Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, November 1, 2016

TARIHIN GARIN KANO.....


               TARIHIN GARIN KANO….


Tarihin Birnin kano yana da tsawo kwarai yana nan kuwa a Rubuce, Munji ance wani mai suna Bagauda ne ya fara Sarautar Kano, kuma ance jikan Bayajidda ne wadda ya kashe Macijiyar Daura. Tun daga zamanin Bagauda har karshen zamanin da Habe suka yi Sarauta anyi sarakuna Arba’in da takwas (48) a kano.

FARKON SHIGOWAR MUSULUNCI…
Ganuwar Kano ta farko an gina ta wajen shekara fiye da Daari takwas da tamanin (880) da suka wuce, amma a lokacin Birnin bashi da girma kamar yanzu, amma ban samu labarin sarakunan lokacin ba sai dai ance a lokacin Maguzawa ne. sai wajen tsakanin 1300 da 1400, wajen shekara dari bakwai da suka wuce, a zamanin wani Sarki da ake kira Yaji, a lokacin ne Addinin musulunci ya shigo kano. Watakila Fulani ne suka shigo dashi, nan da nan mutanen kano suka karbi Addinin musulunci hannu biyu-biyu suka shiga gina masallatai wannan shi yasa mutanen kano suka fara yaki da mutanen da suke kusa dasu da wasu kasashe na Hausa, suka shiga kai hari ga mutanen da suke kudu dasu wato mutanen Bakin Kwara har Biniwai.
      Daga baya sai mutanen da kano taci da yaki suka ture mata Ganuwar suka kuma kore mutanenta, ganin haka sai Ban gaskiyarsu ga Addinin musulunci yayi sanyi suka koma addinin maguzancinsu. Daga nan suka shiga yaki da Zazzau, wani lokaci suyi Nasara wani lokaci ayi Nasara a kansu. A wajen  shekarar 1420, watau shekarar 527 da suka wuce, a wannan lokacin ne  mutanen kano suka fara gamuwa da mutanen Barno, A lokacin ne kuma Rakuma suka fara shigowa kasar Hausa. Sukazo da Ilmi da Littatafai da suka samo daga Timbuktu, daga nan ne hanyar ci gaba ta bude a kasar Hausa musamman Kano.

ADDININ MUSULUNCI YA ZAUNA.
Muhammadu Rumfa yana daya daga cikin shahararrun sarakunan kano, yayi Sarauta tsakanin 1463 zuwa 1493, A zamaninsa ne malamai sukazo daga kasar Masar suka gyara Addinin musulunci a Kano. Muhammadu Rumfa ya ginawa kansa Fada ya kuma gina sabuwar Ganuwa mai kofofi Bakwai (7), a lokacin Birnin ya cika kwarai da jama’a har wasu suna gina gidaje a bayan Ganuwa. Kano kuma sai ta juya yake yake da Katsina, har akwai wani yaki da suka shekara goma sha daya suna bugawa, daga baya Kano taci Nasara. Wani shahararren Sarkin Kano kuma shine Muhammadu kisoki a farkon sarautarsa abin bai yiwa kanawa kyau ba, don wadansu mutanen wajen Timbuktu sun kawowa kasar hari kuma sukaci birnin, amma daga baya kano ta murmure harma suka fara yake yake da Barno. Wannan yaki anyi ta bugashi har kusan zuwan Turawa, mutanen Jukun kuma sun kawowa kano hari har sun cisu, suka saka musu Haraji suna biya amma Jukunawa basu dade ba.

          Daga su fa sai Barno ta lakume kano, duk wadda yasan Birnin kano sosai yasan  gidan da ake kira Gidan Shettima. Nan ne gidan Razdan na cikin Birni, to nan ne gidan da Wakilin Shaihun Barno ke zaune a kano a lokacinda kano ke karkashin Barno.

        FULANI SUN KARBE MULKI…….
Cikin shekarar 1806, watau wajen shekara 216 kenan sai Tawayen Fulani ya kai kano. Anan wani shugaban Fulani da ake kira Dan Yahya ya buga da sarkin kano a wani wuri mil 25 daga Arewacin Birnin kano, yaci Nasara a kansa. Amma dukda haka hargitsi bai kwanta ba. Gidajen Sarauta biyar na Fulani kowa ya kawo gwaninsa yace shi za’a yiwa Sarautar kano. Da aka rasa tayi sai aka kai maganar gaban Shaihu Usman Danfodiyo, shikuwa yaki zaben kowa a cikinsu. Sai ya tambayesu ko wanene yafi kowa Ilmi a kano? Sai suka ce masa wani ne da ake kiransa Sulaimanu, ba ma wadda ya san shi sosai, Da jin haka sai Shaihu Usmanu yayi masa Sarautar kano.

             ZUWAN TURAWA…..
Duk wadda ya karanta Tarihin Nigeria ta Arewa da yadda ta koma hannun Turawa, yaji labarin yadda Magajin Kafi ya kashe Razdan din da ake kira da suna Moloney, da yaga abinda yayi lalle zai janyo bubban Tashin hankali sai ya gudu yaje gaban Sarkinsa Sarkin Zazzau, kunsan da can kasar na cikin kasar Zazzau ne. a zamanin Gwamna Lugga ne akayi abin kafin ya zama Gwamna, sai Lugga yace Sarkin Zazzau ya bada Magajin Kafi ayi masa Shari’ah, amma Sarki yaki. Suka taru da Magajin Kafi suka gudu kano. Sai Gwamna Lugga da Sojojinsa suka bi zuwa kano, kano tace babu wata maganar a bada wadannan mutane sai dai ayi yaki. Gashi ma tana samun riba wajen sayar da Bayi, Turawa suna neman hanawa. Bugun farko anyi shi a cikin 1903 a Bebeji ta kasar kano, Turawa suka make Bebeji suka wuce zuwa Kano. Dama Birni a shirye yake an kulle duk kofofi, Dakaru kuma suna shirye, Amma Sarki da Magajin Kafi sun gudu sun nufi Sakkwato. Turawa suka daidaici  Ganuwa suka buga mata Igwa sai ta Rushe, suka shiga Birni. Da shigarsu sai aka waste fada yak are kowa ya kama gabansa. Kashegari kowa na ta harkarsa kamar ma babu abinda ya faru, in mutum yaje kasuwa sai ya iske mutane suna ta saye da sayarwarsu, babu abinda ya damesu. Amma nan da nan Turawa suka rufe kasuwar sayar da Bayi suka bude Kurkuku aka fidda wadanda suke ciki. Daga nan fa kano ta shiga sabuwar hanya ta ci gaba a cikin mulkin Turawa.

MADOGARA....
Razdan  C.R Niven
Muhammadan Emirate.
Assessment report by colonial Administration.