HADEJIA A YAU!
MASARAUTAR HADEJIA………
- Takaitaccen Tarihin Masarautar Hadejia .
Masarautar Hadejia dadaddiyar masarauta ce wadda ta kafu shekaru da dama da suka gabata, daga lokacin kafuwarta kawo yanzu masarautar tayi fice da kuma yin suna bisa ga muhimman tarihi da take dashi. sannan tana daga cikin masarautun da sarakunan Habe suka mulka kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, kuma tana daya daga cikin masarautun da suke KarKashin Daular Usmaniyya. Daga Gabas ta yi iyaka da Tsohuwar Daular Borno da Gorgaram, daga yamma tayi iyaka da Masarautar Kano, daga Kudu kuma ta yi iyaka da Masarautar Katagum sannan daga Arewa ta yi iyaka da Masarautar Gumel. Birnin masarautar yana cikin garin Hadejia dake Arewa maso gabashin Jigawa a Arewacin Nigeria, sunan garin ya samo asalinsa daga wani Maharbi wadda shine ya kafa garin, wannan maharbi ana Kiransa da suna HADE, yana da matarsa da ake Kiranta da suna JIYA, Sunayen wadannan mutane shi aka hada ya zama Hadejia . A wancan lokacin mutanen wasu garuruwa in zasu zo sukan ce mun tafi garin Haden jiya, wato ana masa Lakabi da sunan Matarsa. Saboda taKaita kalma ta Hausawa shine yasa aka hade sunan ya zama Hadejia . A wani littafi da Marigayi Tafidan Hadejia Abdu Maigari ya rubuta ya bayyana cewa ‘‘Shi wannan mutumin da ya kafa Hadejia wato Hade ya taho ne daga yankin Machina a yawon farauta da yake har ya iso wannan yanki, kuma da ya shigo sai yaga Daji mai Ni’ima da tsuntsaye da namun daji ta ko ina, kuma ga kogi ya fito daga yamma ya gangara zuwa gabas Sannan ga ‘ya’yan itatuwa kala kala. Da ganin haka sai ya kewaye dajin sosai don ya samu inda ya dace ya zauna, sai ya samu wuri ya kafa Gadonsa irin na maharba yaci gaba da farautar Namun daji da tarkon tsuntsaye’’. Bayan kwanaki wannan maharbi yana zaune a wannan wuri sai yayi shawarar ya koma ya Dauko matarsa don suci gaba da zama a wannan wuri. A lokacinda yayi niyyar komawa sai ya debi abinda zai iya diba na naman da yayi farautarsa ya dawo garinsu ya Dauki matarsa ya koma wannan dajin da yanzu ake kira da suna Hadejia , sai ya kafa bukkarsa a kan jigawa kuma yaci gaba da farautarsa a wannan wuri har mazauna karkara dake kusa da wurin suka san da zamansa suke zuwa sayen nama da sauran dabbobin daji. Ana haka ne jama’a suka rinKa zuwa suna kafa bukkokinsu wasu masunta wasu kuma mafarauta da masu kamun tsuntsaye har gari ya zama gari ake Kiransa Garun Haden Jiya, sannan akayi shugabanci, zuwa wani dogon lokaci aka takaita Kalmar ta zama Hadejia . Ance a lokacinda ya zauna a bangaren Arewa akwai wani gari da ake Kira Hadegwaigwai inda yanzu Rubban Dakata take, sannan a bangaren gabas akwai gari da ake kira Kulunfarda inda ada can yake kan hanyar Tandanu. A yamma kuma akwai garin Kadime sannan a Arewa akwai garin da ake Kira Majeri, a bangaren kudu kuma akwai garin Tunawa wadda yanzu ake Kira Auyakayi. Sannan akwai Kudiginda HadebaKo wadda a lokacin take kusa da Kafur, sannan akwai Urki wadda yanzu ake Kira Unik sannan akwai Majawa, da kuma manyan garuruwa irinsu Auyo, Garungabas, Kazura, Dawa da Fagi.
