HADEJIA A YAU!
A kashi na farko kunji yanda Buhari suka kare da Wazirin sokoto da Mutanen Katagum: da kuma komawar sarki Buhari shabawa wato iyakar Hadejia da Gumel da kuma Damagaram.
YAKIN TAKOKO:- Bayan an Nada Ahmadu a matsayin Sarkin Hadejia, sauran Magoya bayan Buhari sai suma suka bar Hadejia suka koma Shafowa inda Buhari yake suka zauna tare. Sarkin Hadejia Buhari anan ya zauna tsakanin Takoko da Shafowa a Arewacin Hadejia da mutanensa kuma yake tafiyar da wannan yankin. Kuma iyakar Hadejia ce da Damagaram da Machina ta Arewa maso Gabas wato yankin Niger da kuma Borno. Kuma Buhari ya bada Gudun mawa sosai a wannan Yankin wajen Maidasu Musulmi. Inda yayi ta jihadinsa a yankin, kuma a wannan zama da yayi a Shafowa Buhari ya samu kyakkyawar dangantaka da Sarkin Machina da kuma Shehun Borno Umar wanda ya mulki Borno a wannan shekara (1835-1880) wannan dangantaka ta kara baiwa Buhari karfin gwiwa.
A shekarar 1851, Sarkin Musulmi Alu Bubba ya yanke shawarar daukan matakin Karshe akan Buhari, saboda yana tunanin Shehun Borno zaiyi amfani da Buhari ya rusa Daular Sokoto saboda ya zame musu Barazana a Arewa Maso Gabas. A wannan lokacin kuma DanGaladiman Sokoto ya hada Mayaka daga Hadejia,Kano,Katagum,Misau da Jama'are zuwa shafowa.
A wannan lokacin kuma Buhari ya fita kudu da shafowa shi da Sarkin Machina yana garin Takoko shida Jarumansa. A lokacinda Dangaladiman sokoto suka fito su yaki Buhari sai ya zabi Sarkin Jama'are Samboli ya jagoranci yakin, saboda shi ya fisu sanin Yankin. A ranar da zasu yaki buhari kuma a ranar Buhari ya shirya mamaye Garuruwanda suke kudu da Hadejia, sai aka hadu a Garin Takoko. Yayin da aka hadu aka gwabza fada Buhari yaci Galaba a kansu duk suka gudu, Sarkin Hadejia Ahmadu yayi kokarin ya Gudu Kasar Kano amma sai Barde Risku ya bishi ya Kashe shi.
Bayan Yakin Takoko yazo karshe kuma an kashe Sarkin Hadejia Ahmadu Amma ba'a son ran Buhari ba kuma aka masa Sallah aka kaishi Hadejia aka binne shi, sannan sai Buhari ya koma Hadejia yaci gaba da Mulki. Sakamakon wannan yakin, dangantaka ta sake baci tsakanin Hadejia da Sokoto, kuma Sarkin Musulmi yaki yarda da ya nada Buhari Sarkin Hadejia. Sai ya nada Tukur Na yayari, kanin Sarki Ahmadu kuma yace ya zauna a Mashama a Kasar Katagum a Matsayin sarkin Hadejia ya Gaji wansa Ahmadu. Amma Tukur bai yarda ya zama Sarkin Hadejia ba saboda yana tsoron Buhari, sai yaga bazai iya yin haka ba. Kuma saboda Gudun kar Buhari ya kasheshi sai Tukur ya Gudu daga Mashema yayi kaura zuwa Kano Lokacin Sarkin Kano Usman Na1(1846-1855) Sai aka Turashi ya Mulki Yayari a Kasar Birnin Kudu. (Yayarin Tukur) Tukur ya zauna acan Har zuwa lokacinda ya Mutu 1909. Buhari kuma yaci gaba da mulkin Hadejia yana kai hare hare a matsayin Jihadi Har saida yakai Gabasawa,Sankara,Ringim da Kuka kwance A Arewa maso yamma. A Kudu saida ya mamaye Kununu,Takalafiya, Kafin baka, Doma, Ruba, Itas da Kwanda. A Gabas kuwa saida ya Mamaye Babuwari, Kazura, Dawah, Gatare da Margadu. Saida Sarki Buhari ya fadada kasar Hadejia tafi Ko ina fadin Kasa a karni na19.
