"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, January 13, 2014

HAWAN SALLAR GANI (MAULUDI) A HADEJIA 13/01/2014.

HADEJIA A YAU!
Sallar Mauludi ko Gani a Hadejia ya samo asali ne shekara 90 da suka gabata, wato 1910-1925. A lokacin Sarkin Hadejia Abdulkadir aka fara hawan Mauludi ko Gani a Hadejia, kuma ya kirkiro wannan hawa na Gani ne daidai sabuwar shekarar Musulunci, a Inda yake Ganawa da Hakimansa na waje (District heads) domin suyi jawabin Nasarori da Matsalolinda suka samu a kasarsu a shekararda ta gabata.

Saboda bikin yazo daidai da shekarar Mauludin Manzon Allah (s.a.w.) Sarkin Hadejia Abdulkadir sai yakan hau da Yamma tare da Hakimansa kamar yanda abin yake har yanzu. Kuma a ranar da safe akan gudanarda bukukuwa na Nadin sarautar Hakimi idan ta kama. Sarkin Hadejia Abdulkadir yakan yi hawa da hakimansa inda ake zagaya gari kuma a lokacin yakan bi ne ta Unguwanninda suke da Tsangaya domin ya taya Malaman murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (s.a.w.).

Kamar yanda Abin yake har yanzu Sarki zai fito daga fadarsa da yamma, zai bi ta Tudun mabudi ta Kasuwar kuda sannan yabi ta Kasgayama zuwa Kwarin madaki, sai ya fito ta bayi zuwa Magama hudu zuwa Unguwar Dukawa zuwa Hudu, sannan zai wuce ta Tagurza zuwa Majema zuwa bakin kasuwa, sannan sai ya biyo ta Makwallah zuwa Baderi zuwa Kofar Liman. Sannan ya koma fadarsa. Hadejia A yau.

Monday, December 30, 2013

TARIHIN KAFUWAR HADEJIA A TAKAICE..

HADEJIA-TARIHIN KAFUWARTA Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, a yawon farauta da yakeyi ne wata rana yana tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo ko da tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi mamakin hakan har ma sai yabi sawunta. Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye suna shawagi a gurin. Sai ya yanke shawarar zama a wannan gurin, kuma hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa yake harbe harben Namun daji kuma yayi suw, wato kamun kifi. In ya kashe namun daji sai yaje ya sayar da fatun. Harma ya dauko Matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan gurin. Kuma mutane sai suke zuwa sayen fatu da nama a wajensa. Duk wanda yazo gurin sai yayi sha'awar zama a gun, haka nan gari ya fara bunkasa wasu maharba, wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada zango a garin. To kasancewar gari sai da shugabanci ne yasa shi Hade ya zama shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu ko nama sai yace na tafi garin Haden jia. Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia. Kuma bayan zamanin wannan mutumin Hadejia taci gaba da zama gari kuma tare da shugabanci wato mulkin Habawa. Hadejia A yau! Kuma a lokacin akwai kananan Garuruwa masu cin gashin kansu kamar Rinde, yayari, wunti, Anku da dai sauransu. Wadanda suma suna da nasu sarakunan a wannan Lokacin. Amma yanzu duk unguwanni ne a cikin garin Hadejia. Kuma Hadejia sunyi sarakunan Habe guda talatin da biyu(32) amma sunan mutum uku ake dasu wadanda sukayi mulki kafin zuwan Fulani. 1, BAUDE 2, MUSA 3, ABUBAKAR. Kuma a lokacin Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin Hadejia tana karkashin Mulkin Habawa ne, kuma ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman dan fodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune suke sarautar Kasar Hadejia. Hadejia A yau..