HADEJIA A YAU!
KASUWAR KWADI DAKE HADEJIA ( Hadejia Market of Toads)
Babbar kasuwa da Masayen Kwadi ke zuwa daga Jahohin Benue da Kogi da Nasarawa da kuma wasu daga cikin Jahohin Kudu Maso Gabashin Nageriya domin sayen Kwadi.
Ni da kaina ajiya Lahadi na ziyarci Kasuwar kuma na zanta da Madam Inya-Ozi-Ohinoyi daya daga cikin dinbin Masu ziyartar Kasuwar duk sati tana sayen Kwadi.
Da farko dai Mun gaisa kuma na tambayeta ko daga ina take zuwa sayen wannan Kwadi? Sai ta ce min tana zuwa tun daga garin Igumale da ke jahar Benue, sai kuma na Tambayeta ko tun yaushe suke tasowa daga garinsu zuwa Nan? Madam Inya sai tace tun ranar Juma'a da yammaci suke tasowa suwayi gari har ranar Asabat kuma Nan da Maraice sun iso Hadejia kafin washegarin Lahadi ranar da Kasuwar ke ci.
Bayan haka na tambaye ta ko nawa take sayen duk tsinke daya na Kwadi (Stick of Frogs) sai tace kananan tsinke suna sayensa dari 700 zuwa 800 Manya kuma suna sayensa dubu 2800 zuwa 3200, na kuma ta cigaba da tambayarta cewar idan ta sayi kwadin ina take kaiwa sai ta ce min daga Nan suna loda sune a babbar Mota da take Kai musu Kasuwar Garin Gboko da ke Benue daga Nan kuma akwai Wadanda suke zuwa suke saya Musamman masu gidajen sayar da abinci (Restaurant) da Otel da kuma daidaikun Mutane.
Kasuwar ta Kwadi da ke garin na
HADEJIA ta fara kafuwa ne kusan shekaru 10 da suka Gabata, Amma a wadancan lokutan Kasuwar bata girma ba sakamakon kyama da kuma rashin Takamemen wajen sana'ar.
A Dan shekarun baya bayan Nan dai Kasuwar ta kafu a dan wani waje na wucin gadi da ake Kira Kasuwar "Jam Bulo" bayan da ruwan sama da ke taruwa akasuwar lokacin Damina, sai Masu sana'ar kamin kwadin sukayi kaura zuwa wani wuri na wucin gadi a gefen filin Ma'aikatar Raya Kogin Hadejia jama'are (Hadejia Kama'are river Basin), inda suke har yanzu.
Kungiyar Masu sana'ar kwadin da ke garin na HADEJIA bukaci da Hukumomin jahar da su nema musu wuri na dindindin (Permanent site) domin cigaba da sana'arsu ganin cewar Gwamnatin karamar Hukumar.
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!