"" /> HADEJIA A YAU!: TARIHIN GARIN BARNO (MAIDUGURI)...

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, October 30, 2016

TARIHIN GARIN BARNO (MAIDUGURI)...

HADEJIA A YAU!
        
Mutanen  Barno suna da yawa qwarai, ita kuwa Barno tana kusa da Tafkin Chadi ne, wannan Tafki yana da ban mamaki qwarai don baya da zurfi har mutum yana iya tuqa kwale-kwale ya ratsa Tafkin na Chadi saboda Ruwan Kogi kaxan yake shiga Tafkin kuma iska tana hura shi daga gefe zuwa gefe. Da ka matso kusa da Tafkin sai kayi ta ganin abin mamaki, in kana gabar tafkin bazakaga Ruwa ba sai kayi ta ganin Ciyayi har fiye da Mil biyu gabanka. Mazauna wurin Larabawa ne da suka Dogara da tafkin don rufawa kansu Asiri. In ka duba kewaye da tafkin sai kaga kasa ce shimfidaddiya, ta ko ina kuwa shimfidaddiyar kasar nan ta kai Mil dari da wani abin, amma in ka matsi tafkin sai kaga gangara kadan zuwa tafkin. 

Wannan shimfidaddiyar kasa ta zama kamar hanya tsakanin  kasashen Afrika ta yamma da tsakiyar Afrika da Dafur da kuma kwarin kogin Nil. Ta nan ne matafiya na Afrika na shekaru suke wucewa. Hanyar nan tana da wuyar bi amma bata da wuya kamar hanyar da take Arewacinta, wadda sai an ratsa Hamada ko wadda sai an bi tsakanin Duwatsu  daga kudu. Wurin nan kana ma kamar fadama lokacin Ruwa, amma kuma in Ruwan ya janye ana iya wucewa. Iyakar saninmu wadansu mutane ne an ace musu ‘SO’ suka fara ama a wurin nan, kuma ana cewa mutanen suna da Girman jiki da tsawo kamar wadanda suka fara ama a Kano. Amma cikin Tarihi abinda aka iya samu nasu shine manya manyan Tukwane, wadda akace matansu suna dibar Ruwa dasu. Tukwanen suna da nauyi har sai mutane da dama sun hadu zasu iya daga su daga wurin da suke. Kowace Tukunya kuma tayi misalign kafa biyar a tsaye, wadannan mutane a Gabar Tafkin Chadi suka zauna. Babu dai wadda yasan daga inda suka fito, kuma da wuya a kara gano wani abu game dasu, sai dai in an kara hako irin abinda suka bari…


WADANDA SUKA FARA MULKI A WURIN….
Wadanda suka fara mulki a kewayen Tafkin Chadi, wadansu mutane ne ana ce dasu SEF. Asalinsu kuwa Berber ne, watakila sunzo ne da kansu ko kuma sun hade ne da mutanen da sukazo daga kudancin Bahar Rum ne. sune suka kafa Mulkin Kanem, suka zauna sukayi mulki a wurin yau misalin Shekara 1,225 kenan da suka wuce, sai wasu Kabilu suka kara zuwa suka zauna har suka kara girman wurin. Cikin 1250, shekara ta 697 kenan Dunama  Dabalemi, Mai na Kanem ya mulki makekiyar kasa wadda tun daga Kogin Nil taa kai Kogin Kwara, har wani yankin Hamada Kasar nan ta mamaye. Daga Fezza (A Kudancin Tarabulus) har Duwatsun nan na Mandara na kudu da Chadi duk kasarsa ce. Kasarsa tayi iyaka da Songhai wajen kogin Kwara, har dai kasar Hausa duk cikin Kasarsa take a da. Masu mulkin wannan kasa suna saduwa da masu mulkin kasar Masar da Tarabulus harma wakilan waccan kasar suna zuwa wannan kasar don wani muhimmin Al’amari. A lokacin nan ana tsammanin Kanuri wadda Hausawa ke kiransu Barebari, sun gauraya da wasu kabilu ne daban. Ana tsammani su Kanuri tare sukazo da kakannin kakannin Hausawa.