GAMON KAFUR:-
HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Thursday, July 5, 2012
Tuesday, July 3, 2012
DAJIN DUHUN KARO A HADEJIA.
HADEJIA A YAU!
DUHUN KARO:-duhun karo wani Daji ne dake kasar Hadejia kuma yafi yawa a Gabashin Hadejia. Wannan Daji daji ne mai Dimbin tarihi wadda duk wadda yake kasar Hadejia zaice maka haka ya taso yaga wannan Dajin. Hasali ma wadda ya kafa Hadejia (HADE) ni'imar wannan Daji ce tasa ya zauna a wannan yanki. Dajin Duhun Karo yana tafe ne da Ruwa a Gefensa sannan ga Itatuwa masu bin Danshin ruwa a gefen ruwan, Kuma wannan dajin ya taso ne tun daga Falgore yamma da Kano har ya dangana da komadugu ta Jihar yobe, sannan ya nufi Jihar Borno har zuwa Tafkin Chadi.
Wannan Daji ya kasu da yawa a Kasar Hadejia inda ya bazu kuma yafi girma da Ni'ima a Yankin Baturiya da Gabta da yankin Kadira har ya shiga zuwa Kasar Gorgaram. Duk wadda ya saba bin hanyar kano ta Ringim zai ga wannan dajin musamman kwanar Auyo zuwa Hadin mai dan karofi inda nan ne ya fito har bakin titi musamman ma Burtalin fulani na Wajedu, sannan shine ya shiga Muhimbira har fateka zuwa Bubbar Riga yayi Gabas har Sansanin Sarkin Damagaram Tanemu.
Na shiga wannan Dajin kuma banda kukan tsuntsaye da Namun daji babu abinda kake ji. Nayi tafiyar kilo meter takai biyar a cikin dajin, har saida ya Kaini Askandun fulani da Akurya, na gamu da wani Bafulatani mai suna Musa kuma na tambayeshi shekarar sa nawa a wannan dajin? Sai yace shima anan aka haifeshi, kuma yanzu shima yana da 'ya'ya wadanda ya haifa a wannan Dajin. Na tambayeshi ko zai bani labarin wannan dajin? Sai yace ya tashi yaga Kuraye suna zuwa suna razana musu shanu, kuma yace akwai Namun daji kamar Gada, Barewa, Bauna da dai sauransu. Amma tunda aka fara sarewa dajin sai sukayi nisa kuma da 'yan farauta da suka damesu. Yace Amma har yanzu akwai kananan Namun daji kamar Zomo, Guza, kuma wani lokacin ana samun Gada. Tsuntsaye kuwa dukda harbi da ake Har yanzu akwaisu da dama.
Dajin in ka shiga cikinsa baza kasan ana rana ba saboda tsabar Inuwa da take ciki kuma ga Ruwa a gefensa. Akasarin bishiyoyin da ke dajin farar kaya ce da kuma Bishiyoyi kamar su Danya, Darbejiya, Gabaruwa, Kirya, Kanya, Magarya, da sauran bishiyoyi masu Ni'ima.
Kalu balenda wannan Daji yake fuskanta shine Sare saren Bishiyoyi da ake yi a cikinsa da kuma fadada Gonakai da makwaftan dajin sukeyi. Ta wani fannin kuma akan samun wasu suna kunna masa wuta. Amma dukda haka in ka shiga zai baka sha'awa. Na tambayi wani dattijo mai suna Garba Tandanu mai shekara 60, yace wannan dajin yasan lokacin da kuraye suke Hanasu zuwa Hadejia ta Rugar Isa inda sai sun zagaya ta Tuwankalta sannan zasuzo Hadejia Amma yanzu sai dai tsuntsaye da kananan namun daji. HADEJIA A YAU.
Subscribe to:
Posts (Atom)