HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Sunday, July 15, 2012
TARIHIN ALH. DANJANI HADEJIA
HADEJIA A YAU! Tun Lokacinda nace zan rubuta tarihin Alh. Danjani Hadejia na samu kiraye kiraye a waya akan cewa ana sauraro na. To matsalar itace muna nan muna tattara Bayanai domin kar muyi garaje bamu kammala ba mu saki. Mai Karatu zaiga na rubuta Tarihin Alh. Danjani Hadejia, Wannan satin in Allah ya yarda zamu Maida Hankali wajen Tarihin Alh. Danjani Hadejia. Da irin gwagwarmaya da yayi. Alh. Danjani yana daya daga cikin Mutanen da suka Daga darajar masarautar Hadejia idan mukayi la'akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ganin Talaka yayi kyakkyawar rayuwa babu Tsangwama daga masu sarauta. Abinda yasa bazamu Rubuta duk tarihin ba sai mun samu Hotonsa wanda yayi da farar riga da bakin takalmi da kuma Jar hula. Hadejia a yau.
Monday, July 9, 2012
TARIHIN KAFUWAR HADEJIA KASHI NA (1)
TARIHIN KAFUWAR Hadejia Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, shi wannan maharbi ya taho ne daga yankin Machina ya yiwo yamma har yazo wannan wuri da yanzu ya zama Hadejia. Lokacin da yazo sai ya iske Daji mai bishiyoyi ga kuma Namun Daji da Tsuntsaye ta ko ina, sai ya zauna yaci gaba da farautarsa har saida wata rana yana tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo ko da tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi mamakin hakan har ma sai yabi sawunta. Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye suna shawagi a wurin. Sai ya yanke shawarar zama a wannan wurin, kuma hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa yake harbe harben Namun daji kuma yayi SU,wato kamun kifi.
In ya kashe namun daji sai yaje ya sayar da fatun. Harma ya dauko matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan wurin. Kuma mutane sai suke zuwa sayen fatu da nama a wurinsa. Duk wanda yazo wurin sai yayi sha'awar zama a wurin, haka nan gari ya fara bunkasa wasu maharba, wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada zango a garin. Kuma makwafta masu zuwa sayen Namun Daji sai suke kiran garin da suna Garin Haden-jia, wato suna masa lakabi da sunan matarsa.
To kasancewar gari sai da shugabanci ne yasa shi Hade ya zama shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu ko nama sai yace na tafi garin Haden jia.
Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. To sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia.
Kuma bayan zamanin wannan mutumin
Hadejia taci gaba da zama gari kuma tare da shugabanci wato mulkin Sarakunan Habawa. Kuma a lokacin akwai kananan Garuruwa masu wadda suke kusa da Hadejia kamar Rubban Dakata, Auyo, Hadagwaigwai da dai sauransu. Wadanda suma suna da nasu sarakunan a wannan Lokacin. Kuma Hadejia sunyi Sarakunan Habe guda talatin da biyu(32),amma sunan mutum uku ake dasu wadanda sukayi mulki kafin zuwan Fulani.
1, BAUDE
2,MUSA
3, ABUBAKAR.
A zamanin Mulkin Sarkin Hadejia na Habe Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin Hadejia tana karkashin Daular Borno, domin tana karbar Umarni ne daga Galadiman Borno. Sarkin Hadejia na Habe shi ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman Danfodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune suke sarautar Kasar Hadejia.
A GABA ZAN KAWO MUKU TARIHIN
SARAKUNAN FULANI DA DALILIN KARBAR TUTA DA YADDA SUKA TUNKUDE SARAKUNAN HABE DAGA SARAUTA.
Subscribe to:
Posts (Atom)