Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, February 19, 2016

TARIHIN HADEJIA.



Takaitaccen Tarihin masarautar Hadejia.


Masarautar Hadejia dadaddiyar Masarauta ce wadda ta kafu shekaru aru aru da suka gabata, daga lokacin kafuwarta kawo yanzu masarautar tayi fice da yin suna bisa ga muhimman tarihi da take dashi. Masarautar Hadejia tana daga cikin masarautu da sarakunan HABE suka mulka kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, kuma tana daga cikin masarautun da ake kira Hausa Bakwai. Masarautar tana daga cikin Masarautu da suke karkashin Daular Usmaniyya, daga Gabas tayi iyaka da Tsohuwar Daular Borno daga yamma tayi iyaka da Masarautar Kano, daga Kudu kuma tayi iyaka da Masarautar Katagum sannan daga Arewa tayi iyaka da Masarautar Gumel. Birnin masarautar yana cikin garin Hadejia dake Arewa maso gabashin Jigawa a Arewacin Nigeria, sunan garin ya samo asali ne daga wani Maharbi wadda shine ya kafa garin wato HADE, da kuma Matarsa JIA. Sunayen wadannan mutane shi aka hada ya zama HADEJIA, domin a lokacin mutanen wasu garuruwa in zasu zo sukan ce mun tafi garin Haden jiya, wato ana masa Lakabi da sunan Matarsa. Saboda takaita kalma ta Hausawa shine yasa aka hade sunan ya zama Hadejia. 

Masarautar Hadejia tana da fadin kasa wadda ta kai Murabba’in kilo mita dubu shida da dari tara da sittin da uku(6963), wannan yanki yana da shimfidaddiyar kasa mai kyau wadda ake kwatanta yanayinta da na kasar Chadi, kuma tana da Jigayi masu tarin yashi da kuma kwari mai tabo da laka amma bada da tsaunuka ko Duwatsu. Kasar Hadejia tana da Kogi wadda ya kasance akwai ruwa kowane lokaci, sannan tana da fadamu masu yawa wadanda suke kafewa lokaci zuwa lokaci.

Kogin kasar Hadejia ya taso ne daga Kudancin Katsina ta Arewa da Zaria sannan ya nufi Arewa maso gabas ya shigo ta Kasar Kano ya ratsa kasar Hadejia, sannan ya nufi Tafkin Chadi. Wannan Kogi ya ratsa ne ta Kudancin Hadejia da Gabashinta, wannan bangare ne da yake samarda ruwan sha da kamun kifi da kuma aiwatar da Noman rani. A lokacin damina kogin yakan cika inda yake samarda kananan fadamu a sassa daban daban wadda ake amfani dasu a wajen noman lambu. A bangaren Noma Masarautar Hadejia tana gabatarda noma a lokuta biyu wato Rani da Damina, inda masana yanayin kasa suka tabbatar cewa duk abinda aka shuka a wannan kasar zai fito yayi kyau saboda yanayin kyawun kasar. 

A bangaren kasuwanci kasar Hadejia ta shahara wajen saye da sayarwa tun kafin Jihadi, domin ta zama wata mahadar kasuwanci ce tsakanin Daular sokoto da Daular Borno. Mutanen Masarautar suna da sana’oinsu da dama kama daga sana’ar hannu zuwa Fatauchi da sauransu. Kasar Hadejia tana da kasuwanni da yawa wadanda suke ci a dukkanin sati sannan da masu ci a kowacce rana.

Masarautar Hadejia tana da Kabilu da yawa wadanda suke yarensu da Al’adunsu sun banbanta kuma suna zaune a yankuna daban daban na kasar, Kabilun kuwa sun kunshi Hausawa, Fulani, mangawa, Ngizmawa, koyamawa, Baddawa, da sauransu. Wadannan Kabilu kowanne da irin yarensa da kuma Al’adarsa da irin tsarin zamantakewarsu, sai dai duka suna bin Tafarkin Addinin Musulunci ne tun bayan Jihadin Shehu Usman Danfodiyo.

posted from Bloggeroid

Tuesday, October 6, 2015

KO KUN SAN?........

KO KUN SAN?.....
A shekarar 1971 anyi wata gagarumar yunwa da fari wanda aka sawa suna KWAKWUDUBA, a wannan lokacin hatta fadamu da koguna duk sun kafe babu ruwa, kuma abinci yayi karanci ga mutane. Hakan tasa mutanenmu musamman wadanda garuruwansu yake kusa da Kogi (Masunta) sukayi Kaura daga garuruwansu suka nufi Gabas. Wasu sun wuce har Chadi wasu kuma suka shiga har Kamaru, yayinda wasunsu suka tsaya a garin Baga.

