"" /> HADEJIA A YAU!: DAJIN DUHUN KARO A HADEJIA.

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, July 3, 2012

DAJIN DUHUN KARO A HADEJIA.



HADEJIA A YAU! 

DUHUN KARO:-duhun karo wani Daji ne dake kasar Hadejia kuma yafi yawa a Gabashin Hadejia. Wannan Daji daji ne mai Dimbin tarihi wadda duk wadda yake kasar Hadejia zaice maka haka ya taso yaga wannan Dajin. Hasali ma wadda ya kafa Hadejia (HADE) ni'imar wannan Daji ce tasa ya zauna a wannan yanki. Dajin Duhun Karo yana tafe ne da Ruwa a Gefensa sannan ga Itatuwa masu bin Danshin ruwa a gefen ruwan, Kuma wannan dajin ya taso ne tun daga Falgore yamma da Kano har ya dangana da komadugu ta Jihar yobe, sannan ya nufi Jihar Borno har zuwa Tafkin Chadi.

Wannan Daji ya kasu da yawa a Kasar Hadejia inda ya bazu kuma yafi girma da Ni'ima a Yankin Baturiya da Gabta da yankin Kadira har ya shiga zuwa Kasar Gorgaram.   Duk wadda ya saba bin hanyar kano ta Ringim zai ga wannan dajin musamman kwanar Auyo zuwa Hadin mai dan karofi inda nan ne ya fito har bakin titi musamman ma Burtalin fulani na Wajedu, sannan shine ya shiga Muhimbira har fateka zuwa Bubbar Riga yayi Gabas har Sansanin Sarkin Damagaram Tanemu. 


Na shiga wannan Dajin kuma banda kukan tsuntsaye da Namun daji babu abinda kake ji. Nayi tafiyar kilo meter takai biyar a cikin dajin, har saida ya Kaini Askandun fulani da Akurya, na gamu da wani Bafulatani mai suna Musa kuma na tambayeshi shekarar sa nawa a wannan dajin? Sai yace shima anan aka haifeshi, kuma yanzu shima yana da 'ya'ya wadanda ya haifa a wannan Dajin. Na tambayeshi ko zai bani labarin wannan dajin? Sai yace ya tashi yaga Kuraye suna zuwa suna razana musu shanu, kuma yace akwai Namun daji kamar Gada, Barewa, Bauna da dai sauransu. Amma tunda aka fara sarewa dajin sai sukayi nisa kuma da 'yan farauta da suka damesu. Yace Amma har yanzu akwai kananan Namun daji kamar Zomo, Guza, kuma wani lokacin ana samun Gada. Tsuntsaye kuwa dukda harbi da ake Har yanzu akwaisu da dama.
Dajin in ka shiga cikinsa baza kasan ana rana ba saboda tsabar Inuwa da take ciki kuma ga Ruwa a gefensa. Akasarin bishiyoyin da ke dajin farar kaya ce da kuma Bishiyoyi kamar su Danya, Darbejiya, Gabaruwa, Kirya, Kanya, Magarya,  da sauran bishiyoyi masu Ni'ima.


Kalu balenda wannan Daji yake fuskanta shine Sare saren Bishiyoyi da ake yi a cikinsa da kuma fadada Gonakai da makwaftan dajin sukeyi. Ta wani fannin kuma akan samun wasu suna kunna masa wuta. Amma dukda haka in ka shiga zai baka sha'awa. Na tambayi wani dattijo mai suna Garba Tandanu mai shekara 60, yace wannan dajin yasan lokacin da kuraye suke Hanasu zuwa Hadejia ta Rugar Isa inda sai sun zagaya ta Tuwankalta sannan zasuzo Hadejia Amma yanzu sai dai tsuntsaye da kananan namun daji. HADEJIA A YAU.

3 comments:

  1. Mallam Ismaila kana da kishin garinku. Allah ya saka maka da alheri.

    ReplyDelete
  2. Wannan haka yake sai dai yanzu duk an sare dajin.

    ReplyDelete
  3. Bubban abinda yake jawo mana iska take barna shine sare bishiyoyi da akeyi. Ai da ba'a iskarda take tada mana hankali lokacin akwai dajin.

    ReplyDelete

RUBUTA RA'AYINKA!