"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, January 4, 2019

AVM. HAMZA ABDULLAHI..

HADEJIA A YAU!

Air Vice Marshal (retired) Hamza Abdullahi (2 March 1945-3 January 2019.
Hamza Abdullahi was born in Hadejia in Jigawa State, on 2 March 1945. He attended the Nigeria Air Force Tactical Training Wing, Kaduna in 1964. He completed the Aircraft Technical Officer’s Course in West Germany (1964–1966), and studied at the Royal Military Training Centre in Chichester, England in 1974. In July 1975, Lt. Colonel Abdullahi was air provost marshal and assisted in the coup that removed General Yakubu Gowon from power, replacing him with General Murtala Mohammed.

Hamza Abdullahi was appointed the Governor of Kano State in January 1984, he announced in January 1985 that his government was revitalizing the Expanded Program on Immunization, targeting children and pregnant women at risk from preventable diseases. As Minister of Federal Capital Territory from 1986 to 1989, Abdullahi oversaw the construction of Phase 1 of Abuja. His goal was to have 75% of the ministries in Abuja by 1990, the target date for the official transfer of the capital from Lagos. He described the new city as "a symbol of our unity". Abdullahi was promoted air vice-marshal in October 1988 and retired from the Nigerian Air Force two months later. He dead 3/1/2019. May his gentle soul rest in Jannatul firdaus. 

Sunday, November 11, 2018

MATASA A FAGEN SIYASA.....

HADEJIA A YAU!



1. MATASA A FAGEN SIYASA.  
Da farko zamu dubi kalmar matasa ko matashi, me ake nufi da matasa?
Matasa ko matashi wata kalma ce ta Hausa wadda ake kiran wasu mutane da ita, (Mai Tashe) ana nufin wadanda shekarunsu ya fara daga goma sha takwas  18, zuwa shekara Arba’in 40. Domin ko a musulunci matasa su aka fi bukatar su bada gudunmawarsu don ci gaban al’umma, sannan matasa sune suke shirya duk wani tsari mai inganci na zaman rayuwa wadda idan sun gyaru hakika al’umma ta gyaru.

Matasa a fagen siyasa suna da muhimmiyar gudunmawa da zasu taka domin dorewar Demokradiyya, duk wata gwamnati  bata zama ingancacciyar gwamnati saida matasa. tarihin siyasar duniya  ya nuna matasa sune kan gaba wajen juya akalar rayuwar al’umma, domin sune masu zabe kuma daga cikinsu ake zaba. Babu wata siyasa da zata ci gaba ba tare da matasa ba, kuma matasa zasu iya tsare mutuncinsu a siyasa ba tare da anyi amfani dasu an gurbata siyasa ba. Tun lokacin NPC ta Sardauna da NEPU ta Aminu Kano aka baiwa matasa dama wajen tsayawa takara a kujeru daban daban don inganta rayuwar Al’umma, misali duk dan takarar da ya tsaya takara a lokacin Npc da Nepu babu wadda shekarunsa suka wuce 40, duk daga 35 ne zuwa 37. Haka akayi har zuwa zamanin NPN da PRP Idan ka debe shekarun Shehu Shagari daga lokacin da yayi mulki zuwa yau zaka gane lalle yayi Shugabancin Nigeria ne yana Matashi, Haka Gwamnonin zamaninsa irin su Rimi da sauransu har zuwa Senatoci da ‘yan majalissun Tarayya da na jihohi. Tun daga wancan lokacin zuwa yau matasa ne suke jan akalar Siyasar Nigeria, dukda cewa ana samun tsarmi da yawa da mutanen da muke kira Dattijai. Idan muka dubi lokacin Gwamnatin Saminu zamu ga yayi gwamna ne shekarun sa basu kai Arba’in ba, haka Mataimakin sa Barrister Ibrahim Hadejia ya zama Deputy Governor yana da Shekara 37 zuwa 38. Wannan yana nuna mana cewa Matasa sune dai a fagen Siyasar Nigeria, amma yanzu abin haka yake kuwa? Wadannan mutane da na saka hoton su wato Mustapha Sule Lamido, Ahmed Bello, Hussaini Rally, Barr. Mallam Abubakar Jallo, sune suka fanshi Matasa a fagen Siyasar wannan lokaci, kuma sune zasu zama fitila ga sauran matasan mu zuwa nan gaba, domin sun kasance sun karfafawa matasa Gwuiwa wajen damawa dasu a fagen Siyasa.

