Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, November 4, 2012

WAKAR TARIHIN YAKIN HADEJIA DAGA LIMAN MUHAMMADU (Fassara daga Alh. Ibrahim katala).

Easily Upload Your Images To Myspace
Free Music Hadejia A yau. 1, Allahu sarki shi kadai yake wahidun, sammai da kassai jalla bashi da kishiya. 2, Shi ba fari shi ba baki ba ubangiji ba ja ba ba alkashi bashi ga rawaya. 3, Ba sake sake ba ba kamar yarani ba shudi da kore jalla bashi da mai kama. 4, Zatinsa baya tattara bai rarraba da kawai da motsi bayayi ko sau daya. 5, Sarkinda ba na biyunsa ba na uku nasa ka dadan basira zanyi waken shahidu. 6, Ranar talata munga tashin duniya Rannan Muhammadu yai shahada zahira. 7, Shi yai jawabi ya fada shi bai gudu kuma bashi mai kamu a darul duniya. 8, Raggo ake kora a bishi a cim masa amma sadauki bai gudu sai faduwa. 9, Sarki Muhammadu yai jawabi ya cika shi bashi mai kamu a jashi ya tunkiya. 10, Dan melle sarkin yaki shima ya fada in dai da rai sarkinmu baya kamuwa. 11, Ma'ajin Hadejia saleh shima ya fada mun dau shahada zahira bahakikiya. 12, Manya da yara duk shirin yaki suke kowa yana wanka yana yin alwalah. 13, Kowa yana yin sallama a gida nasa sunsa gabansu a lahira ba dawaya. 14, Jama'ar Hadejiawa fa duk sun hallara kowa yana cewa fa mun zama shahidai. 15, Sarki Muhammadu mai shahadar zahiri ba badili ko dai cikin tawaga tasa. 16, Shi bai kamar tsoro ba baya razana kan ya ije ma babu sauran hanzari. 17, Ajali idan yayi babu kwana duniya kai dai zamo kullum shiri duka safiya. 18, Shi bai kamar tsoro a baya razana baya gudu dan Garba sarkin jarumai. 19, Mutuwa tafarki wanda kowa zayabi ai kulli nafsin dukka rai zai dandana. 20, Aka daura sirdi nai ya hau bisa ya tsaya yace mu dau himmar shahada zahira. 21, Sarki Muhammadu baya tsoro ko kadan Allah ma'aiki su take tsoro kadai. 22, Hauninsa linzamin mayani ya rike damansa tasbihi salatin annabi. 23, Dan mai karatu tudun kasa ba dawaya dan garba jikan sambo sarkin adalai. 24, Duk mai shahada auwalinsa madacima suka barace da fari ya mutu shahidi. 25, Farkon hawa yaki galadima sai haru ranar talata sun ka sauka a barzahu. 26, Alkali sarkin yaki kaura amada sarkin arewa da sunkaje can sun tsaya. 27, Suka jeru sunka tsaya a nan kofar gabas kafin suje har mai ruwa ya taddasu. 28, Kasan igwa dokinmu shi bai santa ba duka dokuna na faduwa ba lissafa. 29, Igwa tana tashi madafa na zuba yau sai ta Allah babu sauran shawara. 30, Jaruman Muhammadu basu tsoro ko kadan sun gwammace mutuwa da dai subi kafiri. 31, kuma sabo jikan tete harbi nai ake anan a kofar fada duk suka tuntsure. 32, Firyan Hadejia shi da bori na salihu kofar gabas suka fadi nan aka cim musu. 33,Dan Dodo Barwa da shi da gwanki baran nufe, sun karbi hartashi a kwaryar kai nasu. 34, Ai babu mai mutuwa gaban ajali nasa kan surfa gero kan daka wasu sun fice. 35, iko idan Allahu yayi nufi nasa ai ba tsimi balle dabara ko daya. 36, Tamkar kamar inuwarka baka guje mata in kai gudun ta bika harma ka tsaya. 37, Hartashi na yawo kamar burduduwa tamkar zubar wake a can a masussuka. 38, Ya ratsa soraye ya ratsa katanguna tamkar kabewa ko kamar tumfafiya. 39, Yasha zarar soro ya keta katanguna da kago da zaure sun zube ba tambata. 40, Tsarnu da kurna har kasa durumi dada ya kar dabinai cediya da itatuwa. 41, Rannan Hadejia munga tashin hankali Allah da manzo su kadai ne magani. 42, Abdulwahabu baka tana hannu nasa artashi ya samar ya tsinke tsirkiya. Edited by (Idris M. Eddy) DA SAURAN BAITI SAI A SAURAREMU A GABA.