"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Wednesday, February 29, 2012

Wakar Malam Amadu Dan matawalle Hadejia

1, Harama fasihi ka kara shiri, sarkin samari da 'yan mata.


2, Bismilla nayi nufin waka allah ta-ala kaban hikima, in shirya waka da hausa ta.


3, Nine nasan duk abinda nake nufi a wakar Hadejiawa.


4, sarki yana da mabudinsa nima ina da mabudi Malam idi kaine mabudina.


5, D.O yana da akawunsa nima ina da akawuna Abdu yaro kaine akawu na.


6, Ga mai fasaha kanin sidi, na abdu yaro na maitaushi.


7, Dan maraya na cikin daji, mugun dawa na cikin bene.


8, Su gajango an samu gun Ala, hannun ruwa zaya sha kashi.


9, A gidan biki damisa tilas aka sata sai da ta dau tandu.


10, Giwa tana yin bikin 'yarta, zaki ka bai alwalin ango namun dawa za'a sha hidima.


Sauran baiti goma a baya!

Wednesday, February 22, 2012

TARIHIN SARKIN HADEJIA HARU BUBBA

Sarkin Hadeji Haru bubba shine Mahaifin Sarkin Hadejia Muhammadu mai Shahada, wanda a zamaninsa Turawa sukaci Hadejia da yaki. Sarki Haru bubba Malami ne kuma mutum ne mai son zaman lafiya, kuma shine ya gina Masallacin juma'a Na Hadejia. Kuma a zamaninsa Gumel sukayi yaki da Hadejia, wato lokacin sarkin Gumel Abdu jatau. Sarkin Gumel ya aikowa Sarkin Hadejia zai wuce ta kasarsa wato ta kudu a gayawa Talakawa kada su tsorata bazai taba kowa ba. To amma koda yazo wucewa sai ya saba Alkawari don yana sawa ana debe kayan talakawan ana kaiwa Gumel. Koda Sarkin Hadejia ya samu labari sai yasa akayi sirdi aka fita, a wannan yakin aka kashe sarkin Gumel Abdu jatau. Galadiman Hadejia yakuba shine ya sareshi. Dama sarkin Gumel yayi mafarki bazai koma gida ba. Sai ya fadawa kaninsa Abubakar in ya mutu to a kaishi Gumel ayi masa jana'iza, kuma hakan akayi. Kuma a zamanin Sarkin Hadejia Haru ne Dansa Muhammadu Yayi yaki da Maguzawan Mada Rumfa ta Sokoto, inda sarkin musulmi ya masa sarautar Sarkin yakin Sarkin Musulmi. Kafin ya Zama Sarkin Hadejia. Allah yaji kansu.