MECECE SIYASA?
Ma’anar siyasa itace tsara rayuwa ko samar da shugabanci da duk abinda yake ta’allake dashi, kamar tsarin zabubbuka, yin doka, umarni da hani. Tsarin horo ga wanda ya karya doka, kira ga hukuma da tayi ko ta bar wani abu.

Haka kuma kalmar siyasa kalma ce ta larabci aka arota zuwa harshen Hausa, ita kalmar siyasa ta samo asali ne daga ‘SASA’ ko ‘SULASI’. Kaga kenan wannan kalma ta “SIYASA” tana nufin Jagoranci, hikima, kiwo, horarwa da gudanarwa. Haka kuma ana amfani da siyasa yayinda wani abu na son zuciya ya shiga, amma wannan ba shine ainihin  kalmar ba. Ilmi yana da matsayi mai girma a tsarin siyasar kowace Al’umma. Daga kaarshe ina Addu’ar samun Nasara ga Matasa da suka tsaya Takara a kujeru daban daban, Allah ya tabbatar mana da Alkairi a Nigeria baki daya.

Matsayin Ilmi a siyasar Turai... masu ilmin falsafar Turai sunyi  ijma’i  game da muhimmancin Ilmi a siyasa. Plato yana ganin masu ilmi ne kadai suka cancanci su shugabanci jama’a, yayinda shi kuma  Aristotle yace A’a idan ana son siyasa ta inganta sai a baiwa jama’a  Ilmi. Shi kuma Spinoza cewa yayi amfanin siyasa shine ‘yanta Dan-adam da samar masa da Adalci, wannan kuwa bazai samu ba sai an bashi Ilmi. Shi kuwa Emanuel kant yana ganin rayuwa ce gaba daya sai da ilmi, yadda zaka kare lafiyarka, yadda zaka nemi Aure ka rikeshi, yanda zaka zabi shugaba.

Wasu mutanen su dauki ma’anar siyasa kamar wata kasuwa ce ta baje hajoji, inma a samu riba ko a samu faduwa. Irin masu wannan tunanin ne ake kira ‘yan siyasa marasa akida, domin su babu ruwansu da abinda ya dace illa abinda Aljihunsu ya dace dashi. Wasu kuma sun danganta siyasa kamar  dabi’a ce ta halittu masu rai aga uwa tana gaba ‘ya’yanta suna biye da ita, wato mai hankali shike shiga gaba domin na baya yayi koyi dashi.

Ismaila A Sabo
Ismailasabo@gmail.com

Sunday, July 29, 2018

TARIHIN SARKIN ZAZZAU JAFARU......

HADEJIA A YAU!




TARIHIN SARKIN ZAZZAU JA'AFARU....1936-1959.
Na rubuta wannan labari nawa don in bayyana godiya ta ga Ubangiji, kuma mutane kuga tsaunukan da na taka har na kawo ga wannan matsayi.

A cikin shekarar 1911, watau ina da shekara Ashirin da hudu (24) da haihuwa kenan, aka aika dani makarantar Dan-Hausa dake Kano. Na shekara guda acan na dawo gida. rannan ina zaune sai ga Shehu Baloha masinjan Joji, yace wai Joji yana kira na a Bariki. bayan naje sai naga Razdan ya dauki lambar Masinja ya lika mini a riga ta, yace "Yau ka zama Masinja" sai na durkusa nayi godiya. aka yanka mini albashin sule Talatin (30).

 Bayan nayi shekara uku ina wannan aikin sai rannan na roki Razdan ya maida ni makarantar Turawa ta Zariya, in rika koyawa 'yan makaranta Larabci.
Razdan yace "A'a wannan aiki bazai yi maka ba" saboda haka ya kai Magatakardar sa M. Kwasau can, Malami guda kuma Malam Umaru ya maida shi aikin Shanu, nikuwa aka game mini aikin su duka nake karbar Sule saba'in (70).

