HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Monday, June 25, 2012
GARKO DA SANA'AR SU. TUN KAFIN ZUWAN BATURE
HADEJIA A YAU! GARKKO Unguwar Garko Tana daya daga cikin unguwannin da suke Garin Hadejia, kuma Unguwa ce mai dimbin tarihi idan mukayi La'akari da Dadewarta. Garko tana daya daga cikin garuruwanda sarakunan Habe suka mulka a Hadejia amma A lokacin Gari ne mai zaman kansa kafin ya hade da Hadejia ya zama Unguwa. Kuma suna da sana'ar su wanda suka gada Iyaye da kakanni. Hakan ta bunkasa tattalin Arzikinsu tun a wancan lokacin zuwa yanzu. Sana'ar su Itace Amfani da kasa ko yumbu domin yin Randa,Gajirami,Tukunya,Tuli,Kula,Kasko,kafara da dai sauransu. Kuma wadannan kayan sune kayan da ake amfani dasu a kasar Hausa kafin zuwan Turawa. Domin Amfanin Gida wato Girki ko Aje ruwa ko makamantansu. Na samu wani Dattijo yana gina Randa a kofar gidansa Na tambayeshi ko A ina suke samun yumbun da suke gina randa? Yace duk a Hadejia suke samu akwai Mailolo ta Gabas da Hadejia anan suke samo yumbun da suke gina duk abinda nagani anan. Na tambayeshi ko shekara nawa yana yin wannan sana'a? Sai yace ya kai shekara Hamsin da biyu yana yi, kuma suna yi ne da Mahaifinsa da kannensa har zuwa yanzu ya zamanto shine bubba. Na tambayeshi menene dalilin da in an gina ake zuwa a gasa ta a wuta? Zan kawo muku karashen firar mu.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!