A lokacin da Sarkin Marma Muhammadu ya dawo daga Sokoto wajen taya Sarkin Musulmi Yakin Madarumfa, jama'ar gari da mahaya Dawaki sun fita taryen sa domin kafin yazo labari ya iske Hadejiawa cewa Sarkin Musulmi ya nada shi Sarautar Sarkin Yakin Sarkin Musulmi na Gabas. Kafin Sarkin Marma ya iso kofar Fada Sarkin Hadejia Haru Bubba ya fito filin fada don jiran isowar Sarkin Marma, ko da ganin Sarki ya fito sai aka sanarwa Sarkin Marma cewa Sarki yana filin kofar fada.
Shi kuwa Sarkin Marma Muhammadu da ya iso kusa da Masallacin Juma'a sai ya tsaya anan, mahaya dawaki suka rinka zuwa suna yi masa Gaisuwa (Jafi). Anan Sarkin Jauje ya shirya masa wata waka da yake cewa...
Wai ina wani ba kai ba zaki wan dawa,
Uwa hana kukan talaucin duniya,
Mu je mai randa mu debo tulina,
Ina ke gaba ina ke gaba,
Da ku fadawa ku daina haye masa.
Bayan an gama gaisuwa (Jafi) sai Sarkin Marma ya nufi Kofar fada yayi gaisuwa a wurin Sarkin Hadejia Haru Bubba, sannan ya wuce gidan sa ya sauka. Bayan ya zama Sarki a shekarar 1885, sai ya maida wannan Jafin Al'adar hawan sallah, duk sallar Azumi da Layya zai tsaya a kusa da Masallacin Juma'a Hakimai su zo su yi Jafi. Haka Al'adar ta ci gaba har zuwa yau.
Allah ya karawa Masarautar Hadejia daraja da daukaka.
Ismaila A Sabo.
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!