Ina cikin wannan aiki a cikin shekarar 1918 sai wani Hakimi na Zangon Katab ya taba kudin Jangali, aka fishe shi, ashe Allah ya nufa Sarautar a kaina zata fada, aka nada ni Hakimcin Zangon Kataf na koma can.

Sa'ad da nake Hakimi a wannan Kasa, naga abubuwan Tashin hankali guda biyu. wata shekara ina karbar Haraji sai Arnan Unguwar Gayya suka yi mini Tawaye. ina zuwa kauyen sai naji sun dauki kuwwa, nan da nan baka suka taru makil, kowa daga kwari sai baka a hannun sa, sai kayi tsammani wani abu ne yasa wannan bore. Dalili kuwa wai sun gaji da biyan Haraji ne kawai! Abu kamar wasa sai wani Arne wai shi Gankwan ya dana kibiya, yako duban ya sako mini ita. Sai ya kuskure mini ya samu Sarkin fada na a kafada. Yara na daga ganin haka sai suka yi kazam akan Arna! da Arnan nan suka ga bamu da Alamar tsoro sai suka bada baya, suka shige Kurmi gidan Tsafi.

Muka shiga garin muka tarar ba kowa, duk sun gudu mazan su da matan su. Na kira Sarakunan su da basu cikin tawayen, na gaya musu su lallashi mutanen su su dawo, babu komai. Washegari ni kuwa na yi zuwa Mabushi. A can na samu labari sun dawo sai shi Gankwan da ya harbi Sarkin fada na shine ba'a gani ba. Na aika ga Sarkin Zazzau Dalhatu da abinda ya faru duka, yace in kara matsawa kan neman Gankwan. Amma Ina? Ai har yau ba'a same shi ba, kamar an biya bashi dashi. Sarkin fada na kwanan sa wajen Arba'in a Mabushi yana jinyar daffin kibiyar nan.

Kai Arnan Zangon Katab a lokacin suna da wuyar sha'ani wajen al'amarin Haraji! Dubi wata shekara kuma da ni da wani Joji muna kama Awakin wadanda basu biya Haraji ba a Zankuwa, ba sai muka kama na wani wadda ya biya ba? sai gashi faram faram da matar sa suka zo suka durkusa suka ce mana "Wadannan Awaki namu ne, mu kuwa mun biya Haraji" Joji yace "To mu dai mun kama Awaki. Watau Makwafcin ka ya biya kenan, in ya samu kudi sai ya biya ka."
Da suka koma gida sai matar sa ta shiga zuga mijin ta na cewa "Allah wadan ka! Ashe dai kai ba Namiji bane? yaya don tsoron Sarauta zamu yarda a kwace mana Awaki? Ina ruwan mu da Makwafcin mu da zamu biya masa Haraji? Kai in baka dauki Kwari da baka ka tarad da Baturen nan ba, ina sa Wuta in kone su in kuma rabu da kai." Daga nan sai maigida ya dauki Kwari da baka ya tanka, 'ya'yan sa kuwa kowa ya dauko tasa, suka nufo wajen mu zasu tada Jihadi. Da na hango shi sai na daka masa tsawa sai ya yada Baka sai yazo ya fadi gabanmu yana haki. Na lallashe shi, na bashi magana sa'an nan ya koma. Ka ji tashin hankali da na hadu dasu lokacin ina Hakimcin Zangon Katab.

Na samu wannan Sarauta zamanin Sarkin Zazzau Aliyu ne, bayan shi aka nada Dalhatu. Daga nan sai Sarkin Zazzau Ibrahim ya kama Sarauta, shi kuma ranar 31/1/1937 ya rasu. Allah yaji kan su Amin. Bayan rasuwar Sarkin Zazzau Ibrahim, ina Hakimci a Zangon Katab sai ga waya ana nema na a Zariya, don Gwamna da manyan mashawartan Zazzau sun yarda in zama Sarki a shekarar 1936.

Madogara... Gaskiya Ta fi Kwabo ta 17. 1939.

 Daga nan sai na koma Zazzau da zama, muna rokon Allah da ya taimake mu rikawa Amin.

Sarkin Zazzau Ja'afaru shine dan M. Isyaku Sarkin Zazzau, dan Sarkin Zazzau Abdu dan Hammada. Allah ya masa rahma. 

Wednesday, February 14, 2018

HADEJIA.....

