Budaddiyar wasika ga mai girma shugaban karamar shukumar Hadejia da yan majalissarsa.
Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, ina mai farin
cikin rubutoma wannan takardar domin in nuna irin
goyan baya da nake bawa wannan jam'iya da wannan gwabnatin mai albarka, bayan haka ina jinjinama bisa irin kokarin da kake wajen ciyarwa da
wannan karamar hukuma gaba. Ina sake jinjinama da yadda kake gudanarwa da mulkinka cikin
kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Bayan haka ina so nayi amfani da wannan damar na tunatar da kai wasu muhimman abubuwa
wanda idan kayi su zasu taimakama wajen samin sahihiyar
hanyar ci gaba da kuma adana tarihi ko bayan
ranka, wannan abun kuwa sune kamar haka.
Kasancewar garin hadejia babban gari ne mai tsohon tarihi a jeri garuruwan Hausa to ya kamata
ace yau akwai abubuwan da zamu yi alfari da su wajen tarihi kamar yadda ya'u idan kaje Daura zaka tarar da abubuwan da suka faru shekaru dari uku ko hudu
da suka shude kamar yau akayi su.
Ma'ana muma a garin Hadejia muna da irin guraren
nan kamar kabarin mai tumbi, kofar mandara, ruwan Atafi, Rijiyar turawa, mabuga, majema, marina, bariki da sauransu.
Kuma ya kamata ana tunawa da mutanan da suka bawa wannan gari gudunmawa misali saka
sunayensu a titinah,dakin taro makarantu dasauransu. mutane irinsu Alh Haruna uji ya kamata a
na tunawa dasu, amma abin al'ajabi aka saka sunayen mutane a titinah aka manta da Haruna
uji, wanda ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen daukaka masarautar hadejia.
Saboda haka a madadin daliban Hadejia emirate ina
mika wannan sakon ga maigirnma shugaban karamar hukuma da fatan za'a duba. Nagode.
Comrade Aji kima hadejia secretary general Hadejia student Association.