Hadejia A yau!
DAGA MUHAMMAD IDRIS HADEJIA
Shirin Taurarinmu zai Rinka tabo takaicaccen Tarihin Mutanen Kasar Hadejia da Irin ci gaban da suka bata, Domin kaima ka bada taka Gudunmawa. Kuma zamu fara da takaicaccan Tarihin.......
ALHAJI HAMZA TURABU ***************
Alhaji Hamza Turabu. Bahadeje mazaunin kano. Alhaji Hamza tsohon ma'aikaci ne a Hukumar Aikin Gona ta Jiha. Yana rike da
mukamin Director Forestry tun muna kano har muka zo jigawa kuma akansa ya bar aiki.
Dattijo ya yi wa mutane da yawa hanyar samun aiki musamman a Ma'aikatar Aikin
Gona kuma shi ne ya assasa filantaishin masu yawa da muke gani a yau fadin kano da
jigawa.
Alhaji Hamza mutum ne mai son ya ga matasa sun yi karatu shi ya sa gidansa ya zama mazaunin Dalibai 'yan wannan masarauta har a yau. Hadejawa suna ma
addu'a Allah ya albarkanci zuriyarka. Amin.
SHEIKH MUHAMMAD LAMIN KHAN (MALAM MODIBO YALLEMAN) ****************
Marigayi Sheikh Muhammad Lamin Khan yana daya daga cikin dattijon 'Yalleman, daya daga
cikin malaman addini na wannan
masarauta, shine bubban Limamin
'Yalleman.
Malam Modibo ya zaga kasashen
Afirka da dama akan neman ilmin addini kuma ya same shi domin ya karantu a bangarori na addini dabam-dabam. Ana zuwa
har daga garuruwan makwabta a dauki karatu a wurinsa.
Bayan kasancewar gidansa makaranta ce shi ne ya assasa Makarantar firamare ta Madani da kuma Sakandiren Madani. Matasa da yawa cikin garuruwan
'Yalleman, Dakayyawa, Hadiyin, Ubba, da kewaye a wannan makaranta suke karatu. Malam Modibo ya hada duk wani hali
na dattako da ake so,don haka yake da girma a idon jama'a a ciki da wajen wannan masarauta.
Muna addu'a Allah ya sa kur'ani ya
cece shi. Amin.
HAJIYA LAMI AMINU KANI ***************
Hajiya Lami Aminu Kani 'ya ce a wurin Sarkin Fulanin Hadejia Alhaji Daudu Saleh. kuma matar
na hannun daman AVM Hamza Abdullahi, wato Alhaji Aminu Kani. Hajiya Lami tana daya daga
cikin tsofin 'yan boko mata na wannan masarauta.
Hajiya Lami babbar ma'aikaciya ce
a hukumar bayar da wuta "PHCN" Kuma zamanta a wannan wuri ya amfanar da wannan masarauta matuka domin idan ka
kasa masu aiki a PHCN na wannan masarauta kashi dari Hajiya Lami ce ta kai kashi saba'in daga cikinsu PHCN. Mace mai kamar maza.
Hadejawa sun baki Sarkin Fulanin
Mata. Muna addu'a Allah ya kara daukaka. Amin.
HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Monday, March 18, 2013
Saturday, March 16, 2013
SAKO ZUWA GA MASU AMFANI DA FACEBOOK.
Hadejia A yau!Shafukan INTERNET da Wayar Hannu ta GSM....Bincike ya nuna cewa shafin internet na FACEBOOK da wayar hannu ta GSM suna daga cikin ababen dake kara rura wutar fadan addini a Nigeria.
Hakan yana faruwa sakamakon irin yadda mutane ke amfani da su wajen isar da sako atsakaninsu. Mutanen mu suna da son bayar da labari,Inma ingantacce ko mara inganci don neman addu'ar 'yan uwansu ko don nuna bajintar su ko kuma don wata manufa ta su ta daban.
Wannan yasa dayawa sukan fadi abinda basu da tabbas akansa, ko kuma suyi kari cikin labarin na su.
Ya kai dan'uwana mai son bayarda labari! Kaji tsoron Allah, kada kafadi, ko kada karubuta sai abin da kaji ko kagani kokuma kake da tabbas akansa. kasani za ka amsa tamyar Allah akan abinda kake fadi kokuma kake rubutawa a duniya (facebook), wacce amsa ka tanada?
Ba wani abin birgewa bane afara jin labarin dake tayar da hankali agurinka. Addinin muslunci ya hore mu da yin magana ba tare da ILIMI ba. Mu kiyaye ko Allah (S.W.A) ya kiyaye mu.
Ya Allah! Kakiyaye mu, kabamu zaman lafiya, Amin.
Haka kuma a Facebook zakaga GROUP ko PAGE wadanda basu da Aiki sai watsa Labarin karya. Misali sai a saka Hoton Yarinyar da bata jiba bata Gani ba wai Ace tace tana neman Miji. Wanda kuma Addinin Musulunci bai yarda da hakan ba.
Kuma 'yan mata kuji tsoron Allah duk abinda ya sameku kuke Janyowa kanku. Domin kune kuke yawan sauya Hoto dan ku Birge mutane!
A garin hakan kuma sai a samu wasu bata gari suyi downloading din hoton su dinga Talla daku.
Ko kuma Namiji ya Bude 2go da sunan mace yasa hoton wadda bata jiba bata gani ba. Wai dan ya yaudari 'yan Iska 'yan'uwansa. Allah ya kiyaye mu.
To Jama'a sai mu kula da fadar jita jita, domin karya haramun ce. Allah ya kare mu amin....
Subscribe to:
Posts (Atom)