HADEJIA A YAU!


                     MASARAUTAR HADEJIA………

  1. Takaitaccen Tarihin Masarautar Hadejia .
Masarautar Hadejia dadaddiyar  masarauta ce wadda ta kafu shekaru da dama da suka gabata, daga lokacin kafuwarta kawo yanzu masarautar tayi fice da kuma yin suna bisa ga muhimman tarihi da take dashi. sannan tana daga cikin masarautun da sarakunan Habe suka mulka kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, kuma tana daya daga cikin masarautun da suke KarKashin Daular Usmaniyya. Daga Gabas ta yi iyaka da Tsohuwar Daular Borno da Gorgaram, daga yamma tayi iyaka da Masarautar Kano, daga Kudu kuma ta yi iyaka da Masarautar Katagum sannan daga Arewa ta yi iyaka da Masarautar Gumel. Birnin masarautar yana cikin garin Hadejia dake Arewa maso gabashin Jigawa a Arewacin Nigeria, sunan garin ya samo asalinsa daga wani Maharbi wadda shine ya kafa garin, wannan maharbi ana Kiransa da suna HADE, yana da matarsa da ake Kiranta da suna JIYA, Sunayen wadannan mutane shi aka hada ya zama Hadejia . A wancan lokacin mutanen wasu garuruwa in zasu zo sukan ce mun tafi garin Haden jiya, wato ana masa Lakabi da sunan Matarsa. Saboda taKaita kalma ta Hausawa shine yasa aka hade sunan ya zama Hadejia . A wani littafi da Marigayi Tafidan Hadejia Abdu Maigari ya rubuta ya bayyana cewa ‘‘Shi wannan mutumin da ya kafa Hadejia wato Hade ya taho ne daga yankin Machina a yawon farauta da yake har ya iso wannan yanki, kuma da ya shigo sai yaga Daji mai Ni’ima da tsuntsaye da namun daji ta ko ina, kuma ga kogi ya fito daga yamma ya gangara zuwa gabas Sannan ga ‘ya’yan itatuwa kala kala. Da ganin haka sai ya kewaye dajin sosai don ya samu inda ya dace ya zauna, sai ya samu wuri ya kafa Gadonsa irin na maharba yaci gaba da farautar Namun daji da tarkon tsuntsaye’’. Bayan kwanaki wannan maharbi yana zaune a wannan wuri sai yayi shawarar ya koma ya Dauko matarsa don suci gaba da zama a wannan wuri. A lokacinda yayi niyyar komawa sai ya debi abinda zai iya diba na naman da yayi farautarsa ya dawo garinsu ya Dauki matarsa ya koma wannan dajin da yanzu ake kira da suna Hadejia , sai ya kafa bukkarsa a kan jigawa kuma yaci gaba da farautarsa a wannan wuri har mazauna karkara dake kusa da wurin suka san da zamansa suke zuwa sayen nama da sauran dabbobin daji. Ana haka ne jama’a suka rinKa zuwa suna kafa bukkokinsu wasu masunta wasu kuma mafarauta da masu kamun tsuntsaye har gari ya zama gari ake Kiransa Garun Haden Jiya, sannan akayi shugabanci, zuwa wani dogon lokaci aka takaita Kalmar ta zama Hadejia . Ance a lokacinda ya zauna a bangaren Arewa akwai wani gari da ake Kira Hadegwaigwai inda yanzu Rubban Dakata take, sannan a bangaren gabas akwai gari da ake kira Kulunfarda inda ada can yake kan hanyar Tandanu. A yamma kuma akwai garin Kadime sannan a Arewa akwai garin da ake Kira Majeri, a bangaren kudu kuma akwai garin Tunawa wadda yanzu ake Kira Auyakayi. Sannan akwai Kudiginda HadebaKo wadda a lokacin take kusa da Kafur, sannan akwai Urki wadda yanzu ake Kira Unik sannan akwai Majawa, da kuma manyan garuruwa irinsu Auyo, Garungabas, Kazura, Dawa da Fagi.

