"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, November 27, 2012

MANYAN 'YAN SIYASAR HADEJIA

Hadejia A yau. Wadannan mutane sune Ruhin siyasar Hadejia! Gudunmawar da suka bayar a siyasa da ci gaban yankin Hadejia sai dai Allah ya saka musu da Alkairi. Sunyi siyasa a lokacinda ba'a san Daga kai sai 'ya'yanka ba! Domin sun kafa mutane da dama a Hadejia da kewaye. Duk unguwa zakaga akwai mutanenda suka kafa a siyasa. Lalle sun cancanci yabo. Idan muka fara da Marigayi Alh. Bello Auyo zamuga cewa Ayyukanda yayi a Hadejia har yanzu babu wani ko wata gwamnati da tayi makamancin nasa. Kama da Secretaria, Maternity, da sauran abubuwanda har yau ana amfana dasu a Hadejia. Allah ya kyauta kwanciya. Mallam Ibrahim Kwatalo shima ya gina mutane daban daban a Tarihin siyasar Kasar Hadejia. Duk Wanda yanzu yake Cikin Gwamnati, in ba yaronsa ba sai wanda shine ya kafashi. Allah ya kyauta kwanciya. Alh. Shehu Mujaddadi (Alkali) shehu Illa shehu, shima kamar M. Ibrahim Kwatalo, ya gina mutanenda suka gina Mutane a Tarihin siyasar Hadejia. Kuma Har yau Taswirar siyasarsa ce take Tasiri a Hadejia. Allah ya kyauta Kwanciya. Alh. Muhammadu Danjani Hadejia tarihin siyasar Hadejia bazai manta da kai ba! Shi ya fara Dan majalissar Wakilai a Jamhuriya ta biyu. Kuma jigo ne a jam'iyyar NEPU. Wadanda sukayi yaki da mulkin Danniya da kama karya. Shaho birkita kaji na Garba, Bauna wanda ya dosheta babu maduhu sai wani ba tasa ba. Allah ya kyauta kwanciya. Ahmed Garba (M.K.) ko an kika irinka akeso. Har yau Taswirar siyasar Hadejia tana Hannunsa. Duk unguwarda kaje a Hadejia to akwai mutanen da a kafa kuma suka kafu. Ya samawa matasa aikin yi bansan Adadi ba! Amma nasan babu wanda yayi kamarsa kawo yanzu. Zabgai yabin Bauchi da kare dangi Maza sai kui Hankali, Mai tulu kaji tsoron fad da mai sanda ko yana a kwance! Kainuwa dashen Allah yaya zakuyi? Ruwa sai ya kare Kainuwa ta kare ba dai kaga bayanta ba. An karawa kogi Ruwa mai jinga kayi jingarka zai karya Inda yakeso yabi. Masu fura da zuma sun kula da gwangi, idan gwangin zakusha to, Allah ya bamu zuma ku ya baku Gwangin baya tana son gaba. Hadejia A yau.

Thursday, November 15, 2012

TAKAITACCEN TARIHIN SHETTIMAN HADEJIA DA M. BILYAMINU USMAN.

Easily Upload Your Images To Myspace
Free Musichttp://www.MyspaceImageCodes.net">Easily Upload Your Images To Myspace
Free Music Hadejia A yau! Assalamu alaikum! Barkanmu da shigowa sabuwar shekarar Musulunci. A daidai lokacinda muke kokarin Bankwana da shekarar 2012, Allah cikin Ikonsa wannan shekara tazo mana da wani bubban Rashi wanda bazamu manta dashi ba! Wannan rashin kuwa shine na Alh. Bilyaminu Usman da Alh. Hassan Hadejia (shettiman Hadejia). A ranar Asabat 20/october/2012 Allah yayiwa M. Bilyaminu Usman Rasuwa yana da shekaru 83. Kafin rasuwarsa ya rike mukamai da dama musamman a hukumar Ilmi. M. Bilyaminu ya fara koyarwa a Middle school wato Abdulkadir a shekarar 1948, kuma yayi sakataren Ilmi a Hadejia kuma a shekarar 1976 yayi kwamishinan Ilmi a tsohuwar jihar Kano a lokacin Gwamna Sani Bello. Kuma M. Bilyaminu yayi ministan Ilmi a Jamhuriya ta biyu Lokacin shehu shagari. Kuma ya rike Mukamin Chairman primary Education Board a shekarar 1999. Allah ya kyauta kwanciya. Kuma ya bar mana abin koyi a sha'anin zaman rayuwa, wato Gaskiya da rikon Amana. Ko wadanne Irin darasi muka koya daga Rayuwarsa? Hadejia a yau. http://www.facebook.com/Ismailaasabo Haka kuma Ranar laraba 7/November/2012 Allah yayiwa Shettiman Hadejia Rasuwa Alh. Hassan Abbas, sakamakon 'yar gajeriyar jinya, Shettiman Hadejia tarihin Hadejia bazai manta da irin Gudunmawar da ya bayar ba ta hanyar ci Gaban garin Hadejia da Taimakon Addini, masu iya magana suna cewa ba rabuwa da Gwani ba Maida Gwani. Wannan Haka yake Kasar kago bata Maida Kago. Shettiman Hadejia ya rike mukamin Minista a lokacin Jamhuriya ta daya, bayan nan ya rike mukamin Ministan Man fetur a zamanin Ibrahim Babangida, kuma shine shugaban Kaduna polo club, sannan shine Chairman Board of Directors a kamfanin Leadway Assurance! Sannan Board member A Masallacin sultan Bello dake Kaduna. Allah ya kyauta kwanciya! A cikin abubuwanda ya bari wadanda zamuyi koyi dasu akwai kyautatawa al'umma da taimakawa Addinin musulunci da zumunci. Hadejia a yau. Muna rokon Allah ya bamu Albarkar wadannan mutane, Allah ya maida mana makamantansu, Allah ka kara mana Gaskiya da Rikon Amana da taimakon Al'umma. HADEJIA A YAU.