Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, April 21, 2013

TARIHIN SARKIN HADEJIA UMARU DAN BUHARI DA ZUWAN SARKIN DAMAGARAM HADEJIA..

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU!



SARKIN HADEJIA UMARU: A SHEKARAR 1863 allah ya yiwa Sarkin Hadejia Buhari rasuwa a Yakinsu da sukayi da Gogaram (bade). Ko da aka dawo Hadejia aka binne shi sai Manyan fadawan Hadejia wadanda akwai Amana tsakaninsu dashi Buhari. Kamar SARKIN AREWA TATA GANA DA SARKIN YAKI JAJI suka jajirce Sai an Nada UMARU DAN BUHARI SARKIN HADEJIA. kuma hakan Akayi!


SARKIN HADEJIA UMARU NA BIYU an nadashi yana da shekara Goma sha Takwas (18). Kuma manyan fadawan Mahaifinsa sune suke gudanar da Sarautar tunda shi yaro ne. Kuma a zamaninsa Sarkin Damagaram Tanimu ya kawo yaki Hadejia. Kuma yayi sansani a Arewa da Hadejia daga nan har Jigawar Kasim mutanensa ne. saida yayi kwana Arba'in ana yaki amma Hadejiawa basu fasa wasanninsu na dandali ba. Sannan kuma basu fasa duk harkokinsu na kasuwa ba, su kuma mutanen Sarkin Damagaram suna kaiwa farmaki kauyuka suna kwace musu kaya! Sannan sun hana mutanen kauyuka shigowa Hadejia domin saye da sayarwa. A nan kuma sun hana Makiyaya kiwon Dabbobinsu, Sai sarkin Arewa yasa akayi sanarwa a Hadejia cewa: duk mai dabbobi gobe ya sako su za'a kaisu kiwo, kuma hakan sukayi suka saki dabbobinsu Sarkin Arewa da Mutanensa sukaje sukayi kiwon suka dawo. Ta wajen Dan-Rago kusa da Maficin Sarki.

Da Abin ya ishi Mutanen Hadejia sai suka Sanar da Sarkin yakin Hadejia Jaji, sai ya tara Fadawan Hadejia yace Naji ance Sarkin Damagaram yazo, Yau wajen kwana 40, sukace hakane! Sai sarkin Yaki yace so kuke yazo ya koremu daga Garin?

Da safiya tayi sai sarkin yaki Jaji ya hau dokinsa ya dauki Takobinsa ya fita yacewa sarkin Kofa in ya fita ya rufe Kofar Gari, kuma ko an koroshi karya sake ya bude, idan ya bude masa to zai kashe shi. Sarkin yaki Jaji yaje ya fara baza Mayakan sarkin Damagaram yana korasu, saida ya korasu har Rumfar Sarkin Damagaram ya dawo da niyyar Washegari aci gaba da yaki.

Da sarkin Damagaram yaga anyi haka sai ya tara Hakimansa da fadawa yace gobe zamuci Hadejia da yaki. Suka amsa suna Alwashi, bayan an baje sai Chiroman Damagaram ya samu sarki yace masa Shawara nazo in bayar, sarki ya yarda. Chiroma yacewa Sarkin Damagaram duk garin da mukaje musu yaki basu da sukuni saboda suna tsoronmu, Amma yau kwananmu Arba'in (40) Hadejiawa basu fasa duk abinda sukeyi ba! Kuma mun samu Labarin Sarkin Hadejia bai san munzo ba, yacewa sarki Ina ganin ya kamata ko mu shiga mu yakesu ko kuma mu koma Gida!

Wata rana ana yaki Sai aka harbi dokin Sarkin Arewa! Koda ya mutu sai akaje gida aka dauko wani Dokin aka cire kayan wancan Dokin aka sakawa wanda aka kawo. Tata gana ya koma kan doki, kashe gari ana cikin yaki sai Tata gana ya sauko daga Dokinsa yayi alwala ya koma kan Dokin, to ashe Sarkin Damagaram yana kallon su sai yace Lalle Sarkin Hadejia ya Isa ana yaki ka sauko kayi alwala? Jiya ma an kashe masa Doki amma saida akaje aka dauko wani a gari? Sai Zagin Sarkin Damagaram yace ai ba Sarkin Hadejia bane Yaronsa ne! Sai Sarkin Damagaram Tanimu yace to Ina Sarkin Hadejian? Sai zaginsa yace ai ance yana gida tunda aka fara yakin nan bai taba zuwa ba. Sai sarkin Damagarm yace wa fadawansa Gobe zamu bar Hadejia kar mu tsaya ayi ta kashemu. Saboda Sarkin Hadejia ya raina mu kwananmu Arba'in amma bai taba zuwa anyi yaki dashi ba? Wa yasan me zai mana in ya zo? Amma basu san Sarkin Yaro bane. Washe gari suka juya suka koma Damagaram. Kuma lokacinda sukazo Hadejia Da kaka ne! Anyi girbi Manoma basu gama Tare Amfaninsu ba. Shi yasa suka dade a Hadejia saboda akwai abinci da ruwa a kusa dasu.

SARKIN HADEJIA UMARU Mutum ne mai son Nishadi kowane Lokaci yakan fita Bakin kogi ko Gona Domin Debe kewa. Kuma anyi amfani da wannan Damar inda wata rana ya fita sai aka Rufe Masa Kofa. Koda yazo yaga kofa A rufe sai ya juya ya tafi Chamo ya zauna. Aka nada Kanin Mahaifinsa Sarkin Hadejia Wato HARU BUBBA. 1865-1885. Shi kuwa UMARU DAN BUHARI yayi zamansa a Chamo kuma Ya rasu a shekarar 1920. Allah yaji Kansu Ameen.

HADEJIA A YAU.