Da wannan kudiri da yake ransa, Buhari yayi kokarin ya cinye Gogaram (Bedde) da Yaki don ya Nada kaninsa Chiroma Sarkiyo a matsayin Sarkin garin. Kuma dukda yayi haka zuciyarsa daya, wasu daga cikin 'yan-uwansa sai suka yi kokarin su baza masa abinda ya tsara! Dan haka wani daga ciki 'yan-uwan Buhari sai ya fara yada jita-jita a tsakanin fadawan Buhari cewa yana so ne ya kaisu a kashe su don ya cimma wata manufarsa, su kuma fadawa sai suka ga Dangantakarsa da Buhari bazai fadi karya ba sai suka yarda da maganarsa.
Dan haka fadawa sai suka fara shawara a junansu ba tare da Sarki Buhari ko wani ya sani ba, don su yiwa Buhari tawaye a gun yakin, kuma duk suka amince da hakan. Bayan kwanaki sai Buhari ya sanar da fadawa cewa zasuje suci Gogaram da yaki, amma bai san an warware masa shirinsa ba. Aka saka rana Buhari ya jagoranci mayakan Hadejia don su ci Gogaram da yaki,
sarkin Hadejia Buhari ya shiga Gogaram ta kofar Garin yamma amma mayakan Buhari kamar su Sarkin Arewa Tatagana da Sarkin yaki Jaji da sauran fadawa sai suka tsaya suka ki su bi Buhari, ko da ganin Haka sai Buhari ya shiga garin suka fara dauki ba dadi da Mayakan Sarkin Gogaram DAN BABUJE. Har suka sokeshi da Mashi, kuma sai suka fice daga Garin suka koma Bedde ta yanzu. Koda mayakan Hadejia suka ga an raunata Buhari sai suka bisu da yaki, bayan sun dawo sai suka taho da Buhari zuwa Hadejia, inda suka yi Gadon Kara suka Dora shi. Akan hanyarsu ta dawowa Hadejia Buhari ya musu jawabi kuma suka fahimci cewa Munafurci ne akayi tsakaninsu da Buhari. Kuma yace musu lalle In ya mutu su kaishi Hadejia su binne shi, kuma Allah ya dauki ransa a Madaci kusa da Hadejia. Bayan fadawa sun fahimci 'yan-uwan Buhari ne suka munafurceshi, sai suka yanke shawarar cewa dukda Kankantar Dansa Umaru shi zasu Nada A matsayin Sarkin Hadejia. Kuma hakan akayi karkashin jagorancin Tatagana da Jaji. In kazo kayi Gaisuwar Mutuwar Buhari sai ka Juya kayi Mubaya'a a gun Sabon Sarki wato Umaru Dan Buhari. Hadejia A yau.
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!