A wancan lokacin ance Hadejia tana Karkashin Daular Auyo ne amma wasu sunce a’a tana KarKashin Ikon Garungabas ne tunda daga can ne ake nada Sarki ake kawoshi Hadejia, masu wannan da’awa sun bada labari kamar haka… ‘A zamanin Sarkin Kano Yakubu Dan Abdullahi Barja wadda yayi sarautar kano a cikin shekarar (1452-1463), Algalfati Dan sarkin Machina yaje kano tare da ‘yan-uwansa guda uku inda sarkin kanon ya bashi sarautar Gaya, dan-uwansa na farko kuma yaje Rano sarkin Rano ya bashi sarautar Dal, na biyun kuma yaje Zazzau Sarkin Zazzau ya bashi sarautar Gayan, na ukun yazo Biram Garungabas inda Sarkin Gabas ya bashi sarautar Hadejia . Zuriyarsa ne sukayi mulkin Hadejia har tsawon lokacinda Sarkin Borno Mai Ali Ghaji ya tura Dansa Mai Idris Aloma ya yaki kano, sai ya biyo ta Hadejia ya yake ta ya cinyeta da yaki da sauran Kasashen dake yammacin Borno, sai ya danka ikon Hadejia da Garungabas da Dawa da Fagi a hannun Galadiman Borno, kuma shi Galadiman Borno sai ya barsu a rarrabe kamar yadda suke tun farko. Sashen Auyo ya barshi a hannun sarkin Auyo, Hadejia ya barta a hannun sarkin Hadejia , Garungabas ya barta a hannun sarkin Gabas, sannan Dawa da Gatare da sauran duk sai ya barsu a hannun fadawansa, amma duk a wurinsa suke karbar umarni kuma shi ake kaiwa Albarkar Kasa har zuwa tsawon lokaci’. Koda yake ba’a samu rubutaccen tarihi game da sarakunan Habe da suka mulki Kasar Hadejia ba, ance anyi sarakuna guda Talatin da biyu (32), kafin mulkin Fulani. Masarautar Hadejia tana da fadin Kasa wadda ta kai Murabba’in kilo mita dubu shida da Dari tara da sittin da uku (6963), wannan yanki yana da shimfidaddiyar Kasa mai kyau wadda ake kwatanta yanayinta da na Kasar Chadi, kuma tana da Jigayi masu tarin yashi da kuma kwari mai tabo da laka amma bata da tsaunuka ko Duwatsu. Kasar Hadejia tana da Kogi wadda ya kasance akwai ruwa kowane lokaci, sannan tana da fadamu masu yawa wadanda suke Kafewa lokaci zuwa lokaci. Kogin Kasar Hadejia ya taso ne daga Kudancin Katsina ta Arewa da Zaria sannan ya nufi Arewa maso gabas ya shigo ta Kasar Kano ya ratsa Kasar Hadejia, sannan ya nufi Tafkin Chadi. Wannan Kogi ya ratsa ne ta Kudancin Hadejia da Gabashinta, wannan bangare ne da yake samarda ruwan sha da kamun kifi da kuma aiwatar da Noman rani. A lokacin damina kogin yakan cika inda yake samarda Kananan fadamu a sassa daban daban wadda ake amfani dasu a wajen noman lambu. A bangaren Noma Masarautar Hadejia tana gabatarda noma a lokuta biyu wato Rani da Damina, inda masana yanayin Kasa suka tabbatar cewa duk abinda aka shuka a wannan Kasar zai fito yayi kyau da iznin Allah saboda yanayin kyawun Kasar.
GUDUNMAWAR DA MASARAUTAR Hadejia TA BAYAR GA DAULAR USMANIYYA….