Koda yake a lokacin wannsn garin da ake Kira Doran Baga mutanenmu ne suka je suka kafa Daba a kusa da gabar Kogi. Anan ne sukaci gaba da zamansu suna Kamun Kifi da sauran Albarkatun ruwa sannan su sarrafa su kawo Maiduguri da wasu sassa na jihar Yobe su sayar. Haka gari yaci gaba da girma sakamakon zuwan mutane Masunta domin su samu abinda zasuci da Iyalensu. Sakamakon gari ya zama gari har sai ake kiran Dabar tasu DORON BAGA.

Akasarin mutanen da suka tafi daga kasar Hadejia mutanen Kafinhausa ne da kuma yankunan Kirikasamma da Guri, idan ka lissafa wancan lokacin zuwa yau zai baka shekara 44. Wadannan mutanen wasunsu sun bar garuruwansu ba tare da suna dawowa suna gaida Iyayensu ba, wasunsu kuma har iyayen nasu suka bar Duniya basuzo sun gansu ba,wasu a cikinsu sun manta yanda yanayin garinsu ma yake saboda sun samu Duniya acan. Da yake ba duk aka taru aka zama daya ba wasu sukan zo su gaida 'yan-uwansu da abokan Arziki sannan su koma tunda Allah yayi zamansu acan.

RIKICIN BOKO HARAM....
A cikin Shekarar 2008/2009 Rikicin Boko Haram ya faru a Gabashin Nigeria, musamman yankunan Jihar Borno da Yobe da wasu sassa na Adamawa da Bauchi da Gombe, wanban rikici yayi Asarar Rayuka da Dukiyoyi masu dinbin yawa, inda akayi ta kone Gidaje da Kasuwanni da wuraren Sana'a. Wannan ne yasa wadancan mutane da na Ambata a sama wadanda Kwakuduba tasa suka bar garuruwansu sai suka fara tunanin su dawo gida, sakamakon fadin Hausawa " Giji Lahira ce" anan ne fa suka fara dawowa ba tare da abinda suka tara a can ba, wasu sun dawo gida sun tarar duk wadanda suka sani sun mutu wasu kuma tsufa ya kama su.

TAKAITACCEN TARIHIN RAYUWAR CHIROMAN HADEJIA. ALH. AMINU HARUNA

Daga Muhammad Yawale....
.

text-align: center;">

Bismillahirrahmanir-rahim.
An haifi Alh Muhammadu Aminu Haruna a garin Guri a shekara ta 1943, A lokacin mahaifinsa Alhaji Haruna Abdulkadir yana Chiroman Hadejia Hakimin Gundumar Guri. Ya halarci makarantar kur'ani wato allo a garin Guri makarantar sule Gangaran a 1952-1956, ya halarci makarantar Elementary primary Dallah a cikin garin Hadejia a 1953-1956, ya halarci makarantar middle school ta fantai hadejia a 1957-1960, sannan ya halarci makarantar horarda malamai ta Bichi a shekara ta 1960-1962.
Marigayi ciroman Hadejia yayi karatu a potiskum (s.t.c sage 1) a 1970 yayi karatu a kaduna polytechnic (stage2-3) a 1971-1974 yayi karatun higher diploma a zaria Insitute of Administration (A.B.U) a 1979-1980. Ya halarci tarurruka na karawa juna sani a wurare daban daban na kasarnan.

AYYUKAN DA YAYI:
Yayi malamin makaranta a lokacin (N.A) ta Hadejia na tsawon shekaru 2, a karkashin tsohon Head master marigayi Alh Abdu maigari Tafidan Hadejia, yayi malamin makaranta a primary ta dubantu a 1965, yayi sakataren karamin minista na MADAKIN Hadejia Muhammadu Gauyama, a ma'aikatar tsaro ta kasa a lagos bangaren jiragen sama (Air-force) a shekarar 1965-1966,
Yayi malami a kotun babban alkali lokacin alkali Dahiru. A shekarar 1966-1968, yayi malamin Turakin Hadejia lokacin Turaki Adamu, yayi Akawu a ma'aikatar mulki ta (N.A), yayi sakataren karamar hukuma a wadannan wurare Bichi, ringim, gumel, wudil, babura, gezawa, kafin hausa, dawakin tofa yayi sakatare na musamman a karamar hukumar birni da kewaye (kano municipal council).

Ya rike mukamin DPM a kananan hukumomin garki, malam madori, Taura a inda yayi ritaya. Marigayi Sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje Haruna ya nadashi Tafidan Hadejia Dan majalisar sarki a shekara ta 1994, cikin yardar Allah kuma Sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar ya nadashi Chiroman hadejia a ranar asabar 13 ga watam march 2004 a inda ya gaji yayansa chiroman Hadejia Alh. muhammad Abbas.

