HADEJIA A YAU!
Daga Fatuhu Mustapha.
Sabbin Masarautun: Rano Gaya, Karaye da Tatsuniyar Bayajidda...
Daga Fatuhu Mustapha.
Dama dai mun san meye asalin garin Bichi, domin bawani jimawa yayi ba. Amma meye asalin kafuwar wadannan garuruwa da na lissafa a sama?
Akwai hanyoyi kusan hudu da zamu fahimci kafuwar wadannan garuruwa, sun hada da...... Tarikh Arbab Wato Kano Chronicle, Hausa Girgam, Wakar Bagauda da kuma kundin Waraƙa Maktuba fiha-asl al Wangariyun. Wadannan sune manyen kundayen da ake dogaro dasu akan tarihin kasar Kano.
Amma kafin nan, bari mu koma baya mu fahimci me ake nufi da kasa, mai kuma ake nufi da gari. Kasa dai kamar yadda zamu ce kasar Kano, kasar Katsina, Kasar Zazzau, Kasar Zamfara, na nufin wata nahiya dake zaman kanta, Wadda a turance ma iya cewa tana da Sovereign power ko kuma authority, da take gudanar da alamuranta ba tare da wani katsalandan na wata kasa ba. Acikin littafin Raudatul Afkar, na Malam Gidado Bin Mustapha (Malam Dantafa), ya bayyana wannan yanki namu da sunan Sudan ta Tsakiya, wanda ya banbanta su da Sudan Madaukakiya da kuma Sudan Makaskanciya. Kasashen Sudan a cewar malamin sun hada da: Borno, A'ir, daulolin dake sahara, Kano, Katsina, Gobir da Zazzau. Wadannan a cewarsa sune kasashen dake Sudan ta Tsakiya. Ba shi kadai ne ya ambata haka ba, shehin Malamin nan na Timbuktu wato Ahmad Babq al Timbukti a wata amsa da ya aikewa wani almajirinsa dake zaune a kasar Masar wato Ibrahim al Isi, wacce ya kira da Al Kashf wal Bayn fi hukm mujallab al Suud, ya bayyana cewa " amma kasashen Hausa sune: Kano, Katsina, Zazzau, Gobir da kuma Borno " in banda Borno da ya sanya aciki, dukkan wadannan kasashe, an tabbatar da Dauloli ne masu zaman kansu a kasar Hausa. Duk wata Daula da kaji to daga baya ne.
- Kafuwar Daulolin Tsakiyar Sudan
Mafi dadewa a iya saninmu sune Daular Tumbi da Washa, wanda a yanzu Tumbi wani kauye ne a kasar Gumel, yayin da Washa ke kasar Damagaram. Wadannan dauloli sunyi karfi kwarai a wasu lokuta masu tsaho, sai dai bawani cikakken nazari a kansu, dalilin kafuwarsu, karfinsu da kuma dalilin rushewarsu. Amma dai mun san tun shekara sama da dubu, dakarunsu kan kai hari zuwa Kano da Katsina da Zaria.
Kasar Kano da Asalin Mulkinta
Shaidu na tarihi sun tabbatar da cewar kasar Kano ta samo asali ne, tun kusan fiye da shekaru 3000 da suka gabata, bayan da wasu kabilu da ake kira maguzawa (Majusawa: kamar yadda Murray Last ya bayyana asalin sunan), Wanda ake zaton sun taso ne daga tsibirin Dahlak na kasar Ethiopia wato Habasha. Wannan kabila sun zo nan kasar Kano karkashin jagorancin wani babban limamin addininsu maisuna Dala, da kuma wasu yanuwansa guda uku: Kanau, Ranau da kuma Gayya.
Wadannan mutane ba yan siyasa bane tun farko, hankalinsu yafi tafiya wurin yada addininsu na Maguzanci, daga sune aka samu firqoqi ko dariqu irinsu Gwandarawa dake jihar Nasarawa a yau, Arna da a yanzu kusan duk sun koma Kirista, da Domawa dake kasar Kazaure da Kismawa dake Dambatta da sauransu.
Sun kafa wurin bautarsu a kan dutsen Dala dake cikin garin Kano Wanda suka kira Kakuwa, inda Suke bautar wani aljani da suke kira da Tsumburbura, Danko, ko Shamus, Wanda Malam Adamu Na Maaji yace shine Yaquqa da ake bautawa tun zamanin Annabi Nuhu acikin littafinsa: Iilan bi Tarikh Kano. Wasu kuma yanki suka kafa nasu bautar a Bakin Ruwa, inda suke bautar Ruwan Jakara (sai dai wadannan ana ganin ba Maguzawa bane, asalinsu Abagayawa ne). Akwai kuma wasu masu bautar bishiya wata Tsamiya da ake kiransu da Gazargawa, wadanda ke zaune a Madatai. Da Gwandarawa dake bautar farji a dutsen Bompai da sauransu.
A wannan lokacin garin Kano ba komai acikinsa in banda wuraren bauta, a saboda haka baa noma kasar, ko ayi farauta, ko yaki ko a haki maadananta. Wannan babban laifi ne ga addinansu. A wannan hali bukatar siyasa da ta tattalin arziki ta taso, Wanda ya sanya, bayan rasuwar Dala, wasu daga cikin kannensa suka ga bukatar lallai su nemawa kansu da mutanensu mafita. A saboda haka suka fara tarwatsewa daga Kano. Ranau da yake zaune a Kusurwa (nan inda gidan Galadiman Kano yake a yanzu wato gidan Wambai) ya tashi ya koma wani wuri da ake kira Zamna Gaba (wato Rano a yau) ya kafa gari. Gayya ma ya tashi ya koma ya kafa garin Gaya. A ka bar Kanau a matsayin babban limamin addininsu a Kano. Amma duk da wannan suna tare da cibiyarsu ta addini dake Dala. Babu wata shaida da ta nuna, wadannan garuruwa sun kafa wata kasa tasu mai zaman kanta.
Bagaudawa da Sabon Canji
Asalin Bagaudawa dai Hausawa ne dake zaune a yankunan kasar Bauchi. Akwai masu raayin kalmar Bauchi na nufin Bahaushe. A wani kaulin kuma ana zaton tana nufin 'Bawa'. A wani rangadi da Firauna Hausal ya fito, a jirgin ruwa, an bayyana cewa ya fado ta tafkin Chadi, ya biyo ta kogin Jakara, ta Hadeja Jamaare, ya shiga kasar Bauchi (Baushe)inda ya iske mutane, daga nan ya bi ta kogin Binuwai ya je har Bargu (Barku), ya bi ta kogin Kwara ya fada zuwa Tekun Atlanta ya koma gida.....
(Zamu cigaba inda zamu ji alakar Bagauda da Daura, da karairayin tatsuniyar Bayajidda) insha Allah.....