HADEJIA A YAU!
An haifi Ɗan Hausa a cikin shekarar 1876, bai fara aiki a ko ina ba sai a Nigeria a cikin shekarar 1903. ya fara aiki a matsayin mataimakin Razdan, kuma sunansa shine Sir. Hanns Vischer, ya fara zuwa Ƙasar nan akan aikin Mishan ne. ya fara zuwa ƙasar nan ne tare da Dr. W.R. Miller da Sarkin Hausa Reb. G.P. Bargery, farkon samun aikinsa an ajiyeshi a waɗansu wurare harma ya taɓa zama a Barno. yana can Barno ne yayi tafiya da Ayarin Raƙuma daga Tarabulus zuwa Barno ta hanyar Marzuk. har ya rubuta littafi akan tafiyarsa, wadda ya sakawa suna ƙetarar Sahara. yayi wannan tafiya tare da wani yaronsa da ake ƙira Sa'id. shi Sa'id ya daɗe yana Masinja sai a shekarar 1945 ya rasu, duk waɗanda sukayi makaranta a Nasarawa ta kano sun sanshi.
Cikin shekarar 1908, Ɗan Hausa ya zama gwamnan makaranta har yaje ƙasar Sudan don ya koyo yadda za'a shirya Al'amarin Ilmi anan. A shekarar 1910 ya kafa makarantar Turawa a Nasarawa dake Kano, yara da samarin da aka buɗe makarantar dasu bayan shekara uku kuma sai su fita suje suyi koyarwa a makarantu na ƙasashensu, kamar su Katsina, Sokoto, Barno, Bidda da Zariya. Wannan makaranta ta Ɗan Hausa tana nan a kusa da ofishin Razdan na Kano kuma har yanzu wannan gida yana nan. Cikin shekarar 1915 ya shiga aikin soja har ya zama laftanal aka gama shi da masu kula da shirin labaran yaƙi, ana nan har ya zama kyaftin har dai ya kai matsayin Manjo. Cikin watan Yuli 1917 Ɗan Hausa ya koma Ingila sakamakon Jinya da ta dameshi, amma dukda haka bayan ya koma Ingila yaci gaba da Taimakon ƙasar nan ta hanyar Ilmi.
Ɗan Hausa yakan riƙa bada labarin zamansa a ƙasar nan har yakan riƙa bada labarin wani Masinjan Razdan na ƙasar nan Mr. George Tomlinson, lokacin da Masinjan zai je Hajji sai da ya isa Bahar Muhid aka ce ya makara, da zai koma gida ya kewayo ya biyo ta Bahar Rum. har ya isa Birnin Southampton inda Ɗan Hausa yake aiki. anan ya zauna a tashar Jirgin Ruwa tare da sauran fasinja, amma da 'yan Gadin sukaga irin siffarsa sai suka ƙi yarda dashi suka kai shi wurin Ɗan Hausa. Shi da ganin mutumin ya san Bahaushe ne amma Ɗan Hausa bai nuna masa ya iya Hausa ba, sai ya faɗa shi da tambaya da turanci, Bahaushen nan tsoro ya kama shi, amma da yaji Ɗan Hausa ya masa magana da Hausa sai yayi ta kuka don murna. ya sa aka bashi masauƙi mai kyau kuma ya gamashi da Takarda cewa mutumin nan abokin aikinsa ne na Africa. kaga bai taɓa sanin mutumin ba amma saboda yana ƙaunar mutanen Africa yayi masa wannan Darajar. Cikin 1917 aka kai Ɗan Hausa ofis ɗin wakilin Ingila dake Spain ya zauna acan har aka gama yaƙi.
A shekarar 1923 ya zama sakataren wata jam'iyya mai lura da yadda za'a shirya zancen ilmi a ƙasashen da suke ƙarƙashin mulkin Ingila, kafin ya huta a wannan aiki ne ya samu bubbar lambar Girma ya zama ''Knight'' yana cikin waɗanda suka kafa jam'iyya mai lura da zancen harsuna na Africa watau ''Institute of African Languages and cultures''
Mallam Bello Kagara yace....
Haƙiƙa ya cancanci ace dashi Ɗan Hausa, don dabarar sa da yayi nufin bude makarantu anan Nijeriya ta Arewa sai yaje Sakkwato a hankali ya fara da can ya ɗauko ta daga tushe. Bayan haka kuma yaga babu inda ya kamata ya kafa makarantar sai tsakiyar jama'a watau Birnin Kano, sai yaje Nasarawa gabas da kano ya bude ta". Da fari bai ɗauki kowa ba sai 'ya'yan sarakuna, da Hakimai, da Alkalai, da shaihunnan maluma.
Akwai manyan Sarakuna daga cikin Almajiran sa, kamar sarkin Gwandu da Sarkin Zazzau, da Lamidon Adamawa Mustapha da Sarkin Yawuri, Hakimai kuwa Allah yayi yawa dasu! Sunan Ɗan Hausa har abada bashi ɓata anan ƙasar musamman a ƙasar Kano.
Malam Bello Kagara yace... "babu abinda yake ban mamaki kamar zamanmu dashi a Nasarawa, ga Almajiran sa cikin Aji da Amawali da Alkyabbu, dasu da malamai sun zama bubba da hula yaro da hula, ga Dawakai da zagage a ƙofar makaranta duk na Almajiran sa ne suna jira a tashi su hau. Amma duk da haka Ɗan Hausa ya ƙyale mu, kowannen mu in safiya tayi zamuyi shara tun daga ciki har waje, ga Barorinmu na kallo basu da ikon su karbe mu. Mu ratsa Kano har Dala mu ɗauko fid da sartse a kai, alhali kuwa ga Dawaki da zagage da Alkyabbu sun riƙe a ƙofar makaranta".
A cikin 1913, yaga malamai sun samu sai ya fara bude makarantu a manyan Alƙaryu don a watsa Ilmi a ko ina, dubi yanzu yadda abu ya tabbata. Amma kam kada ka tona wahalar da Turawan farko suka sha kafin Ilmin Boko ya tabbata.....
MADOGARA....
Gaskiya tafi kobo ta 175.
Sir. Hanns Wikipedia
Eap.bl.uk.
Allah ya kara basira. Dan Hausa yayi kokari matuka.
ReplyDeleteGaskiya ne
ReplyDelete