Ziyara wani Nau'i ne na zumunci wanda mutane suke aiwatar da ita domin sada zumunci ga 'yan'uwa da abokan Arziki. zumunci wata irin halayya ce ta kwarai wacce ke sadar da dangantaka ta nasaba tsakanin ’yan'uwa ko bare. Zumunci ne ke kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da fahimtar juna tsakanin al’umma.
Ta hanyoyin da mutum zai bi ya inganta zumunci shine, kaiwa ziyara ga 'yan'uwansa kamar kaka, uba kokuma kanin mahaifi ko kanin mahaifiya da sauransu. Ta haka ne mutum zai gane irin yadda Alaqarsa take da 'yan uwansa na nesa ko na kusa. Haka kuma kowa yana da iya kimar zumuncin da zai gudanar a tsakaninsa da wani. Kamar yadda Hausawa suka ce zumunta a kafa take, to wannan gaskiya ne,domin
kuwa daya daga cikin manyan ginshikan zumunta shi ne ziyartar juna. Idan ka kula da zumunci shike sa mutum ya niki gari zuwa gidan abokinka ko wani dan'uwanka, ko bare musamman domin ganin yadda yake. Wannan ziyara kawai, ita ke haddasa kauna da mutunci mai dorewa a tsakanin al’umma.
A shekarun baya kamar shekara kamar goma zuwa sama,saboda muhimmancin ranar Juma'a,iyaye sukan je da 'ya'yansu gidajen 'yan'uwansu da Abokan Arziki domin gaisawa wanda hakan yana nuna ana nusar da yara ne da kaiwa ziyara ga 'yan uwansu. Harma yara suke kiran wannan ziyara da yawon Juma'a. Amma saboda shagaltar da zuciya irin ta shaidan tasa wannan kyakkyawan Aiki na ziyara ya fara ja baya ga yara harma da manyan a wannan zamani,domin shi bubba yana tunanin ai in yaje zai bada kudi, sannan yaro yana tunanin kar yaje ba'a bashi kudi ba.
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!