"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, July 4, 2016

AL'ADUN KASAR HADEJIA... Kashi na Daya (1)



WASU DAGA CIKIN AL’ADUNMU KYAWAWA…
Kasar Hadejia mutanen cikinta suna da Al’adunsu kyawawa wadda suka dace da koyarwar Addinin musulunci, wadannan Al’adu saboda kyawunsu yasa mun taso a cikin kyakkyawan tsari da taimakon Junanmu. Shekaru da dama da suka gabata zakaga mutumin Hadejia bubba da yaro yana da Tarbiyyar idan yaga bubban mutum ya gaidashi, kokuma idan yaganshi da kaya a hannu yaje ya karveshi, wannan Al’ada tana da kyau kuma tayi daidai da tsarin Addinin musulunci. Sannan a shekarun baya duk Unguwar da kaje zakaga tsarin zamantakewarsu akwai ban sha’awa, domin wurin zaman manya daban na yara daban sannan idan zaka wuce Bubban mutum yana zaune zaka cire Takalmi sai ka wuce sannan ka saka. Wani abin ban sha’awa shine Lokacin cin Abinci babu yadda zakaga mutum yaci abinci shi kadai ai haduwa ake mutum huxu ko biyar ake ci tare domin neman Albarka. Wannan ya nuna akwai son juna a tsakaninmu, domin wadda Allah bai bashi ikon yin abinci a gidansa ba to bazai wuni da yunwa ba domin idan yazo Dandali zaici tare da ‘yan-uwansa. Haka yara matasa suma kowa yakan dauko abinci daga gidansu a fito a hadu a ci, wannan muke kira da suna Ciyayya.

ZAMANTAKEWA…
Zamantakewa wata kalma ce da take nuni ga yanayin yadda mutum yake rayuwarsa tare da Abokan zamansa wadda Allah ya hadasu, walau a zaman Makwaftaka ko sana’a da sauransu.

TSARIN SHUGABANCHI…
Shugabanci yana nufin rikon on ragamar Al’umma da basu Umarni da kuma yi musu Jagoranci bisa tafarkin da suka aminta dashi, sannan da tsara musu Dokoki da sasanta tsakaninsu. A Kasar Hadejia tsarin shugabanci ya faro ne tun daga cikin gida inda mutum a gidansa shine shugaba mai shirya komai da kuma bada Doka da Oda, sannan sai shugabancin Unguwa wadda ya kasance kowace Unguwa tana da nata shugaban mai sawa da hanawa da bada umarni shine muke kiransa da suna Mai-unguwa. Duk wani umarni yana fitowa ne daga bakin Mai-unguwa kamar hani da kuma sawa. Shi wannan Mai-unguwa duk abinda ya shafi Unguwarsa shine keda iko akai, kamar Umarni, hani, sasanto tsakanin mutane. Kuma duk Bakon da yazo wannan Unguwa akan kaishi gidan Mai-unguwa ne domin shike da Alhakin yaji abinda ke tafe dashi idan mazauni ne shine da hakkin bashi masauki ta haka ake tsaftace Nagari da Mugu a cikin Unguwa. Baya da Mai-unguwa a gari akwai Malami wadda idan wani Bakon malami yazo wurin Wannan malamin za’a kaishi shi zai bashi masauki sannan yaji Dalilin abinda ke tafe dashi. Haka kuma Idan Bakon dan kasuwa ne akan kaishi Gidan Zangoma wadda shine da hakkin saukar Baki musammam masu saye da sayarwa, shi zangoma shine zai tambayeshi irin Hajojin da yake sayarwa kokuma yake saye domin ya sadashi da masu ciniki. Kaga duk wannan yana nuna muna da kyakkyawan tsari na zamantakewa wadda duk mutumin da ya shigo kasar Hadejia ansan Dalilin zuwansa da kuma abinda yazo yi. A duk lokacin da aka samu hakan shi Mai-unguwa shike da Alhakin sanarwa Bulama sannan Bulama ya sanarda Hakiminsa, shi kuma Hakimi zai sanarda Majalissar Sarki.

Wannan tsarin shugabanci shi ake amfani dashi a kasar Hadejia har lokacin zuwan Turawan Mulkin Mallaka. Koda yake Turawa ma da sukazo sai suka lura cewa muna da kyakkyawan tsari na shugabanci, dan haka sai suka nemi Hadin kan Sarakunanmu ya zamanto zasu bada Umarni ne ga Sarakuna sannan Sarakuna su bada Umarni ga Talakawansu. Turawa sunzo sun samemu da Al’adunmu kyawawa sannan muna da tsari na shugabanci kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada mana, wannan dalili yasa Turawa suka samu damar Mulkarmu ba tare da sunsha wahala ba.

