na hadejia wanda ake fadi.
2, A watan august ran litinin kwana daya nai wakar nana tarihin mai girkin dina.
3, Zamanin nan a Hadejia shi ba sarkin samari bane Allah ne yai masa martaba.
4, 'ya'yan sarki da na hakimai talakawa 'ya'yan tajirai a gidansa ake girkin dina.
5, zamanin nan a Hadejia abinda ya shirya babu mai rushewa malam amadu.
6, sai malam yai musu shawara aduba budurwa mai mukami Hadejia ayi mata gwamnati.
7, samari sai sukace masa a dallah asa mai jidda domin tafi budurwar zamani.
8, gurinda take ban al'ajab bata fushi mai jidda bata da girman kai kuma ga ladab.
9, in tana zance fa murmushi ga karamar murya a gunta kamar 'yan matan india.
10, sunan mai jidda hawa'u gwamnan 'yan mata a hadejia.
Allah sarki duniya!
HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Sunday, February 12, 2012
Saturday, February 11, 2012
WAKAR MALAM AMADU DAN MATAWALLE! DAGA ISMAILA A SABO HADEJIA.
Amshi- Hakane malam amadi na idi ka kara shiri duniya ta Allah ce malam amadi.
1, Ku saurara jama'a zana baku labarin malam amadu, sa'ar Bayero sarkin kano yana mulki malam amadi.
2, Yajeshi kano ranar litinin ya dawo malam ran laraba, ana masha'a kwana takwas ciroma sunusi yana hakimi.
3, Yajeshi kano gun maina bashir da sarkin shanu da malam haruna su duka 'ya'yan sarkinmu ne.
4, Yajeshi kano suka gaisa dashi, domin shi mai kaunarsu ne, sa'ar da yajeshi ya samesu duk suna middle ba'a tasosu ba.
5, Malam sai ya wuce har bichi, yaje gurbin wambai Abubakar shima mai kaunarsa ne.
6, Wambai dan sarkin duniya, duk a kano ba tamkar Abubakar wane jikan sarki Alu.
7, Kyawu dan sarki ai a sanshi mai kyauta da halin arziki wambai yayi halin arziki.
8, Sai kuma taken malam na sidi ban kwana da mutanen kano malam zaya tsaya zakirai.
9, Malam yayi shirin duniya da safe da yamma mutane kuji, domin rainin wayon mahassada da magauta baya sake.
10, Yafi zuma zaki na haruna amma in ba'a fareshi ba, malam in aka fareshi ko madaci baiyi ya dacinsa ba.
11, Malam amadu ne kokuwar tabo ba dadi wan shekara, in kaine kayi kayen ka baci in ma kai aka kayar ka baci wanda ka duba kowa tabo.
12, Malam amadu ne kainuwa dashen Allah yaya zakuyi, wanda ya zauna kayin mahassada sai ya kauce zasu kau, ruwa sai ya kare kainuwa ta kare ba'a ga bayanta ba.
13, Malam amadu in yai adonsa randa yasa riga koriya, in ya fito ya kore mahassada sai yanda yace zasuyi.
14, Dumau yake ba fashi ko cikin sa'a daya bashi da dadin gamo, bangon dutse in kaki masu sarawa da diga sa gaji.
15, Talau yake kaifin adda na sidi malam mai zurfin hankali, tilan dan badi ko an daka a turmi sai ko yakai badi.
16, Zabgai yabin Bauchi da kare dangi maza sai kuy hankali, malam amadu baya sake kanin darasuma na malam barau.
17, Alqur'ani yaro da saurayi da budurwa in babu gaskiya aka dafa asha wuya.
18, Sarkin 'yan mata gaskiya wuka ce inda ka dokata sai ta kama mai nasara dole gaskiya tafi karya dadin fada.
19, Kaka sara kaka Hadejia kwado yaci kunama ashe, ko ya kama kafin ya karta su duka kowa yasha wuya.
20, Malam yai baiti sha tara, sai na cikon ashirin wanda zaya sanya dan ya zamo gargadi.
21, Mai gina ramin keta gina gajere dan juyin zamani, karka haka da tsawo domacin na baya su zosu suna shan wuya.
22, Tamat wa bi hamdi ilallahi zana saurara waka ta cika.
Subscribe to:
Posts (Atom)