"" /> HADEJIA A YAU!: GANUWAR HADEJIA DA KOFOFIN TA...

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, June 15, 2021

GANUWAR HADEJIA DA KOFOFIN TA...

HADEJIA A YAU!










Garin Hadejia gari ne wadda ganuwa ta kewaye shi, sannan yana da kofofin shiga guda biyar. 

In muka duba Report din Lugard akan Africa wanda yace "Duk kasar Hausa babu gari kamar hadejia wajen jarunta da rundunar mayaka majiya karfi, akwai ganuwa a zagaye da garin masu kofofi guda biyar masu karfin gaske wanda harsashin bindiga bazai iya fasa kyauran kofar ba." Lugard Ya rubuta wannan magana acikin (kundin Najeriya ta Africa shafi na 247). Wanda yake ajiye a dakin da ake ajiye kayan tarihi na Najeriya ta Africa a Arewa House Kaduna.

A wata wasika da Captain Philips H. C. B. ya rubutawa Colonel Larymore ranar 17 December, 1903. Inda yace. 
 "HADEJIYA BUBBAN GARI NE SOSAI KUMA TANA DA GAWURCACCIYAR GANUWA MANYA-MANYA MASU KYAU SOSAI A  ZAGAYE DA GARIN MAI TSAWO KIMANIN KAFA TALATIN GABA DA BAYANTA, TA KO INA A ZAGAYE DA ITA AKWAI KOFOFI GUDA BIYAR KADAI, ITA KANTA GANUWAR KAURINTA YA KAI KAFA TALATIN DAGA KASA. KYAMAREN KOFOFIN MASU KARFI NE SOSAI YADDA HARSASHIN BINDIGA BAZAI IYA FASA SHI BA CIKIN SAUKI, YAWAN JAMA'AR DA KE CIKIN GARIN SUN KAI KIMANIN DUBU TAKWAS ZUWA DUBU GOMA. FADIN GANUWAR GARIN YA KAI KIMANIN MAYIL HUDU DA RABI. GARIN ZAI YI KWATANCI DA KAMAR RUNDUNA, AMMA TA KAI KIMANIN DARI UKU DA HAMSIN (350)."

A Zamanin Sarakunan Habe garin Hadejia bashi da ganuwa sai dai wani abu da ake kira "KAFI", wato wani Asiri ne na kafewa gari wadda abokan gaba bazasu samu nasarar yakar garin ba. Shi kafi ana sanya Layu ne a cikin Tukunya ko a kahon rago da sauran su, sannan a binne a farkon gari da karshen gari ta kowane bangare. A lokacin da Sarkin Hadejia Sambo ya samu nasarar korar Sarkin Hadejia na Habe, bayan ya zauna a gidan sarautar su sai ya sake tsara taswirar fadar sa, inda ya sake gine-gine da soraye da masaukin baki da sauran su. Dalilin da yasa aka samu Kududdufin Atafi kenan, domin anan aka rinka debo ƙasar da aka gina sorayen fada.

Sarkin Hadejia Sambo shine ya gina ganuwa a Hadejia, inda kuma yayi kofofin shiga garin guda hudu. Wannan Ganuwar daga yamma iyakar ta Kofar Jarma, daga kudu kuma Bakin Ramin Atafi kusa da gidan Sarkin Busa. Daga gabas kuma iyakar ta ramin Tankari kusa da Unguwar Hudu, daga gabas kuma iyakar ta Unguwar Dallah. A zamaninsa kuma Fulani suka bar mazaunin su da yake Rinde, can kusa da Gandun Kabo suka dawo cikin garin Hadejia, inda da yawan su sai suka zauna a yamma da gari inda yanzu Unguwar Rinde take. Bayan Sarkin Hadejia Sambo shima Sarkin Hadejia Buhari ya fadada ganuwa ta bangaren Kudu har sai da ta kai kusa da Kogin Hadejia, shima Sarki Haru ya ci gaba da fadada ganuwa har sai da ta kai inda take a yanzu, sannan ta ci gaba da zama kofofin ta guda hudu. 

Kofar Gwani itace Kofar gabas
Kofar Matsaro itace kofar yamma
Kofar Kogi itace kofar kudu
Kofar Barno itace kofar Arewa.

Ganuwa kuma ta zagaye garin domin babu ta inda zaka shiga cikin gari sai ka bi ta kofofin nan. A zamanin Sarkin Hadejia Muhammadu wadda ya gaji Sarkin Hadejia Haru ya sake ginin kofofin nan, inda aka sake musu gini mai kyau a shekarar 1871. Dalilin wannan gini ne ma yasa ake kiran kofar Gabas da suna Kofar Gwani, domin wani magini ne mai suna Gwani ya gina su har ma da Soron fada da ake kira Soron Bubban Gwani.

Itama Kofar Kogi ta sauya suna a zamanin da aka rufewa Sarkin Hadejia Umaru Kofa, saboda ambaton kalmar kyale su da yayi shine yasa ake kiran ta Kofar Kyale su. 

Kofar Barno itama ta sauya suna yanzu an fi kiran ta da sunan Kofar Arewa, dalilin da yasa ake kiran ta da Kofar Barno kuwa shine, saboda Unguwannin da suke kusa da kofar duk mazaunin Barebari ne, irin su Gagurmari, Kilabakori, Kakaburi, Zonagalari da sauran su. 

Itama kofar yamma dalilin da yasa ake kiran ta da suna Kofar Matsaro shine saboda Sarkin Kofar ne ake kiran sa Mai Tsaro, shine ake cewa kofar Mai tsaro daga baya sunan ya sauya ya zama Matsaro. 

Zamanin Yakin Hadejia da Turawa a shekara ta 1906, Turawan sun rusa ganuwa ta Kudu da gari inda suka samu suka shigo Hadejia suka cita da yaki. Bayan an gama yaki ba'a gine wurin da Turawan suka shigo ba, sai aka gyara wurin aka saka masa kyauren kofa, sannan ake kiran kofar da suna Kofar Talata. An yiwa wannan Kofa lakabi da sunan ranar da Turawa suka fasa Ganuwar suka shigo Hadejia, wato ranar Talata.

Bayan shekaru da yawa kuma wannan kofa sai ake kiran ta da suna Kofar Mandara, domin akwai wata mata da ake kira Mandara kullum a wannan kofar take wuni domin tana tura dabbobin ta kiwo tun safe har zuwa yamma. Saboda karuwar Kofar Mandara sai kofofin Hadejia suka zama guda biyar.

Tun zamanin Sarkin Hadejia Haru wadannan Kofofi guda hudu suke da Sarakunan su, wato masu kula da su kenan. Wadda kuma sune suke sarautar Unguwannin da kofofin suke, misali... Mai Unguwar Matsaro shine sarkin Kofar Yamma, haka sauran kofofin duk masu unguwannin wurin sune sarakunan Kofofin.

No comments:

Post a Comment

RUBUTA RA'AYINKA!