"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, June 26, 2012

RABE DA MUTANEN BORNO


HADEJIA A YAU!
Baramusa wani kauye ne a karamar hukumar Birniwa! Naje ziyara kauyen kuma ganin cewa duk barebari ne a garin, sai na samu damar in tambayi tarihin Rabe dan Fataralle. Na samu wani dattijo mai shekara 76, sai na tambayeshi tarihin Rabe. Kafin ya bani amsa saida ya tsinewa Rabe.
Yace wani mutumin sudan ne wanda ya Addabi bare bari tun daga kukawa Har zuwa Bedde. Sannan yace Rabe ne dalilin zuwansu nan kuma yace duk Babarbare ko bamangenda naganshi a Kasar Hadejia ko wani Guri, to lokacin Rabe ne suka Gudo nan. Yace kamar Kacallari,Kaigamari,kuka Ingiwa,Birniwa.kirikasamma,Jibori, da sauransu duk Gudun Rabe sukayi. A lokacinda Rabe yaje kukawa ya kashe duk mutanen Garin wasu da suka samu labari sai sukayi gudun hijira kasar Hadejia. Wasu kuma suka shigo cikin Hadejia kamar Gagulmari,Kakaburi,zonagalari,kilabakori da sauransu. Yace da can suna da zanen barebari amma yanzu sun canza sai suke zanen a kan fuskarsu wato uku uku. Sauran Labarin sai a Gaba.

Monday, June 25, 2012

GARKO DA SANA'AR SU. TUN KAFIN ZUWAN BATURE


HADEJIA A YAU! GARKKO Unguwar Garko Tana daya daga cikin unguwannin da suke Garin Hadejia, kuma Unguwa ce mai dimbin tarihi idan mukayi La'akari da Dadewarta. Garko tana daya daga cikin garuruwanda sarakunan Habe suka mulka a Hadejia amma A lokacin Gari ne mai zaman kansa kafin ya hade da Hadejia ya zama Unguwa. Kuma suna da sana'ar su wanda suka gada Iyaye da kakanni. Hakan ta bunkasa tattalin Arzikinsu tun a wancan lokacin zuwa yanzu. Sana'ar su Itace Amfani da kasa ko yumbu domin yin Randa,Gajirami,Tukunya,Tuli,Kula,Kasko,kafara da dai sauransu. Kuma wadannan kayan sune kayan da ake amfani dasu a kasar Hausa kafin zuwan Turawa. Domin Amfanin Gida wato Girki ko Aje ruwa ko makamantansu. Na samu wani Dattijo yana gina Randa a kofar gidansa Na tambayeshi ko A ina suke samun yumbun da suke gina randa? Yace duk a Hadejia suke samu akwai Mailolo ta Gabas da Hadejia anan suke samo yumbun da suke gina duk abinda nagani anan. Na tambayeshi ko shekara nawa yana yin wannan sana'a? Sai yace ya kai shekara Hamsin da biyu yana yi, kuma suna yi ne da Mahaifinsa da kannensa har zuwa yanzu ya zamanto shine bubba. Na tambayeshi menene dalilin da in an gina ake zuwa a gasa ta a wuta? Zan kawo muku karashen firar mu.