Bayanda masu mulkin Kanem watau Sef, suka kaura sai suka koma kano, bayan shekara saba’in (70) sai Mai Ali Ghaji ya sake kafa wani mulkin amma a yammacin Chadi ya kafa. Bubban Garinsa shine Birnin Ngazargamu, yanzu garin ya zama kango amma da ganin kangon Garin kasan bubban gari ne. misalin shekara dari uku (300) da suka wuce anyi sarakuna masu hikima a Barno, kamar yadda akayi a sauran kasashe. Cikin Sarakunan Barno akwai wani wai shi Idris Alooma, yana da wani Malami wadda ya rubuta labarai iri iri na lokacin nan, wadda da taimakonsu muna iya gane abinda ya faru a lokacin nan. Amma a lokacin nan Barno ba kamar Barnon da muka sani a yanzu take ba, lokacin nan daga Nguru sai ka fada kasar Hausa. Nguru  tana da muhimmanci kwarai a Daular Kanem, saboda haka sai aka damkata ga Galadiman Barno, daya daga cikin manyan Hakiman Barno…..

       FULANI SUN YAKI BARNO……….
Fulani sun baiwa Barno Kashi har fiye da yadda suka ba Kasashen Hausa, Fulani sun ci Bubban Birnin Kanuri. Koda yake Kanuri sun kori Fulani amma daga baya sun dawo, to da suka sake dawowa sai Mai na Barno ya nemi Taimako daga Kanem. Muhammad Al-Amin El-kanemi wadda aka fi sani da Shaihu Laminu, shine shugaban wadanda sukazo taimakon nan. Shi Shaihu Laminu Haziki ne kwarai, kuma yana da Ilmi mai yawa. Ya taba zuwa Hajji kuma ya taba zama a Masar, lokacin da zaizo yayi ta Gargadi ga mutanen Kanem don suzo su taimaki mutanen Barno. Da sukazo kuwa sai suka samu sa’a suka kori Fulani, amma Fulani basu dade ba sai suka sake cin Birnin Ngazargamu a cikin shekarar 1810. Har yanzu Shaihu Laminu ya sake zuwa Taimakon Kanuri, a wannan lokacin sai ya gayyaci Larabawa suka taimakeshi ya sake korar Fulani. To sai Shaihu Laminu ya zauna a Kukawa, koda yake Sarakunan Barno suke kula da Al’amarin kasar, dukda haka Shaihu Laminu shine Uban kasar Barno.
Umaru dan Shaihu Laminu shine ya gwada sosai don yana so yazama Mai na kasar Barno, amma Mai na karshe wani yaro dan shekara Goma sha bakwai (17), yayi kokarin hana Umaru ya zama Mai. To sai yaki ya tashi, Yakin nan fa shine karshen Sarakunan nan da akayi a Barno daya na bin daya har misalign shekara dubu (1000).

  SHIGOWAR RABEH AZ-ZUBAYR……
Cikin shekarar 1893 sai Rabeh yazo daga Sudan da shiri na gaske, ya afkawa Barno nan da nan yayi Karin kumallo da ita. Allahu Akbar! Cikin yakin nan ne aka kashe Kakan Shaihun Barno na yanzu, wajen shekara shida (6), Rabeh da mutanensa sai abinda sukaga dama a Barno. Wani yaki da akayi a kusa da Farlomi, nan faransawa suka kori Rabeh har suka kashe Dansa Foldlellah. Bayan lokaci kadan sai Ingilishi suka ci kasar da yaki kuma suka mayar da zaman Lafiya da Salama. 

   RIKICIN BOKO HARAM......... 

1 comment:

  1. Waya gaya Maka Fulani sun Bawa Borno Kashi fiye DA kasar hausawa kasake bincike a tarihinka mlm

    ReplyDelete

RUBUTA RA'AYINKA!