Kasar Hadejiya tana da kabilu daban daban, amma duk da haka wannan masarauta a cure take a waje daya. Addinin Musulunci shi ne ya dada hada su da kuma harshen Hausa wadda suke magana da shi a matsayin harshen kasa. Babu wata tababa cewa Addinin Musulunci shine Addinin da mafi yawan jama'a suke bi a wannan masarautar ta Hadejiya. Ka'idoji da dokoki da hukunce-hukuncen Musulunci su ne suke tafiyar da rayuwa da ayyukan mutanen wannan kasa. Addinin Musulunci ya hada kan jama'a kuma ya samar da hanya madaidaiciya ta zaman al-umma. Ta hakane Musulmi masu rinjaye da wadanda ba Musulmi ba marasa rinjaye mazauna kasar Hadejiya kafin mulkin mallaka suna ganin sarkin Hadejiya nada mutukar kima kuma shugaba ne babba duk da yake suna da hakimai da dagatai wadda suke jagorancinsu, Mutanen Hadejiya sukan hadu a kowace shekara su gudanar da bukukuwan Sallah karama da Sallah babba a Hadejiya.
Ta haka al'ummar Hadejiya take cudanya da juna cikin walwala, farin cikin, nishadi, jindadi da annashuwa da sakin fuska. Kuma bisa dukkan alamu, kabilun da suke zaune a Hadejiya sun shiga juna, za'a taras bisa asali, Bahaushe, Bababbare ne, ko Bamange, ko babade, ko kuma bafulatani. Haka dai kabilun kasar Hadejiya suka sarki juna.
Jama'ar da ba Musulmi ba suna karkashin kariya ta wannan masarauta, amma su kuma suna bayar da jizya. Al'adun Hausawa/Fulani Hadejiya suna da babban tasiri na mutanen Gabas wato al'adun Barebari. Akwai misali da yawa da za a iya bayarwa a kan haka, kauki misalin sunayen wasu mukaman sarautu kamar Zangoma da Bulama da Kacallah da Maina (dan Sarki) duka daga wajen Barebari a ka samo su.
Hatta ma bikin Sallar maulidi ana gudanar da shi ne dai-dai yadda Barebari suke yi. Ashe ke nan al'adun Barebari sun yi tasiri. (Sulaiman Ginsau )
Kari a kan wadanan kyawawan huldodi na mutanen Hadejiya a tsakanin junansu, tsarin da masarautar ta bi wajen tafiyar da al'amuranta na mulki ya dada kara wannan dankon zuminci. Tun daga farkon kafuwar daular, Sarkin Hadejiya Malam Sambo ya dora kowace kabila daga cikin kabilun kasar a kan wani mukami na sarauta. Wannan tsari da aka ci gaba da aiwatar da shi, ya sanya jama'ar kasar sun zauna a dunkule tamkar tsintsiya domin kowace kabila ta san tana da wakilci a majalissar wannan masarauta.
Ta fuskar tattalin arzikin kasa kuwa, Hadejiya tana da yalwataccen arziki tare da sana'o'i da masana'antu iri-iri, duk da yake harkokin noma sunfi daukar kaso mai yawa. Magidanci shi ne tushen arziki a tsarin zaman jama'a tare da iyalansa a matysayin masu taimakawa. Talakawa sun tsayu sosai wajen yin noma na lokacin damina da noman fadamu a lokacin rani, sannan kuma kamun kifi da kiwo sun zama ruwan dare a tsakanin mazauna kasar Hadejiya. Amfanin gonar da aka fi nomawa sun hada da:-
1. Gero
2. Dawa
3. Shinkafa
4. Wake
5. Masara
6. Gyada
7. Auduga
8. Alkama
9. Ridi da Kankana
10. Rake da sauran kayan lambu kamarsu Timatir da Tatttasai da Taruhu da Rake da sauran kayan lanbu ana noma su ne ta hanyar noman fadama a lokacin rani. Kasar Hadejiya, kamar sauran kasashen wannan nahiya, tana da kyakkyawar kasar noma Gero da Kiwon Dabbobi. Har wa yau kuma wannan yanayin wuri ne mai albarka ya ba da damar aiwatar da wasu sana'o'I kamar su Rini da Saka da Kira da Ginin Tukwane da Jima da Dukanci da Gini da sauransu.
