HADEJIA A YAU!
SARKIN HADEJIA UMARU: A SHEKARAR 1863 allah ya yiwa Sarkin Hadejia Buhari rasuwa a Yakinsu da sukayi da Gogaram (bade). Ko da aka dawo Hadejia aka binne shi sai Manyan fadawan Hadejia wadanda akwai Amana tsakaninsu dashi Buhari. Kamar SARKIN AREWA TATA GANA (GINSAU MAI KINA BAWO) DA KUMA SARKIN YAKI JAJI suka jajirce Sai an Nada UMARU DAN BUHARI SARKIN HADEJIA. kuma hakan Akayi!
SARKIN HADEJIA UMARU NA BIYU an nadashi yana da shekara Goma sha Hudu. Kuma manyan fadawan Mahaifinsa sune suke gudanar da Sarautar tunda shi yaro ne. Kuma a zamaninsa Sarkin Damagaram Tanimu ya kawo yaki Hadejia. Kuma yayi sansani a Arewa da Hadejia daga nan har Jigawar Kasim mutanensa ne. saida yayi kwana Arba'in ana yaki amma Hadejiawa basu fasa wasanninsu na dandali ba. Wata rana ana yaki Sai aka harbi dokin Sarkin Arewa! Koda ya mutu sai akaje gida aka dauko wani Dokin aka cire kayan wancan Dokin aka sakawa wanda aka kawo. Tata gana ya koma kan doki, kashe gari ana cikin yaki sai Tata gana ya sauko daga Dokinsa yayi alwala ya koma kan Dokin, to ashe Sarkin Damagaram yana kallon su sai yace Lalle Sarkin Hadejia ya Isa ana yaki ka sauko kayi alwala? Jiya ma an kashe masa Doki amma saida akaje aka dauko wani a gari? Sai Zagin Sarkin Damagaram yace ai ba Sarkin Hadejia bane Yaronsa ne! Sai Sarkin Damagaram Tanimu yace to Ina Sarkin Hadejian? Sai zaginsa yace ai ance yana gida tunda aka fara yakin nan bai taba zuwa ba. Sai sarkin Damagarm yace wa fadawansa Gobe zamu bar Hadejia kar mu tsaya ayi ta kashemu. Saboda Sarkin Hadejia ya raina mu kwananmu Arba'in amma bai taba zuwa anyi yaki dashi ba? Wa yasan me zai mana in ya zo? Amma basu san Sarkin Yaro bane. Washe gari suka juya suka koma Damagaram. Kuma lokacinda sukazo Hadejia Da kaka ne! Anyi girbi Manoma basu gama Tare Amfaninsu ba. Shi yasa suka dade a Hadejia saboda akwai abinci da ruwa a kusa dasu. SARKIN HADEJIA UMARU Mutum ne mai son Nishadi kowane Lokaci yakan fita Bakin kogi ko Gona Domin Debe kewa. Kuma anyi amfani da wannan Damar inda wata rana ya fita sai aka Rufe Masa Kofa. Koda yazo yaga kofa A rufe sai ya juya ya tafi Chamo ya zauna. Aka nada Kanin Mahaifinsa Sarkin Hadejia Wato HARU BUBBA. 1865-1885. Shi kuwa UMARU DAN BUHARI yayi zamansa a Chamo kuma Ya rasu a shekarar 1920. Allah yaji Kansu Ameen.
HADEJIA A YAU.
HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau.
Tuesday, March 27, 2012
TARIHIN SARKIN HADEJIA UMARU DAN BUHARI 1863-1865:
All
Full
Saturday, March 24, 2012
HADEJIA A YAU!: SUNAYEN SARAKUNAN HADEJIA TUN DAGA HABE RULER'S ZUWA YAU.
SUNAYEN SARAKUNAN HADEJIA TUN DAGA HABE RULER'S ZUWA YAU.
HADEJIA A YAU!
Kamar yanda na baku labari a baya Hadejia anyi sarakunan Habe tun kafin zuwan fulani. A shekarar 11000 aka fara Mulki a Biram wato Garun Gabas, kuma a shekarar 1805 fulani suka fara mulkin Hadejia. Ga sunayen sarakunan Tun daga shekarar 1700 zuwa yau wato 20012.
1, 1700, KANKARAU
2, ASAWA
3, MAMMAN BAKO
4, KAWU
5, BAUDE
6. MUSA
7, 1805 ABUBAKAR
Wadannan sune wasu daga cikin Sarakunan Habe na Hadejia.
A Lokacin sarkin Hadejia na Habe Wato Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, a karkashin jagorancin Ardo Abdure dan Jamdoji, kuma Sarkin Habe Abubakar shine ya basu wurin zama, kuma zamanin Sarkin fulani Sambo suka dawo Inda fadar Hadejia take yanzu. Kafin su kwaci mulki a Hannun sarakunan Habe.
Sarakunan fulani sun karbi Mulkin Hadejia tun daga shekarar 1808 har zuwa yau. Ga jerin sarakunan Fulani..
SARAKUNAN FULANI
1, 1805-1808 UMARU DAN ARDO ABDURE
2, 1808-1808 MAMMAN KANKIYA DAN UMARU.
3,1808-1845 SAMBO DAN ARDO ABDURE. 1st.time.
4, 1845-1847 GARKO GAMBO DAN SAMBO.
5, 1847-1848 ABDULKADIR DAN SAMBO.
6, SAMBO DAN ARDO ABDURE 1848 2nd time.
7, 1848-1850 BUHARI DAN SAMBO. 1st time.
8, 1850-1851 AHMADU DAN SAMBO
9, 1851-1863 BUHARI DAN SAMBO 2nd time.
10, 1863-1865 UMARU DAN BUHARI.
11, 1865-1885 HARU BUBBA DAN SAMBO.
12, 1885-1906April MUHAMMADU MAI SHAHADA DAN HARU BUBBA.
13, 1906-1909 HARU MAI KARAMBA DAN MUHAMMADU.
14, 1909-1925 ABDULKADIR DAN HARU MAI KARAMBA.
15, 1925-1950 USMAN DAN HARU MAI KARAMBA.
16, 1950-1985 june HARUNA DAN ABDULKADIR.
17, 1985-2002 sept. ABUBAKAR MAJE DAN HARUNA.
18, 14 sept. To date. ADAMU DAN ABUBAKAR MAJE.
A RANAR 14 SEPTEMBER 2012 MAI MARTABA SARKIN HADEJIA ALH. ADAMU ABUBAKAR MAJE (C.O.N) ZAI CIKA SHEKARA GOMA (10) YANA MULKIN KASAR HADEJIA.

Thursday, March 22, 2012
HADEJIA A YAU!: TARIHIN HADEJIA A TAKAICE!
HADEJIA A YAU!: TARIHIN HADEJIA A TAKAICE!: HADEJIA- TARIHIN KAFUWAR Hadejia Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, a yawon farauta da yakeyi ne wata rana yana tafe da karyar sa sa...
Subscribe to:
Posts (Atom)