MAIRAKUMI GARIN SAMBO!
Garin Mairakumi yana daya daga cikin garuruwan Tarihi a kasar Hadejia, wannan gari yana karkashin mulkin Karamar hukumar mulki ta Mallammadori a yanzu. Kuma gari ne bubba wanda yake karkashin mulkin Dagachi (Bulama).
- Garin Mairakumi ya kafu ne a zamanin Sarkin fulanin Hadejia Umaru, a lokacin da Sarkin Hadejia Sambo ya karbo Tutar Jaddada Musulunci bai zauna a Garin Hadejia ba saboda yana gurbin shehu don Neman Ilmi. Bayan Sambo yayi niyyar dawowa Kasar Hadejia sai ya nemi alfarma ga Shehu don yana so ya zauna a Wajen Hadejia, domin ya samu damar kiwon Dabbobinsa da kuma bayar da Ilmi ga Almajiransa, sai Shehu yace masa to idan yaje garin Hadejia a Arewa da Hadejia in ya ketare jigawa guda Hudu to anan akwai wani Daji mai ciyawa dabbobi zasu samu abinci a dajin. Sambo yayi Bankwana da Shehu ya taho kasar Hadejia.
Bayan Sambo yazo Hadejia yayi Mubaya'a ga Sarkin fulani Umaru sai ya dawo Arewa da Hadejia tare da Almajiransa, yazo gurin da Shehu ya fada masa, Sambo da Almajiransa suka fara gyara daji sukayi Tsangayarsu kuma suka Tona Rijiya suka zauna. Sannan suka gyara gurin da za su rinka Noman Abinci. A lokacin da sukazo Dajin sun tarar da Maharba masu farautar Namun daji sai suka zauna a wannan daji har ya zama gari. A wannan Dajin kuma akwai wani Rakumin dawa wanda yake fitowa yake yin kiwo tare da Dabbobin Sambo, saboda baya cutar da dabbobin sai Sambo ya sanar da Mafarauta cewa kar kowa ya kashe shi. Amma a lokacin akwa Zakuna da suke Kashewa Sarki Sambo dabbobi dan haka ya sanar da mafarautan cewa idan suka kashe zakunan zai basu Jar Saniya. Hakan kuma akayi gari ya zama alkarya saboda Almajirai suna zuwa neman Ilmi, kuma Maharba suma suka gina bukkokinsu suke farautar namun daji. Dan haka idan mutane zasuje garin sukanyi Inkiya da sunan Rakumi... Sukan ce mun tafi Gari Mai Rakumi, saboda takaita kalma sai ake kiran garin Mairakumi.
Da yake duk gurin da aka samu Jama 'a ta zauna dole a samu shugabanci, sai Sarki Sambo ya Nada daya daga cikin Maharban nan ya zama shine Shugaban garin, kuma har yanzu Danginsa ne suke mulkin garin. Da duk Dagacin garin ana kiransa ne da Sarkin Baka, sai dai daga kan wannan Dagacin ne ake cewa Bulaman Mairakumi.
A wannan garin ne Sarkin Hadejia Sambo ya zauna bayan yayi Sarautar Hadejia ma a lokacin da yayi Murabus garin ya koma ya zauna, kuma a garin Allah ya dauki rayuwarsa. Har yanzu Kabarinsa yana nan a gidan gonarsa a Unguwar Tsangayar Malam Sambo.
Allah yaji kansa da Rahma.HADEJIA A YAU!
Masha Allah
ReplyDelete