Free Music MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM.
GIDANSU, HAIFUWARSA DA .TASHINSA.
Babban Shehin Malami, Kwararren mai
Tafsiri, Gawurtaccen mai Da’awah,Baban
Salim Ja’afar dan Mahmoodu dan Adamu,
An haifeshi a yankin Daura a jihar Katsina
a Shekara ta 1961. Gidansu Malam
Ja’afar, Gidane da su ke kulawa da Ilimin
Addini da Haddar Alqu’ani, Kakansa ya
kasance yana karantar da Littattafan Fiqhu
da Yaren Larabci, Wasu cikin ‘Ya’yansa
kuma har sun haddace Alqur’ani.
Malamin farko da ya fara dorawa Malam
Ja’afar karatun Alqur’ani, Wani Malami ne
mazaunin gari Daura mai suna Malam
Magaji, yana masa matsayin Babban Yaya
ne, domin sun hada dangantaka da shi a
Kakanninsu, Shine farkon wanda ya fara
koya masa Bakaken Larabci, Wannan
Malami, Mahaddacin Alqur’ani ne tun a
wancan Lokaci.
Baban Salim ya fara koyon karatun
Alqur’ani ne a hannun Mijin Babbar
Yayarsa mai suna Malam Haruna, wanda
shima yana masa matsayin Dan’uwa ne,
Daga hannun wannan Malamin ne aka
maida Malam Ja’afar hannun wani
Malamin kuma Dan’uwansa a kauyen Kuza
mai suna Baba Rabe, Wannan Malamin
shine ya kaurato tare da Baban Salim
zuwa garin Kano a shekarar 1971 ko
1972, Sun sauka a gidan wani
Gawurtaccen Mahaddacin Alqur’ani dan
kasar Nijer ne mai suna Malam Abdullahi
dan Zarmu a unguwar Fage a cikin birnin
Kano. Baba Rabe yayi fatar ganin Malam
Ja’afar ya haddace Alqur'ani tun yana raye,
Amma Allah bai so hakan ya faru a
Idanunsa ba, Wannan Malamin ya rasu a
shekarar 1977 ne, Shi kuma Malam Ja’afar
ya haddace Alqur’ani ne a shekarar 1978
DAGA KARATUN ALLO ZUWA JAMI’A
Baban Salim ya haddace Littafin Allah mai
girma bai wuce da shekara sha Bakwai
ba. Ya fara karatun Alqur’ani gadan-gadan
ne a hannun Malam Abdullahi Mutumin
Nijar, Malami ne da aka san shi da
tsanantawa Almajiransa da matsa musu
kan inganta haddar Alqur’ani, Ina ganin
wannan matsawar ta shafi har Baban
Salim, Domin sakamakonta shine wannan
ingantacciyar haddar Alqur’ani da Allah ya
baiwa Baban Salim, wacce ba kasafai a ke
samun Mahaddata Alqu’ani da irinta ba, In
ban da ‘yan kadan cikin Tsarakunsa.
Malam bai haddace Alqur’ani a hanun
Malam Rabe dan Zarmu ba kamar yadda
Malamin yayi fata, Dalili kuwa shine Malam
Ja’afar da Tsarakunsa a wancan lokaci,
wasan kwallon kafa da zuwa kallonta ya
dauke musu hankali kan tsayuwar daka
kan haddar Alqur’ani, Wannan ya sa,
Malam Rabe ya daukeshi daga hanun
Malam Dan Zarma ya maida shi garin
Hadejiya ya damka shi a hannun wani
Malami dan asalin gari Daura amma
Mazaunin Hadejiya mai suna Malam
Safiyanu,wanda shima Dan’uwa ne ga
Malam Ja’afar domin sun hada dangi da
shi ta Kakanninsu. Malam Rabe yayi masa
haka ne don ya raba shi da kayaniyar Birni
da kuma damuwa da Lamarin kwallon
Kafa, Maiyiwuwa hakan zai sa shi ya maida
hankali kan haddar Alqur’ani, Lalle kuwa
hakan ya faru, domin Baban Salin a can ya
kamala haddar Alqur’ani bayan rasuwar
Malam Rabe.
Bayan fara baiyyanar Kungiyoyin
Musulunci a Nigeria, Musamman ma
Kungiyar Izala, Sai jayayya ta yi yawa
tsakanin Mutane kan wassu Mas’aloli
kamar ; Hukuncin Salatul Fatih, matsayin
Darikun Sufaye, Hukuncin Durkuso a
gaisuwa, Sadakar Fida’u bayan Mutuwa,
Taron Suna da wassu Al’adun kasar Hausa,
Wannan ya tilasta Malam Ja’afar neman
Ilimin Littattafai. Malam Ja’afar ya shigar da
kansa Makarantu Biyu lokaci guda. Ta
farko a wata cibiya ta kasar Masar da ke
garin Kano, Ta Biyu kuma wasu Azuzuwa
ne da aka bude don yaki da Jahilci. Malam
Ja’afar bai shiga Makarantar Firamare ba
saboda a wannan lokaci sun yiwa wannan
matakin karatun girma. Ya yi karatu a
wadannan Makarantu na tsawon shekara
Uku a jere daga 1980 zuwa 1983.