A wancan lokacin ance Hadejia tana Karkashin Daular Auyo ne amma wasu sunce a’a tana KarKashin Ikon Garungabas ne tunda daga can ne ake nada Sarki ake kawoshi Hadejia, masu wannan da’awa sun bada labari kamar haka…  ‘A zamanin Sarkin Kano Yakubu Dan Abdullahi Barja wadda yayi sarautar kano a cikin shekarar (1452-1463), Algalfati Dan sarkin Machina yaje kano tare da ‘yan-uwansa guda uku inda sarkin kanon ya bashi sarautar Gaya, dan-uwansa na farko kuma yaje Rano sarkin Rano ya bashi sarautar Dal, na biyun kuma yaje Zazzau Sarkin Zazzau ya bashi sarautar Gayan, na ukun yazo Biram Garungabas inda Sarkin Gabas ya bashi sarautar Hadejia . Zuriyarsa ne sukayi mulkin Hadejia har tsawon lokacinda Sarkin Borno Mai Ali Ghaji ya tura Dansa Mai Idris Aloma ya yaki kano, sai ya biyo ta Hadejia ya yake ta ya cinyeta da yaki da sauran Kasashen dake yammacin Borno, sai ya danka ikon Hadejia da Garungabas da Dawa da Fagi a hannun Galadiman Borno, kuma shi Galadiman Borno sai ya barsu a rarrabe kamar yadda suke tun farko. Sashen Auyo ya barshi a hannun sarkin Auyo, Hadejia ya barta a hannun sarkin Hadejia , Garungabas ya barta a hannun sarkin Gabas, sannan Dawa da Gatare da sauran duk sai ya barsu a hannun fadawansa, amma duk a wurinsa suke karbar umarni kuma shi ake kaiwa Albarkar Kasa har zuwa tsawon lokaci’.  Koda yake ba’a samu rubutaccen tarihi game da sarakunan Habe da suka mulki Kasar Hadejia ba, ance anyi sarakuna guda Talatin da biyu (32), kafin mulkin Fulani. Masarautar Hadejia tana da fadin Kasa wadda ta kai Murabba’in kilo mita dubu shida da Dari tara da sittin da uku (6963), wannan yanki yana da shimfidaddiyar Kasa mai kyau wadda ake kwatanta yanayinta da na Kasar Chadi, kuma tana da Jigayi masu tarin yashi da kuma kwari mai tabo da laka amma bata da tsaunuka ko Duwatsu. Kasar Hadejia tana da Kogi wadda ya kasance akwai ruwa kowane lokaci, sannan tana da fadamu masu yawa wadanda suke Kafewa lokaci zuwa lokaci. Kogin Kasar Hadejia ya taso ne daga Kudancin Katsina ta Arewa da Zaria sannan ya nufi Arewa maso gabas ya shigo ta Kasar Kano ya ratsa Kasar Hadejia, sannan ya nufi Tafkin Chadi. Wannan Kogi ya ratsa ne ta Kudancin Hadejia da Gabashinta, wannan bangare ne da yake samarda ruwan sha da kamun kifi da kuma aiwatar da Noman rani. A lokacin damina kogin yakan cika inda yake samarda Kananan fadamu a sassa daban daban wadda ake amfani dasu a wajen noman lambu. A bangaren Noma Masarautar Hadejia tana gabatarda noma a lokuta biyu wato Rani da Damina, inda masana yanayin Kasa suka tabbatar cewa duk abinda aka shuka a wannan Kasar zai fito yayi kyau da iznin Allah saboda yanayin kyawun Kasar.