A bangaren saka kuwa kauyen Bangelu wanda yake tsakanin Auyo da Hadejiya ya shahara sosai wajen saka da dinka Rigar Bullamai tare da sauran Rigunan Saki Fari masu inganci. Haka kuma kauyen Hadejia ya yayi suna a sana'ar Rini. Mutanen Hadejiya da suke zaune a daura da kogin Hadejiya sunyi fice a sana'ar Su ta kamun kifi. Haka kuma dajin Hadejiya cike yake da kudan zuma inda ake samun zuma mai tarin yawa. Diban zuma ya zama wata sana'a mai riba ga jama'ar kasar Hadejiya musamman yadda take tallafawa wajen warware matsalolin rayuwar yau da kullum.
Bugu da kari mutanen Hadejiya kamar sauran wurare, sukan sayar da amfanin gona wanda ya yi rara, ta haka suka shiga hada-hadar kasuwancin amfanin gona daga cikin hanyoyin da suka kara habaka Tattalin Arzikin Kasar Hadejiya kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Ta wannan hanya masarautar Hadejiya ta zama wata cibiya kuma muhimmiyar mahada ta cinikin kayan amfanin yau da kullum a gabacin kasar Hausa a karni na sha tara (K19). Masarautar ta yi fice wajen fitar da kayayyakin abinci kamar Alkama da Kifi zuwa Kano da wasu wurare, ita kuma sai ta sayo Goro da makamancin abubuwan da masarautar take da bukata. Kamar yadda aka fada a baya, mutanen Hadejiya na kasuwancin Rigunan Saki ko Rigunan Fari da Zuma da Kiraga wato (Fatu) da Shanu, su kuma su sayo Gishiri da Dawakai da Kanwa. Ana kuma jin cewa Hadejiya ta zama wata hanya ta fatauci na fataken da suke ratso Sahara zuwa Kano ta yamma da kuma Barebari da Larabawan Fezzan da Azbinawa da Buzaye daga gabas da kuma yamma. Wadannan fataken sukan hadu a kasuwar Hadejiya su gudanar da harkokin cinikayyarsu na kayayyaki kamar Rigunan kano da kanwa da Shanu da Bayi da kayan Yaji (Sulaiman Ginsau).
A wannan lokacin da ake Magana, a Hadejiya akwai manyan kasuwanni guda biyu (2) daya kasuwar an yi ta a wajen ganuwa, an kakkafa rumfunan da kuma masaukai na baki wadanda aka yi don samar da wuraran zama da jin dadin fatake da sauran yan kasuwa. A cikin ganuwa ta birnin Hadejiya akwai wata kasuwa wadda take kula da bukatun mazauna birnin Hadejiya da makwabtanta. Wannan ya nuna cewa bayan kasancewar Hadejiya cibiyar mulkin da ayyukan jin dadi jama'a, haka kuma tana matsayin ingantacciyar cibiya ta kasuwanci. Wannan kasuwa tana karkashin kulawar Zangoma wato Sarkin kasuwa. Zangoma shi ne yake karbar dukkan haraji na wannan kasuwa tare da masu taimka masa.
A dunkule, wannan yayi bayanin Hadejiya a matsayin masarauta ta mulkin jihadi da kuma fito da tsarin zaman jama'arta da tattalin arzikinta kafin mulkin mallaka na turawan ingilashi a kan daular Usmaniyya ta Sakkwato.
An kuma nuna cewa a fanning Siya sa, Hadejiya gari ne na 'yan Boko da 'yan siya sa masu yawan gaske kuma Hadejiya garine na kasuwanci wadda hakan ya sa mutane suna zuwa siyan kayayyaki daga gurare daban-daban, sannan masarautace mai karfi a tsakanin masarautun da suke gabacin kasar Hausa, musamman yadda take tsoma baki a harkokin cikin gida na makwabtan ta.
Haka kuma nayi wai-waye ta fuskar tsaro ya bayyana cewa Hadejiya kasace jaruma kuma karshen karni na sha tara (K19) sai ta zama kasa mai kyakkawar huldar dangantaka da zama na lumana da abokan taka da sauran masarautu. (Sulaiman Ginsau)
Muhadu a kashi na biyu 2
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!