Sunday, February 21, 2016

MARIGAYI ALHAJI ADAMU KWANO HADEJIA.....


Daga Mallam Muhammad Rabakaya...

A madadin al'ummar Hadejia da gaba dayan masarautar Hadejia muna addu'a da alhinin Marigayi Alhaji Adamu Kwano (kwano baka karaya) Allah ka gafartawa wannan bawa naka, ka yafe masa kura kurensa da iyayenmu Allah ta'ala kasa aljannah madaukakiya ce makomarsu. Alhaji Adamu Kwano miliyoyin mutane sunyi tarayya da 'ya'yansa wajen gadon dukiyar da Allah ya mallaka masa Allah ka hada mu a Aljannah. zaka\ki so ka\kiji dalili -biyoni..................

Duk wadda ya baka Ilmi ko yayi ma hanyar samun Ilmi ya gama maka alfarma kuma kaci gado daga cikin gadonsa tare da 'ya'yansa. Marigayi Alhaji Adamu Kwano Hadejia Tun kafin a haifeni wannan bawan Allah yana da gida babba mai kallon gidanmu (Gida na a yanzu) Rahama chemist a yanzu ya gina yayi fasalin ajujuwa na Kasa da rufin kwano ya maidashi makarantar  Islamiyya (islamiyyar farko a garin Hadejia), ya tafi kano ya samo Marigayi Malam Aminu Yusuf da Malam Alhaji da Malam Sabo na Madabo da Malam Nasiru Ahli da Malam Rufa'i Kafin Hausa  kuma a matsayin Headmaster da malamai, kuma yabasu mahalli a wancan lokacin mun samu tabbaci daga matar daya daga cikinsu cewa daga gidansa ake dauko musu abinci. Aka saka yara maza da mata aka fara koyarda su darussan addini a tsarin zamani (formal education) mai Allo da Alli.


Daga nan abu ya kara fadada, yasa kudinsa ya cike wani rami mai tarihi wato RAMIN MALAM HUDU inda ya gina ajujuwa na siminti akan ramin da staffroom islamiyya ta koma can ya kara malamai, lokacin duk babu islamiyya sai ita Hudu islamiyya prim. sch. mai tsohon tarihi daga nan gwabnati ta shigo ta taimaka masa da karin Malamai da tsare tsare, Amma gini da gudanarwa nasane.
Bai tsaya nan ba tashinsa zuwa Asibiti inda yake aiki, ya sayi fili anan farin gida ta yanzu ya kara Gina wasu ajujuwan islamiyya ya bude makarantar Islamiyya Garko, duk a lokacin babu Islamiyya sai dai makarantun mu na zaure da na allo, daga nan ya kara fadada niyyarsa da burinsa na habaka ilmin addini a Hadejia ya raba Islamiyya Garko ya Kirkiri Karamar sakandare Islamiyya yasa mata sunan Headmaster na makarantarsa ta farko wato Malam Aminu Yusuf. Ya sake samo wani mutumin Sudan Sheik Ali Fu'ad a matsayin principal inda ya dauka mata malamai itace Aminu Yusuf Junior Islamiyya sec. sch. Hadejia. Wadda daga baya gwabnati ta bashi wani bangare a cikin Buhari primary school Hadejia ta tashi daga Garko ta koma can inda takoma hannun gwamnati kachokam bayan Allah ya masa rasuwa, wannan makaranta yanzu itace babbar sakandaren Islamiyya ta jeka ka dawo ta mata da maza a garin Hadejia.

Daga wancan lokacin zuwa yanzu mutum nawa aka raya? mutum nawa su kuma nawa suka raya da Ilmi? Kuma Bayansa tayi kyau, yana da 'ya'ya da jikoki da sukayi karatun Addini da Boko a fannoni da dama, da wadda yayi digirin farko tun 1977 har zuwa yau agida da kasar waje, sannan kafin yabar aiki yana daya daga cikin wadanda Gen. Olusegun Obasanjo ya baiwa lambar yabo yana shugaban Kasa a shekarar 1977.

Da fatan zamuyi koyi da irinsu a duk bangarorin rayuwa.
posted from Bloggeroid