GUDUNMAWAR DA MASARAUTAR Hadejia TA BAYAR GA DAULAR USMANIYYA….
Masarautar Hadejia kamar sauran Masarautu ta bada gudunmawa sosai wajen tabbatar da kafuwar Daular Usmaniyya, domin tana daga cikin masarautun da suke iyaka da Daular Barno. Masarautar Hadejia ta nuna goyon bayanta ga Jihadin Shehu Usman Danfodiyo a zamanin Sarkin Fulanin Hadejia Umaru. Sarkin Fulani Umaru yana nan yana sarautar fulani sai suka samu labarin jihadin Shehu Usman Danfodiyo , Bayan yaji labarin jihadin shehu sai ya tara jama’ar Fulani sukayi shawara da suje suyi Mubaya'a da Da'awar Shehu,  anan wasu manyan Fulani suka ki yarda da hakan, ciki harda Kawunsa mai suna Jinagana. Sai sarkin Fulani Umaru ya tura mutanensa Karkashin jagorancin Dan uwansa Malam Sambo, sukaje suka miKa mubaya'arsu ga Shehu da kuma nuna goyon baya ga da'awarsa ta jaddada Addinin musulunci. Shehu yayi maraba da zuwansu kuma ya baiwa Sambo Tuta kuma yayi musu umarnin shiryar da sauran yankunan nan biyar na Kasar Hadejia . Sannan yacewa Laraima ya kula da yankin Gabashin Hadejia inda Marma da Fagi da Dawa suke yaje yayi kokarin shiryar dasu kan tabarkin Addinin musulunci. Amma bai bashi Tuta ba, sai sukayi bankwana da Shehu suka dawo Hadejia suka isarda sakon Shehu ga Sarkin Fulani Umaru suka sanar dashi kyautar da Shehu ya yiwa Laraima, sai aka hada Laraima da mutane suka tafi yankinda Shehu yace yaje ya shiryar dasu wato Marma da Fagi da Dawa. Laraima sai ya zauna a Marma saida suka shiryar da duk mutanen wannan yankin, kuma ‘ya’yansa ne sukaci gaba da shugabancin wannan yanki na gabas har zuwa lokacinda Sarkin Hadejia Buhari ya hade Kasar da tasa, wadda a baya MaDaci ce iyakar Hadejia daga gabas. Wannan yana nuna mana cewa masarautar Hadejia ta bada gudunmawa game da tabbatar Daular Usmaniyya, domin tana iyaka da Daula mai Karfin gaskekuma dadaddiyar wato Daular Kanem Borno.
A zamanin Sarkin Hadejia Sambo masarautar ta bada gudunmawa sosai wajen tabbatar da Umarnin Shehu na Jaddada Addinin Musulunci, bayan rasuwar Dan uwansa Sarkin Fulani Umaru an nada Dan wansa wato Mamman Kankiya, wadda shima ya rasu cikin watanni takwas. A lokacin da Sarkin Hadejia Sambo yayi shekara yana sarautar Hadejia sai yayi niyya ya tafi wurin Shehu, da zuwansa Shehu yayi murna kuma yayi godiya ga irin KoKarin da Sambo yake a Kasar Hadejia . Bayan Sambo yayi kwanaki a wurin Shehu ya gama abinda zaiyi sai yayi sallama da Shehu yayi shirin dawowa gida, Shehu ya Kara yin godiya ga Sambo kuma ya baiwa Sambo ikon duk wani Bafulatani wadda yake da Jar Saniya (Aborawa) tun daga bakin Dajin Rubu har zuwa iyakar Kasar Barno. Daga nan sai sambo yayi godiya sukayi bankwana ya dawo Hadejia tare da mabiyansa. Wannan kyauta da Shehu ya masa ta Ikon duk Fulani masu jar Saniya (Aborawa) tasa Sambo yawan Dawainiya domin nemawa wadannan Fulani matsuguni, kuma har zuwa wannan lokaci duk Bafilatanin da ka ganshi da Jar Saniya idan ka tambayeshi zakaji Asalinsa daga Kasar Hadejia yake.  

Sarkin Hadejia Sambo ya sake faÉ—aÉ—a Kasar Hadejia daga Gabas har saida ya mamaye galibin Kasashen da Galadiman Barno yake iko dasu suka dawo KarKashin ikon Hadejia , amma banda Dawa da Fagi domin Shehu ya bada su ga Laraima. Daga yamma har saida ya kai Kaugama da Sharkawa, da Majeri a yamma ta Arewa. Daga Gabas maso kudu saida yakai har Damaturu inda ya YaKi garin, sannan daga Gabas kuma ya tsaida iyakarsa a Madachi. A bangaren Arewa kuwa galibin garuruwan sun bishi ba tare da wata jayayya ba saida ya mamaye Garungabas da Kazura da Gatare har zuwa iyakar Machina da Damagaram.
Saboda irin gudunmawa da Masarautar Hadejia ta bayar ga Daular Usmaniyya, an taba baiwa Sarkin Hadejia Muhammadu Sarautar Sarkin YaKin Sarkin Musulmi.