Masarautar Hadejia kamar sauran Masarautu ta bada gudunmawa sosai wajen tabbatar da kafuwar Daular Usmaniyya, domin tana daga cikin masarautun da suke iyaka da Daular Barno. Masarautar Hadejia ta nuna goyon bayanta ga Jihadin Shehu Usman Danfodiyo a zamanin Sarkin Fulanin Hadejia Umaru. Sarkin Fulani Umaru yana nan yana sarautar fulani sai suka samu labarin jihadin Shehu Usman Danfodiyo , Bayan yaji labarin jihadin shehu sai ya tara jama’ar Fulani sukayi shawara da suje suyi Mubaya'a da Da'awar Shehu, anan wasu manyan Fulani suka ki yarda da hakan, ciki harda Kawunsa mai suna Jinagana. Sai sarkin Fulani Umaru ya tura mutanensa Karkashin jagorancin Dan uwansa Malam Sambo, sukaje suka miKa mubaya'arsu ga Shehu da kuma nuna goyon baya ga da'awarsa ta jaddada Addinin musulunci. Shehu yayi maraba da zuwansu kuma ya baiwa Sambo Tuta kuma yayi musu umarnin shiryar da sauran yankunan nan biyar na Kasar Hadejia . Sannan yacewa Laraima ya kula da yankin Gabashin Hadejia inda Marma da Fagi da Dawa suke yaje yayi kokarin shiryar dasu kan tabarkin Addinin musulunci. Amma bai bashi Tuta ba, sai sukayi bankwana da Shehu suka dawo Hadejia suka isarda sakon Shehu ga Sarkin Fulani Umaru suka sanar dashi kyautar da Shehu ya yiwa Laraima, sai aka hada Laraima da mutane suka tafi yankinda Shehu yace yaje ya shiryar dasu wato Marma da Fagi da Dawa. Laraima sai ya zauna a Marma saida suka shiryar da duk mutanen wannan yankin, kuma ‘ya’yansa ne sukaci gaba da shugabancin wannan yanki na gabas har zuwa lokacinda Sarkin Hadejia Buhari ya hade Kasar da tasa, wadda a baya MaDaci ce iyakar Hadejia daga gabas. Wannan yana nuna mana cewa masarautar Hadejia ta bada gudunmawa game da tabbatar Daular Usmaniyya, domin tana iyaka da Daula mai Karfin gaskekuma dadaddiyar wato Daular Kanem Borno.
A zamanin Sarkin Hadejia Sambo masarautar ta bada gudunmawa sosai wajen tabbatar da Umarnin Shehu na Jaddada Addinin Musulunci, bayan rasuwar Dan uwansa Sarkin Fulani Umaru an nada Dan wansa wato Mamman Kankiya, wadda shima ya rasu cikin watanni takwas. A lokacin da Sarkin Hadejia Sambo yayi shekara yana sarautar Hadejia sai yayi niyya ya tafi wurin Shehu, da zuwansa Shehu yayi murna kuma yayi godiya ga irin KoKarin da Sambo yake a Kasar Hadejia . Bayan Sambo yayi kwanaki a wurin Shehu ya gama abinda zaiyi sai yayi sallama da Shehu yayi shirin dawowa gida, Shehu ya Kara yin godiya ga Sambo kuma ya baiwa Sambo ikon duk wani Bafulatani wadda yake da Jar Saniya (Aborawa) tun daga bakin Dajin Rubu har zuwa iyakar Kasar Barno. Daga nan sai sambo yayi godiya sukayi bankwana ya dawo Hadejia tare da mabiyansa. Wannan kyauta da Shehu ya masa ta Ikon duk Fulani masu jar Saniya (Aborawa) tasa Sambo yawan Dawainiya domin nemawa wadannan Fulani matsuguni, kuma har zuwa wannan lokaci duk Bafilatanin da ka ganshi da Jar Saniya idan ka tambayeshi zakaji Asalinsa daga Kasar Hadejia yake.
Sarkin Hadejia Sambo ya sake faɗaɗa Kasar Hadejia daga Gabas har saida ya mamaye galibin Kasashen da Galadiman Barno yake iko dasu suka dawo KarKashin ikon Hadejia , amma banda Dawa da Fagi domin Shehu ya bada su ga Laraima. Daga yamma har saida ya kai Kaugama da Sharkawa, da Majeri a yamma ta Arewa. Daga Gabas maso kudu saida yakai har Damaturu inda ya YaKi garin, sannan daga Gabas kuma ya tsaida iyakarsa a Madachi. A bangaren Arewa kuwa galibin garuruwan sun bishi ba tare da wata jayayya ba saida ya mamaye Garungabas da Kazura da Gatare har zuwa iyakar Machina da Damagaram.
Saboda irin gudunmawa da Masarautar Hadejia ta bayar ga Daular Usmaniyya, an taba baiwa Sarkin Hadejia Muhammadu Sarautar Sarkin YaKin Sarkin Musulmi.
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!