HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Sunday, June 17, 2012
JIYA BA YAU BA.
HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa da fatan Alkairi Ga 'yan wannan Masarauta, Muna kara godiya ga Allahu subhanahu-wata'ala da ya bamu ikon Rubuta wannan wasika. Domin da Ikonsa ne Komai ya kasance da kuma abinda zai kasance! Bayan haka Ina kira ga shugabannin Hadejia da su taimaka su Inganta mana Muhimman guraren Tarihinmu na kasar Hadejia. Sakamakon Lalacewa da suke kokarin yi. Kamar Tsohon Gidan yari, Gulbin Atafi da Ramin zaki, bariki wato Gidan Rasdan da na D.O., kabarin Captain H.H. Phillips wato Mai Tumbi, Kofar Kudu (chediyar kyalesu) da kuma kofar Gabas. Wani mutum yazo daga BIDDA ta jihar Niger yace min Yana so na kaishi Kabarin Captain phillips, sai nayi shiru Ina tunanin wanene captain phillips? Sai na tuna lokacin muna yara In munje kanya muna zuwa kabarin Mai tumbi. Kuma a jikin kabarin an rubuta captain H.H.phillips! Sai nace masa Muje ko da mukaje sai na fara Gabatar masa da Bariki cewa a nan Turawa suka fara zama. Sai yace dani A'a ai sun Zauna a can Gaba kafin suzo nan. Nace Eh hakane. Koda mukaje Kabarin Mai tumbi sai muka ga Ginin duk ya rushe kabarin yana nema ya bata. Sannan sai yayi kira ga Hukumomi su rinka kawata Guraren Tarihi Irin wadannan. To muma muna kira ga wadanda abin ya shafa da su Gyara guraren tarihi ba sai kabarin Mai tumbi kawai ba. Sannan yace In kaishi Fantai Inda Gidajen Sarakunan Habe suke. Ko da yake munje Amma bamu samu Dagacin Mandara a gida ba amma mun Dauki Hotunan Gidajen nasu da kuma Tsangayar Gwani Gambo a cikin 'Yankoli. Sannan Muka Zarce zuwa Mai-Rakumi mukayi Ziyara ga kabarin Sarkin Hadejia Sambo. Bayan mun dawo Mukayi sallama da Bako ya wuce Gogaram Ta Bade Yace daga nan Zaije har Ngazargamu. Nace Allah ya kiyaye hanya. Sannan sai na fara tunani Ashe tarihi yana da muhimmanci? Sai na tuna Ai malamin History yace:- History is the systematic Account of past and present Event. Zan baku Karashen Labarin anan Gaba. Hadejia A yau.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!