Marigayi chiroman Hadejia mutum ne mai jajircewa kan gaskiya da rikon amana akan harkar da aka dorashi kuma ya nemawa mutane da dama aiki a lokacin gwamnati kuma duk abinda ya gani ba daidai ba baya yin shiru sai yayi magana hakazalika bai yarda kayimasa zancen waniba. Marigayi chiroman Hadejia ya rasu ranar juma'a da daddare 03/10/2015 bayan ya sha fama da jinya muna rokon Allah ya jikansa ya kuma kyautata bayansa.

Thursday, May 14, 2015

YAN GUDUN HIJIRA...



YAN GUDUN HIJIRA!
Tun a lokacin da rikicin Boko Haram ya Addabi jihohin Borno da Yobe aka samu watsuwar 'yan gudun hijira a wasu sassa na Nigeria, ciki harda jihar Jigawa, kuma akasarin wadannan 'yan gudun hijira zakaga Mata ne da kankanan yara wadanda mafiya yawa suna a kasar Hadejia da kasar Gumel. A lokacin da suka fara zuwa wadannan yankuna saboda basu da abinda zasuyi dole wasu daga cikinsu suke bin masallatai da majlissai domin neman abinda zasuci abinci da yaransu. Abin tausayi zakaga yara da basu fi shekara 7 zuwa 10 ba suna bi kantuna da wurin zaman jama'a suna neman taimako, a kwanakin baya basuyi yawan da ya wuce kaga biyu ko uku ba a kullum amma yanzu abin sai karuwa yake wanda a kalla sai kaga goma zuwa sama a rana daya da mata da kananan yara abin tausayi. zaka gansu a kofar masallatai da kasuwa har da Bankuna wurin layin Atm. Dole mumini mai Imani ya tausayawa rayuwar wadannan bayin Allah domin ba a son ransu suka bar gidajensu da 'yan uwansu suka zo suke yin Bara ba! Saboda yawan kwararowarsu yasa jama'a sun fara kosawa ganin abin ya zama ba na kare ba, yanzu kullum a baka gansu a gidanka ba kaga biyar ko shida.

MASU HANNU DA SHUNI....

Hakika Masu hali sai sunyi amfani da damar da Allah ya basu wajen taimakon wadannnan bayin Allah da muhalli da Sutura da Abinci, da kuma kula da rayuwarsu musamman kananan yaran. yana da kyau masu hali su ware wani abu daga cikin Dukiyarsu don taimakon wadannan bayin Allah a matsayin Sadakatul-jariya.

GWAMNATI MAI JIRAN GADO...

Koda yake bani da masaniya game da yunkurin da Gwamnatin Jigawa tayi game da wadannan bayin Allah, kuma ban taba ganin wani wuri da aka ware don 'yan gudun hijira ba zanso in bada shawara ga Gwamnati mai jiran Gado, A karkashin mulkin ko jagorancin Jam'iyyar Apc, dasu fara duba wannan Matsalar ta 'yan Gudun Hijira kafin su fara Aiwatar da kowane Aiki domin ceto rayuwar wadannan Mata da kananan yara daga yin Bara, wanda hakan ya fara jefa wasu daga cikinsu zuwa ga halaka. An fara samun rade radin wadannan mata 'yan gudun hijira sun fara yin Arangama da wasu gurbatattun mutane suna yin lalata dasu suna basu kudi, har ma ance wasu da yawa sunyi cikin shege Allah ya kiyaye! Abin takaici sai kaga idan 'yan Hisbah suka kama mace tana lalata in suka bincika sai kaga 'yar gudun hijira ce. Kasan Dalilin da yasata cikin wannan hali?

SHAWARA GA GWAMNATI....

Ina bada shawara ga Gwamnati mai jiran gado da suyi la'akari da wannan matsalar domin su san ta yadda zasu bullowa wannan Al'amari, ya kamata Gwamnati ta samar musu mahalli na wucin gadi sannan ta sanya yaransu a Makaranta don ceto rayuwarsu. kuma Ina baiwa Gwamnati Shawara da ta sama musu sana'oi domin su dogara da kansu. misali Gwamnati zata iya amfani da makarantar koyon sana'a don koyawa Matan yanda ake yin SABULU, SAKA, DINKI,Da sauransu. Daga karshe ina Rokon Allah da kar ya nuna mana makamanciyar wannan Bala'i da zai sa mutum ya bar gidansa da iyalinsa ya tafi wani wuri yana yin abinda ko a Addini yana daga cikin Abu mai Kaskanci. Allah ka zaunar da kasarmu da Jiharmu lafiya.

Ismaila A Sabo Hadejia.
13/may/2015.

posted from Bloggeroid